← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 157

Sashe 17

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fannin su hindatu uwargidan su zulfa'u bayan kwanaki biyu na ɓuya da nunnuƙe sun yi finalising zasu na zuwa tare da ƴaƴan na su ana koya masu tare wanda da fari dariya zulfa'u ta masu sai da baby doctor ta nuna mata rashin dacewar hakan sannan ta daina,
  Ƴaƴa kam ana samin ƙaruwar su dan har ƴaƴan makota da ke zuwa koyon kararun basu ƙirguwa yayin da baby doctor ta zama tamkar tauraruwa a ƙauyen _koma_ kamar su bauta mata ga ta dai very smallish amma akwai ilimi da fasaha,ganin haka ya sa Dr Zaid yanke hukuncin zuwa tare da ita gidan su Asma'u dan su shawo kan ta ta amince da karatun da za'a na koya mata.

  Tun ranar da suka rabu baram baram basu kuma yin hirar arziƙi ba sai dai abin da ya shafi aikin su da shi ya kawo su garin dama takan yi mamakin sa na rashin son aiki son jiki ya mai yawa dan ko a wun outreach ɗin ita ke major work ɗin baya son yi kwata kwata bata san cewa aikin shi bane wato punishing ɗin ta a garin ko zata rage girman kan tsiyar da ke ɗawainiya da ita shi kuma bai san kan sa yake cuta ba dan ita kam tsakani da Allah ta ke aikin ta babu gajiya ko rangaji a tattare da ita sai ma ta daɗa daraja da ƙima a idon jama'an ƙauyen dan kaɗan ya rage su fara worshiping ɗin ta saboda ire iren kayayyakin da suke kai mata wasu kaji wasu namar dabbobin su wasu fresh milk wasu girki suke yi na musamman su kawo mata duk wannan budirin a idon Dr Zaid ake yin shi ta tafasa sauke bata taɓa ce da shi ba haka take enjoying goodies ɗin ta ita da ƴan gidan..

*********
_Friday evening_
  _4:00pm_

Cikin shigar atamfa hollandaise ɗinkin riga da skirt 8 pieces da ɗaurin Aisha Alhassan wato wanda ake turo shi gaba inkiyar ture ka ga tsiya,da mayafin ta na mutunci haɗe da takalmin spline mai ɗan tudu riƙe da wayar ta a hannu ta fito ƙofar gidan inda ta same shi cikin shigar kaftan lilac colour da hular sa ƙafar sa samye da normal skin takalmi yayi kyau ainun dan abin da ya daɗa fiddo da shi shine baƙar speck ɗin da ya saka sai ya haɗe da jikin sa yayi ras gwanin sha'awa

She must say that he looks handsome in his cultural attire dan haka tana tafe ta bashi unexpected pic wanda ya bala'in yin kyau a hoton amma on reaching to him sai ta É—an haÉ—e rai irin kar ya rainata É—in nan.
  "MashaAllah"ya furtawa kan sa da yayi tozali da ita amma shima ganin ta ɗaure sai ya mazge haka suka kama hanya tinƙis tinƙis sai gidan su Asma'u ma'ullen Mudan.

A ƙofar gidan su suka tsaya ya aika yaro da a masu iso babu jimawa aka basu damar shiga

Tarbo mai kyau aka masu kasancewar shi ɗin ɗan gida ne sai aka karrama su sosai ko da yayi tambayar Asma'u rasa abin cewa mahaifiyar ta tayi dan tun wuraren ƙarfe uku da rabi rabon ta da ita sai ta buɗe baki zata kauce amma sai suka ji bambamin masifar ta

"Wallahi wallahi bilahilazimin ba za'a ci bulus da ni ba ni Asma'u ma'ullen Mudan sai sun san sun É—ebo ruwar tafasa kan su tabÉ—ijam bala'i"......

Kasa kunne suka yi suna sauraron ta sau gashi ta bankaɗo labulen zauren gidan na su ai ko ta ci karo da su Dr Zaid tana ganin su ta antaya a guje wai ta ji kunyar ɗaga muryar da ta yi a gaban su,miƙewa yayi yana kwaɗa mata kira tana cewa
"ÆŠan birni bani sake haÉ—a ido da kai sai nan da sati guda tabb da ni za'a yi abin kunya inaa".. Sai rafka gudu take ai ko daidai wani dandamalin kwata ta antaya ciki bata lura ba............

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
#vote
#comment
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

_i love u all dan kuma kuna so na wato masoya na a duk inda kuje ku san cewa ni siyama ibrahIm ina son ku_
*7*

"Asma'u ki dakata mana kin ga abin da kika janyowa kan ki ko a kan wani silly reason"yana maganar ne yayin da yake ƙoƙarin matso ta ai ko ta tsala wata ihu mai razanarwa wanda yayi sanadiyar firfitowar jama'a har da su baby doctor da je zaune cikin gidan su Asma'u tana mamakin rashin hankali irin na ta..

Taruwa sosai aka yi a wurin ga shi dai ana son yin dariya amma kowa na tsoro dan kana darawa ta san fuskar ka anjima Mudan na zuwa zai keta maka rashin ɗa'a dan haka kowa gimtse dariyar sa yake yi bugu da ƙari ga bokan turai a wurin sai suka rinƙa mamakin abin da ya haɗa shi da ita amma suka yi gum suka bar wa kan su suka tsaya kallon ikon Allah. 

Dr Bilkisu da fitowar ta kenan tayi arba da aika aikan da Asma'u ta ma kanta ga Dr Zaid a tsaye a kan ta ga jama'a duk ita ake kallo ai bata san lokacin da ta kece da dariyar da bata san dalilin zuwan sa a dai dai lokacin ba sai yi take yi har da ƙwalla.
  Mahaifiyar Asma'u da ke gefe tana tir da halin ɗiyar ta ta dan irin kunyar da ta ji baya misaltuwa shiru ta yi tana kallon Asma'un yayin da Dr Bilkisu ke ta dariya babu ji babu gani dan haka cikin mugun ɓacin rai da fusata ya daka mata tsawa cikin turanci dan kar a san me yake nufi ya ce

"For crying out loud Bilkisu will you stop laughing some one is here crying for her life and you are standing there laughing don't you have human sympathy"? Ya ƙarasa yana mai daka mata tsawa kamar ɗiyar gaban shi.

Sai a sannan ta ankare da ɓaranɓaramar da ta yi sai ta ji babu daɗi ko ba komai mahaifiyar yarinyar na wurin kuma ba zata ji daɗi ba dan haka sai ta gimtse dariyar ta ta matsa kusa da su daidai kan Asma'u ta miƙe mata hannu sai dai atafau Asma'u ta ƙi miƙa mata nata hannun wai ita sai dai ɗan birni ya bar wurin shi kuma tsoron matsawa yake gudun kar baby doctor ta wuntsila ta cikin kwatan bayan ta ɗago ta since he knew that ba su cikin good terms.
Ganin bata da niyar miƙo hannun sai baby doctor ta gane cewa kunyar jama'a take ji ciki kuwa har da shi saurayin ma'ullen Mudan ɗin wato Dr Zaid sai ta juya ta ce da shi
"Please she needs privacy"!! A É—age ya kaklle ta dan ya san ba tsakani da Allah zata taimake ta ba sai ya girgiza kai alamun ba zai matsa ba.

"Are you for real?huh?don't you see that your saviour is sinking in this dirty pit"?kallon ta yayi yana son sanin shin tsakani da Allah ta ke son taimakon Asma'un ko dai ganin ido ne sai dai bai hango komai ba dan bata bashi wannan space É—in ba so he have no any other option but to give them space...

Yana ba da baya Asma'u ta miƙa hannun ta da taimakon baby doctor ta fito daga cikin kwatar duk kayan ta ya ɓaci dan har ƙuƙurjewa ta yi a hannun ta haka ta fito fuskar nan tam cike da bala'i ta hankaɗa masu kallon banza ta ce

"Munafukai algungumai annamimai toh ƙwalelen ku ban mutu ba kuma ban kasara ba ku jira ni anjima sai mun zo dukkan ku zaku gane munafurci bai maku rana ba".. Ta ida tana ɓalla masu harara kamar zata zazzago manyan idanun ta haka dai ta lallaɓa suka koma cikin gidan su yayin da su Dr Zaid da mahaifiyar ta suka biyo su a baya bayan ƴar tazarar da suka ma juna dan ce mai tayi ya juya zuwa direction ɗin da aka fiddo ta har su shige ciki kafin ya biyo su hakan ya yi.

Da zuwan su direct cikin ɗakin su ta yi tana ƙoƙarin cire kayan jikin ta dan haka Bilkisu bata bi bayan ta ba ta zauna a tabarmar tana mamakin halin Asma'u ga shi dai a zahiri tsayayyiyar yarinya ce mai kyau amma abaɗini babu halin kirki a ce an fiddo ki daga kwata amma babu kunya kika tsaya fetsa rashin mutunci Allah ya kyauta.

Bayan kamar mintuna goma suna zaune ana ta hira tsakanin Dr Zaid da mahaifiyar Asma'u ita dai nata ido sai complains ta ke ta mai a kan Asma'un a nan ta ke sanar da shi abin da ke gudana tsakanin ta da Mudan toh a nan baby doctor ta daɗa kashe kunne dan jin ta bakin mahaifiyar Asma'un ai ko ta sami labarai da kyau har ta tabbbatar cewa eh lallai Asma'u akwai hankali da wayo duk rashin jin na ta akwai mutuncin ta tare da ita dan dama wai shi Mudan ɗin ya daɗe yana maganar a kawo kuɗin aure amma yayyen ta sun ƙi kuma duk iskancin su shi kan sa baya taɓa ta dan yana riƙe mata gyale sai sun yi sati biyu basu haɗu ba ta ɗau gaba da shi kenan kuma kaf gidan su sai sun san Mudan ya taɓa mata gyale kuma ta shaida cewa sai ta ɗau sati biyu kafin su shirya sai dai a ji ta kawai dan ta saba ire iren maganganun but her momma is very conscious of her act a kuum in zata dawo gidan cikin dare sai ta mata full inspection ta duba jikin ta sosai sannan take samin kwanciyar hankali.
Chapter 17 · 0% Book details