← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 157

Sashe 12

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina ga mun yi creating rapport mai ƙarfi so we can commence"murmushin fatan baki ya mata ganin jama'a sai ya ce
"Yes we can"
Daga haka suka fara shirye shiryen gabatar da abin da ya kawo su from no where suka ji an ce

"Wai farawa za'a yi ban da ni"? Juyawa suka yi daga shi har ita sai ta hango wata ƴar yarinya ƙarama dan ba zata wuce 14years ba fara kyakyawa kamar am zana ta doguwa ƴar mai jiki da ita tana tafe tana taunar chewing gum tana tafe kamar wacce bata san tsarin tafiya ba cikin rashin kunya da fitsara ta tako har inda suke ta buɗe baki tana jujuya idanu

"Wai toh ba dan na zo ba shikenan babu wanda zai aika a kirawo ni"!? ta faÉ—a cikin izza kamar wata sarki,gabaÉ—aya mutabin wurin shiru suka yi suna kallon ta dan in da sabo toh sun saba da halayar nata na rashin girmama na gaba da ita gashi ba'a isa a mata faÉ—a ba da a mata faÉ—a gwara a yi shiru a zuba mata idanu dan bata da kunya ko kaÉ—an

"Wacece ke kuma me yasa tun lokacin da aka zo ke ɗin baki zo ba alhalin tun jiya aka sanar daga fadar mai gari"cewar Bilkisu cikin ɓacin rai dan babu sallama babu gaisuwa kawai fatam fatam faransa kamfani ba oda

Instead ta bata amsa sai ta ja tsaƙi ta na cewa
"Hmm bokan turai ko?toh ki je ki tambaya a baki gamsashiyar labarin ko ni ɗin wacece hatta da ƙaramin yaro ya san da labari na dan haka ni ban da lokacin baki labari na yauwa"daga haka ta juya tana tattauna chewing gum ɗin ta tana sarrafa shi yana bada ƙarar ƙas ƙas ƙas..

Duk mamakin yarinyar ya gama cika baby doctor dan haka ta juya ga Dr Zaid dan tambayar ko ita É—in wacece tunda shine tsohon zuwa dole ya san ta

"Who is she"? Cikin ko in kula ya ce...........,,,,,,

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
#vote
#comment
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

👄 °°° °°°👄
°°
°

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

*5*

"Sunan ta Asma'u kuma ƴar nan yankin ce again bai kamata ki tsare ta kina mata ihu ba kawai dan ta zo ƙarƙashin ki neman abu a gare ki ba"daga haka yayi shiru yarinyar ta kada baki ta ce
"ÆŠan birni baka faÉ—a mata É—ayar sunan ba"sai ta juya ga Bilkisu ta kalle ta cikin fitsara ta ce
"Ma'ulle"inkiya ta kenan kuma bana É—aukar raini ban ma san abin da ya sa na kyale ki kika gasa min magana har haka ba ba tare da na nuna miki ko ni É—in waye ba"ta juya kai tana rakaÉ—i

Tsyawa kallon ta tayi cike da alhinin wannan fitsararriyar yarinya marar tarbiya ta juya ta kalle shi ta ce da shi

"What ever her name is ba business ɗi na bane dan bata gaba na iya abin da na sani ba zan ɗauki rashin kunya daga wun ƴar ƙanƙanuwar yarinya ba kai da ka san ta sai ka nuna mata muhimmancin zuwa na dan bata isa in zauna orienting ɗin ta ba"a zafafe ta karasa maganar wanda hakan ya bashi mamaki dama ta na da masifa har haka?shi kam bai taɓa gani ba sai dai ji a hospital a ce ta masife su a asibitin but shi bai taɓa witnessing ba

"Me ya sa ba zaki iya mata magana da kanki ba alhalin kin san ke ce da laifi"ƴar ƙaramar scoff tayi ta ce

"Are you for real"? ÆŠage mata gira É—aya yayi daga haka ta mai banza ta cigaba da abin da take da niyar yi

"Ku yi haƙuri fah kun san a wuri dole mutum ya haɗu da masu tarbiya da marasa shi in kuma mutum ya haɗu da marasa sanin ina ke masu ciwo dole ya daidaita su domin samin kyakyawar sakamako a wun aiki ko ba haka bane"?cikon chorus suka amsa da
"Haka ne likita"ta yi murmushin gamsuwa ta ce da su

"Toh yanzu dai zamu fara abin da ya kamata saboda yanayi na gari tunda ruwa ake yi yanzu gashi akwai ayyukan gida da za'a yi in an bar nan dan haka ba tare da ɓata lokaci ba zaku gaya min sunayen ku ne da shekarun ku haka ma da ayyukan da kuke yi"murna suka yi sosai dan she tried as much as possible ta wurin bringing kan ta so low wanda ya saka su jin kamar ta saka kan ta a shoe ɗin su ne dan haka babu ɓata lokaci suka fara gabatar da kan su ɗaya bayan ɗaya yayin da ita kuma yarinyar mai suna Asma'u ta haɗe rai tana ta faman kumbure kumbure yayin da shi kuma ya ke ta bata haƙuri,sam ta manta da su a wurin ma kwata kwata sai da aka yi rabi da introduction ɗin ta fara duba shi,chan wani bakin bishiya ta hango su zaune abin ya firgitata dan haka ta juya ga ɗaya daga cikin matan da suka yi introducing kan ta ta ce mata
"Wai ni kuwa baba waccan yarinyar wacece ita"?ajiyar zuciya ta sauke ta ce cikin jimami

"Kin ga waccan yarinyar"? ta girgiza mata kai sai ta cigaba
"Sunan ta dai kamar yadda bokan turai ya sanar da ke Asma'u ɗiya ce ga mamman mai rasuwa dattijon kirki da kamala mutum mai haƙuri duk faɗin yankin nan ana daraja shi ba kaɗan ba dan bayan sarki da mai gari sai shi halin dattako irin tasa yasa ko matsala aka samu wun shi ake zuwa dan ana mutunta shi ba kaɗan ba..ita kaɗai ce ƴar shi mace yayyen ta biyu maza duk yaran kirki ne su ita kaɗai ce ta fito bare babu hali dan uwar ta ta yi ƙoƙarin tarbiyartar da ita haka mahaifin ta ma yayi ƙoƙarin sa sai dai albasa bata yi halin ruwa ba dan daɗin taɓarɓarewar tarbiyar ta wannan tsagerin saurayin nata mai suna Mudan yaron nan babu hankali gashi dai a fuska kamili daga shi har ita sai dai babu halin arziƙi toh a faɗin ƙauyen nan ko wani lungu da saƙo an san su dan tare suke zaga garin kuma duk wanda ya san Mudan ya san shi da jarabar tsiya da fitina toh haka duk wanda ya taɓa Asma'u ya taɓo jaraba dan kusan kowa tsoron sa yake ji ba kaɗan ba shi yasa ƙarfe shida na yamma na bugawa zaki ga yaran gari sun koma gidajen su amma a lokacin Asma'u take cancaɗa kwaliya ta fita ita da Mudan su zaga garin nan sai karfe tara na dare suke dawowa an daka har an gaji amma bata daina ba dan haka aka zuba mata idanu kawai toh kamar dai yadda muka ji shi wannan bokan turai shine yayo dare a hanyar sa ta dawowa daga cikin gari tsageran garin suka tare shi a hanya itakuma sun rabu da Mudan kenan zata dawo gida ta ci karo da su a hanya ai kuwa shine ta masu kaca kaca kuma sun san ko ita ɗin wacece sai suka gudu ba dan haka ba da sun mai kisan gilla dan ba su son harkar asibiti a cewar su duk ma'aikatan asibiti bankaɗo sirrikan su na shaye shaye suke yi daga haka gwamnati sai ta saka masu ido har a tono asirin su a hukunta su wanda hakan ba daɗi ke masu ba,toh kin fah ji labarin wannan botsararriyar ƴar wacce ta fi ƙarfin jama'an gari...

Gwauron numfashi baby doctor ta saukeyayin da jama'ar wurin ke jinjina kai dan gabaÉ—ayan su sun san da wannan rikitacciyar yarinya mai sigar marasa kunya.

Kuma kallon su tayi sai ta shiga mamakin yadda aka yi rasa yarinyar da zai saurara duk jiji da kan nan nasa da fa'ili iya nan ya tsaya lallai dole ta raba shi da wannan fetsararriyar yarinya dan sam bata ma da gurbin zama cikin rayuwar su saboda bata da tsari bare tarbiyar da zata taki matakin zama cikin ahalin su. Hmm ji ƙarfin hali irin na baby doctor.

Cigaba da aikin ta tayi a ƙarshe ta aiki wani yaro ya kirawo mata su sai da ya ja lokaci kafin ya taso ya zo

Tana gaba yana baya suna tafe suna É—an zantawa kallon su take yi ta mayar da idanun ta kan yarinyar da ke tafiya cikin iyayi tana mamakin rashin ji irin na yarinyar har dai suka nufo su sai ya dakata ya ce da ita

"Kin kira ni"cikin tsare gida yayi maganar itama sai ta haÉ—e rai ta ce
"Am done with today session sai ka zo mu ɗau evidence"bai ce ƙala ba ya ɗan rage murya ƙasa ƙasa ya ce mata yana zuwa tana dariya ta ce mai toh haushin ta baby doctor ta ji ta ce
"Na fah gaji"dakatawa yayi ya fiddo wayar sa ya saita ya fara videoing ɗin su yana yi yana tambayar yadda suka ji daɗin abin haka har suka gama da zasu tafi gida aka basu packs ɗin ktautar su kayan wanki da na wanke wanke as an incentive duk dan su dawo washegari da murna haɗe da addu'oi suka tafi gidahen su su kuma suka kama hanyar komawa gida bayan ya ɓata mata lokaci yana hira da Asma'u sun dai rabu akan da yamma zai kawo mata ziyara da haka ta raka shi har wurin da take tsaye ta kalle ta ƙerere ta ce
"Toh likita ni na tafi a huta gajiya lafiya"ƙala bata ce da ita ba wanda bai mata daɗi ba dan so tayi ta tanka mata sai ta juye mata fitsara sai dai hankalin wayayye da ƙidahumi ba ɗaya ba dan haka ta ƙudiri yi mata rashin kunya duk dan ta ƙure ta dan ta amsa mata.
Chapter 12 · 0% Book details