← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 157

Sashe 16

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa uban gayyar ko da ya ji labarin wannan daɗin sauyi na koyawa yaran karatun boko da zata yi sai ya ga why not yayi convincing Asma'ur sa ta zo ta yi joining tunda shi bai taɓa kawowa a ran shi ya koyar da ita ba ko ma ya saka ta a makarabtar bokon ba duk zuwan da yake yi ƙauyen ashe daumi kansa yayi wa wannan dabarar zuwa da baby doctor a da so yayi ya haɗa ta da mutanin ƙauyen ya nuna mata bata da daraja sai dai ya ga yanzu tana da amfani sosai a gare shi he just pray that Asma'u ta amince dan ya ga kamar jinin su bai haɗu da Bilkisu ba..

  Cikin dare suna hira tare da zulfa'u akan abin da zasu yi ita da Dr Zaid next week ana haka ɗaya daga cikin yaran ɗakin matar mai gari ta biyu mai suna hafiz ya zo ya yi sallama kamar yadda ymta koyar da su akan kar su na shiga wuri kai tsaye babu sallama kuma in sun yi su bari har sai an basu izini kafin su shiga

"aunty likita wai ki zo in ji uncle likita yana ƙofar gida yana jiran ki"da mamaki ta kalli time ta ga past 9pm kuma a ƙofar gida ba ma a cikin gidan ba ko me ya faru.
  "Bara na je na dawo ba zan daɗe ba".
  "Toh sai kin dawo likiciya".
 
  Fita ta yi ta same shi a ƙofar gidan dan haka sallama ta mai ya amsa sai ta ce mai
  "Ka kira ni a ƙofar gida da daren nan lafiya ko"?
  Ɗan shiru ya mata yana jin izza izza ita kuma ganin bai da niyar yin magana sai ta juya ta kama hanyar tafiya dan yau itama nata izzan ya motsa.

"Wait"!!! Ya dakatar da ita.
  Inch ɗaya bata ƙara ba ta dakata ya kuma cewa cikin isa
  "Ki dawo mana magana nake son yi da ke"!! wani irin juyin isa da mulki ta mai kafin ta ce
  "Ban ga alamu ba in ka shirya sai ka neme ni ni kuma in ina da lokaci sai in amsa kiran naka"!!daga haka ta wuce cikin gida

"What have i just done?alfarma fah nake son nema a wun yarinyar nan,oh gosh thank goodness ban furta ba whatt"???ya ƙarasa yana godiya ga Allah da bai bashi ikon furta mata niyar sa ba da shikenan she will definitely look down on him.

  Yanke shawarar koyar da Asma'un da kan shi yayi dan yana ganin kamar zata fi amincewa since she respect and value him a lot dan haka ya bari akan gobe a wun outreach zai sanar da ita ƙudirin sa,daga haka ya shige cikin gidan ya kwanta,

"Hakan me ya ce da ke ne wai"? Zulfa'u ce ta mata wannan tambayar sai ta bata amsa da cewa
  "A'a kira aka mai wai ana ta kiran layi na bai shiga shine aka gwada nashi ɗazu a wun aikin nan shiyasa ya kira ni dan sanar da ni kin san ba mu samin damar kira dan babu service a nan"cikin hanzari ta tari numfashin ta ta ce
  "Inaa likiciya ai muna samin sabis a nan gidan zo in gwada miki"ta ja hannun ta zuwa cikin toilet ɗin ta ta nuna mata gefen da zata sami service ai kuwa kamar abin asiri sai full service cikin ɗoki ta danna kiran umman ta da layin ƙasar waje ya shiga sai dai bata ɗauka ba sai ta kuma kiran layin Bahajjatu ringing biyu ta ɗaga
  "Apple dama zamu gana da ke a cikin dajin nan"! Dariya suka saka tare daga bisani suka shiga hirar su ta aminai sosai suka daɗe kafin su yi goodnight..

  Haka ta rinƙa kiran ƴan gidan su suna gaisawa kamar ba gobe sai goma na dare ta fito ta tarar da zulfa'u tana ta jiran ta dan tana so ta tafi turakar mai gari tana jiran ta zo ta rufe ƙofar ɗakin

"Kaii likiciya kin daɗe kamar baki da ranar fitowa toh ni dai zo ki rufe ƙofar zan tafi sai da safe"
  Dariya maganar ta ta bawa Bilkisu ta ce
  "Toh amaryar mai gari Allah ya tashe mu lafiya"ta raka ta ta tafi ita kuma ta dawo ta rufe ƙofar ta chanza zuwa kayan barcin ta ta haye gadon ta kunna laptop ɗin ta da tun da suka zo bata taɓa bi ta kai ba shiga fannin movies ta yi ta yi playing wani nollywood movie mai suna If i were the president tsantsar siyasanci da ha'incin gwamnati ne a ciki ta yi nisa a kallon ta ji ana buga ƙofar ɗakin da mamaki ta diro tana ƙoƙarin saka falmarar rigar ta ta ce
  "Wa nene"?
Aka amsa mata cikin haÉ—a baki
  "Likita mu ne"da mamaki ta ce
  "Ku?ku su wa"?
  A karo na biyu suka kuma ce mata
  "Su hindatu ne likita"a nan ta gano su wato matan mai gari ne hindatu ita ce uwar gidan sai halima sai karime.
  Buɗe masu ƙofar ta yi suka shigo suna leƙe leƙe kamar marasa gaskiya.
  "Ku zauna mana"suka zazzauna a kujerar falon ita ma ta zauna sai suka rasa ta ina zasu fara ita ce dai ta yi initiating maganar ta hamyar cewa

"kun yi shiru da fatan dai komai lafiya babu wata matsala"?
  Suka shiga girgiza mata kai kafin hindatu ta ƙoƙarta ta ce

"Likiita dama wata magana ce mai muhimmanci muka zo da ita wadda muka ga zai fi mana sirri in zulfa'u bata nan dan yarinyar nan akwai karaÉ—i da iyayi".

Oh ikon Allah mutanin nan ba shiryuwa zasu yi ba kishi har a gaban baƙo.
  "Toh ina jin ki maman usee me kuke son in maku"?ta tambaye su tana son maintaining eye contact da su dan ta nuna masu cewa tana tare da su kuma maganae tasu na da muhimmanci a gare ta.
  Cikin sakin jiki hindatu ta ce
  "Likita wannan karatun ta arabi,shi muke son a rinƙa koya mana in an gama koyawa yaran mu amma a ɗaki na zaki rinƙa koya mana ta yadda wannan ƴar ba zata sani ba dan Allah ki taimaka mana"matuƙa ta ji mamaki dan haka ta ce
  "Toh maman usee me ya sa ba za ku so zulfa'u ta sani ba kamar abu marar kyau"?
  Numfasawa hindatu ta yi kafin ta ce
  "Ƴar nan kin ga dai tun zuwar wannan yarinya ta rinƙa ƙoƙarin tursasa mana akan addinin mu muka ƙi yanzu da kika zo muka ga tsarin ki sai muka ji ran mu ya biya har ma muka yanke hukuncin tunkarar ki dan ki fara koyar da mu tunda hasken rayuwa ya biyo mu har gida kuma da kunya a ce kina koya mana yarinyar nan tana gani ai sai ta raina mu". Ta ida tana ɗan chanza mood ɗin ta abin ya ɗaurewa baby doctor kai wai dama haka jama'a ke yawo da duhun kai?lallai tafiya mabuɗin ilimi duk dan kishin da bai kai ya kawo ba.

"Hmm maman usee kin ga ni dai shawara É—aya zan baku in fah kun ji nawa,tunda dai baku ji kunyar zuwa neman ilimi ba bana jin ya kamata ku ji kunyar Æ´ar uwar zaman ku duba da cewa gida É—aya kuke ko mu jima ko mu daÉ—e wataran zata sani kuma kunyar da zaku kwasa sai ya fi ta wadda in kuka bari ta san da fara koyon addinin ku tun yanzu in kun ji nawa kawai ku basar ai ba'a girma a neman ilimi"daga nan ta yi shiru dan jiran jin opinion É—in su.

Ɗan shiru suka yi suka rahe murya suna ƙusƙus kafin daga bisani ita mouthpiece ɗin su ta magantu

"Toh likita mun ji shawarar ki amma ki mana alfarma É—aya"ta kalle su ta ce
  "Ina ji".
  "Yauwwa so muke ki banu daga yanzu zuwa gobe iwar haka zamu sanar da ke shawarar da muka yanke".

Jinjina masu kai ta yi suka miƙe suka mata sai da safe sannan suka tafi,dawowa ciki ta yi tana mamakin wai ita da ta zo health outreach kuma ta ɓige da karantar da ahalin gidan mai gari karatun addini har ma da na bokon da zasu fara,
"Ikon Allah komai na da sanadi"ta ce da kanta tana mai kwantawa a kan gadon,ƙarasa kallon ta yi sannan ta kwanta barci.

************

First week ɗin su went successful da orientation phase ɗin kuma they were able to picture out matsalolin yankin wanda mafi akasari wife/husband battery,domestic violence kuma akan mace ne da ƴaƴan ta wato ƙuntatawa abokin zama wanda a nan garin matan aka fi ƙuntatawan da ƴaƴan su kuma ta lura akwai matsalolin mata da ya shafi jikin su sosai wanda har yayi affecting mata da dayawa ciki kuwa har da wata marar lura da damuwa da kanta ta ke faɗawa baby doctor cewa in ta zaga bayangida wasu lolutan ta kan ga kamar mahaifar ta ya tulluƙo amma wasu lokutan bata gani sai kawai ta saka hakan a matsayin haihuwar da ta yi ne watanni shida da suka wuce a nata tunanin ai zai tafi bayan watanni takwas ta ƙi zuwa asibiti bare a duba ta toh wannan issue ɗin duk ya fi damin baby doctor dan haka ta sanar da Dr Zaid ya ce da ita dole asibiti zasu tafi kafin a duba a ga degree ɗin annular detachment of the uterus ɗin in wanda za'a iya replacing ne sai a yi in kuma wanda sai dai a yi surgery ne sai su sanar da family ɗin ta su yi.
Chapter 16 · 0% Book details