← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 157

Sashe 108

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

 
A nan É—akin Bilkisu kuwa bayan fitar Alawiyya iska Bilkisu ta furzar cikin son kare kan ta ta ce
"Please in ka san blame games ka zo playing da ni har gidan mu just go away i don't want to hate you more"zafi take ji cikin ran ta dan yayi putting blind face to matsalar yana son ce mata bai san me ya faru ba kenan itace mahaukaciya mai É—aukar son sa da kishin sa a kan ta tana yawo da shi..
  Harɗe hannuwan sa yayi bisa ƙirjin sa yana bin ta da kallo dan mamakin ta ya kasa barin sa mutum da mood swing haka da tana da ciki ne ma sai ya ce ɗaya daga cikin changes da ke samin mata kenan in sun yi conceiving amma ita babu but she gets irritated easily.
  Yana kallon ta ta gama maganar da zata yi shi dai nashi ta bashi chance su yi magana ya ji damuwar ta dan dole yana son tafiya Yola washegari kuma bai son tafiya da damuwar Bilkisu a zuciyar sa.
  Takowa yayi kusa da ita ya durƙusa ya kawo hannun sa ya haɗa da nata yana kallon ta tun bata son kallon sa har ta mayar da hankalin ta kan sa ta shiga kallon sa sai a yanzu take ƙare masa kallo tsaf a tsanake.
  Kyawun sa da kyawun shigar da yayi ta ke yabawa a ran ta sai kuma kishin sa ya biyo bayan yabon sa da take cikon ran ta dan ba ƙaramin kyau ya mata ba ko ina zai tafi da yayi wannan irin adon she just pray ba fita zai yi tana roƙon Allah ya sa dan ita yayi adon..
  Ɗago idanun ta tayi ta sauke saman fuskar sa ta tsare sa da ido shi kuma sai ya ɗauka ko attention ɗin ta ta ba sa dan haka ya fara magana cikin lumana da son samin mafita
  "Bilkisu ki saurare ni ki bani breathing space in maki bayanin matsalar da ya kawo mana kai but ba zan iya explaining kai na ba har sai na san damuwar ki ki yi haƙuri ki sanar da ni matsalar me na maki da kika ɗau wannan matakin a kai na"?ajiyar zuciya ta sauke tana mai kallon ƙwayar idanun sa tana so tayi fushin da shi amma ba zata iya ba.

Idanun su cikin na juna ta girgiza kai tana mai juyar da kan ta gefe sai yayi saurin riƙo fuskar taya dawo da shi direction ɗin nasa fuskar suna kallon juna sai ya girgiza mata kai ya ce
"Kar mu fara da haka baki zaki buÉ—e ki min bayani,sam bana son hayaniya Bilkisu but you made me raise my voice on you why"?kallon sa tayi idanun ta na cikowa da hawaye sai ta fara magana cikin karayar zuciya
  "Na san ba ni kake so a,na san ba a hayyacin ka aka haɗa mu aure ba na san ba so na zaka yi ba ko a wani duniyar,amma ka sani nima ba yin kai na bane zama tare da kai,ban taɓa mafarkin zama inuwa ɗaya da kai ba dan bamu da kyakyawar fahimtar juna,,,a ranar da na bari abu ya shiga tsakani na da kai a ranar ka yi manifesting min real you...,,ka nuna min tsana tsantsan,,,ka mim kora da hali Zaid,you should have been patient da na bar maka rayuwar ka at a twinkle of an eye ba sai ka nuna min ƙarara tsanar da kake min for a very long time ba"shiru ta mai bata cigaba da maganar ba sai ya ɗan ɗago daka tsugunnen da yayi height ɗin sa ya zo daidai da nata yana bin ta da kallon da shi kaɗai ya san ma'anar sai ita kuma ta sauke kan ta ƙasa dan hawaye ne ke son zubo mata kuma bata so ya ga weakness ɗin ta.
  Cikin sanyin murya ya shiga yi mata magana kalmar farko sai da ya saukar mata da kasala
"Baby,,..you see....bana son ki saka wani abin a ran ki after what happened between us that night....nayi ƙoƙari dan in ga na gane damuwar ki amma baki bani chance ba...a yanzu da muka haɗu kuma kina son mayar da maganar wani abin daban can you please spot out the main point of concern to me ban san laifin da na maki ba"..idon ta ta zuba mai har ya gama maganar sa sai ta hau girgiza kai tana cire hannun ta cikin nasa ta matsa baya kaɗan haɗe da ture sa daga jikin ta
"Zaid,,,ka faÉ—a min irin tsanar da kake min...please tell me"!!!abin ya É—aure masa kai shi tambayar ta yayi amma ta juyar da maganar zuwa kan sa sai ya ce
"Bilkisu bana son wani blame games anymore just tell me,mai na maki"?idon ta ya canza launi ya ƙanƙance dan ba ƙaramin kuka ta sha ba..
"Baka san laifin da ka min ba"?muryar ta chan ƙasa tayi mai tambayar sai ya girgiza kai yana mai ƙara riƙo hannun ta cikin nasa
"Zaid......,,my first reunion with you.....you didn't even remember me...wata fah ka rinƙa kira...sunan wata ka rinƙa nanatawa sama da abin da zan iya ƙirgawa...i....i...gave you something precious in my life but....you handled it carelessly...duk saboda ka tsane ni Zaid....you broke me into pieces....you made me hate you a hate that has no limitations a hate that is created out of trust...the hate you gave me was a massive one...baka san abin da ke rai na ba akan rayuwar mu amma you diminished everything you changed our fate you spoiled everything and i hate you for that i hate you for tarnishing our future my future i hate you for that Zaid"sai ta shiga dukar sa a ƙirjin sa tana kuka dan ta kasa riƙe hawayen ta dan abin na mata ciwo duk sa'iln da ta tuno kalmar da ya faɗa mata na cewa _yes i have feelings for her and you can't do anything about that_ sai ta ji ran ta na mata zafi dan da a ce bai nuna mata abin da yake buƙata daga gare ta ba da ba zata ji zafin sa sosai ba amma ya nuna mata halin su na maza ya sami abin da yake nema daga gare ta ya ji ta ishe sa..
Chapter 108 · 0% Book details