← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 157

Sashe 56

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ran Hajiya Zeenat fes dan jin an rama masu abin da yaron yayi wa ƴaƴan su har ɓarin jiki take yi washegari yayi su koma germany dan ta labarta ma Hajiya Madina gwanintar da ɗan su yayi,.
A washegarin da wuri Bilal ya raka su airport a inda ta bar mai saƙo zuwa ga babban yayan su wato Jamil akan ya sanar da ƴanuwan su cewa nan da sati za'a yi ɗaurin auren Zaid da Bilkisu saboda Jamil ɗin baya nan ya sami tafiyar gaggawa,bayan jirgin su ya tashi ne Bilal ya kira apple ɗin sa ya sanar da ita aminiyar ta fah zata zama matar brother In-law nan da sati guda kamar ta yi hauka dan murna dan haka ta ce da shi zata bashi goron wannan albishirin da ya mata matuƙar sun haɗu.

***********

Already Hajiya Madina ta gama jin bayani daga wun Baha akan tattaunawar su da Bilkisu itama ta zage akan ba ma Bilkisun shawarwarin zaman aure har da nasihohin haƙurin zaman gidan miji,dama bayan 48hours da ta ɗibarwa Bilkisun ta sami ƙwarin gwiwar sanar da ita cewa ta amince zata auri Zaid hakan ba ƙaramin farincikin ya saka Hajiya Madina ba shi yasa ta ja ta a jiki ta shiga yi mata nasihohi because that is all she have for her at that moment duk wasu maganar gyara kuma sai bayan sun dawo gida dan she is absolutely sure cewa babu wani abin da zai shiga tsakanin ta da Zaid that she can guarantee shi yasa ta dage da koya mata abubuwan mata matan ma masu aure waɗanda suka amsa sunan su ota dai jin Ammin take yi ba wai ta gama yarda Zaid zai so ta bane ko da ya farfaɗo and yet bata gama concluding ba a zuciyar ta son sa take kokuma tausayin sa take..

Lafiya ƙalau suka dawo ƙasar germany a inda suka nufi apartment ɗin su abin da ya zamewa Dr Maher da Hajiya Madina kamar almara dan basu yi tsammani ba a nan prof ke sanar da su ai abin da ya kai su ne dama ya zo masu da sauƙi.
Bayan wasu lokuta sun huta sai Hajiya Zeenat ta matsawa prof akan ita fah lallai lallai sai sun gana da aminiyar ta dan abin na tsungulin ta ya ya iya da ita haka ya bar ta ta tafi asibitin wanda da ganin ta Bilkisu ta faɗa jikin ta kamar zata yi kuka ta shiga complaining wai tun da suka tafi bata kira ta ba sai ta mata bayani haɗe da ɗaga ta daga jikin ta tana mai ce mata zata dawo anjima bari ta gana da momma ɗin ta girgiza mata kai tayi sannan Hajiya Zeenat ta fita ta nufi ɗakin Zaid inda ta san zata ga Hajiya Madina ai kuwa sun yi murna a karo na biyu wanda Hajiya Zeenat ta kasa haƙura har sai da ta feɗe mata daga biri har wutsiya duk a cikin labarin babu wanda ya fi burge ta sama da fansar da Hakim ya ɗaukar masu daga shi sai maganar maganin Zaid ɗin wanda ya saka Hajiya Madina zubda ƙwallar farinciki after a long while ɗan ta zai farka kuma,hira suka yi sosai a nan Hajiya Zeenat ke sanar da ita ai ta kawowa Bilkisu kayan gyara na musamman sai abin ya bama Hajiya Madina dariya ta ce
"In ban da abin ki Hajiya Zeenat ina shi Zaid É—in ya gama samin lafiya har da zai nemi matar sa kar fa ki manta ko ya farfaÉ—o bai gama samin lafiya ba"sai itama Hajiya Zeenat É—in ta dara haÉ—e da cewa
"Hajiya Madina kenan ai yanzu zamani ya zo ma yaran nan da abubuwa daban daban ɗan nan kar kiyi mamakin in ya farka ayan kwanaki kaɗan ya fara nemar matar sa dan fah shi ɗin namiji ne wanda bai san daɗin mace ba the moment ya ga sun keɓe da yarinyar nan ya kuma san cewa matar sa ce a jin ki zai yi ignoring nata ne?ai sai dai bayan ya aikata mai gabaɗayan a maida shi kan gadon asibiti kin ga kenan is inevitable we can't tell"shewa suka yi suna mamakin yaran zamanin nan.
A ranar kuwa aka fara bankawa Bilkisu kayan gyara a same day aka fara treating Zaid da maganin da aka kawo daga Nigeria but basu bari asibitin ta sani ba dan suna iya hanawa su kuwa so suke É—an su ya farka.
Askin da ta damu a yi masa kuwa aka ƙi yi aka ce sai ta aure shi sannan ita ta mai dan tsabagen damuwa har Umman ta ta ma magamar askin bata sani ba because wani abu wai kunya kamar ƙaurace mata yake yi in zata yi maganar Zaid.

A nan Nigeria ana ta preparation na ɗaurin auren Zaid da Bilkisu a nan germany kuwa ana jiran farfaɗowar Zaid dan ana 4th day kenan da aka fara mai treatment tukunna prof bai sami kan sa ba dan haka bai sanar da Dr Maher abin da su Hakim suka aikata ba kuma bai ma nemi Hakim ɗin ba iyakan abin da suke jira shine farfaɗowar Zaid wanda a tsarin treatment ɗin suna saka ran kafin satin ya ƙare zai farfaɗo wanda kuma ya rage saura kwanaki biyu a ɗaura auren sa da Bilkisu ita kanta bata san me take ji dangane da auren ba daɗi ne kokuma tausayin kanta dan daga Ammi,Umma da Baha duk sai zuzuta mata maganar auren suke yi wai dan ta ji sauƙi da daɗi a zuciyar ta.
ranar da ya kasance ranar da su Dr Maher da Dr Muhammad zasu koma Nigeria dan washegarin ranar za'a ɗaura auren ƴaƴan su,a ranar bayan tafiyar su Bilkisu ta kasa sukuni ta rasa me ke mata daɗi gashi tana son ganin Zaid ɗin amma ta rasa yadda zata yi bata gan sa ba sai cikin dare ta sulale ta nufi ɗakin ta zauna tana kallon sa ta rasa me zata yi farinciki ko akasin haka dariyar murna ko akasin haka yanzu fah auren ta za'a ɗaura da shi what if he wakes up and said baya son ta ya zata yi?sai ta kuma mayar da dara daran idanun ta kan kyakyawar fuskar sa ta kasa furta komai ta kasa tantance feelings da take da shi ma Zaid,ƙura mai ido tayi tana kallon sa what is she feeling?the feelings is different is she actually in love with Zaid?sai ta ƙara girman idanun ta ta hanyar buɗe su sosai ta furta a zahiri
"Am i in love with Zaid Maher"?....

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

   *18*
     *_promise_*

  Abin mamaki me ke damin ta ne wai haka,ta yiwa kanta tambayar sannan ta ba ma kanta amsa "what else if not love"!!hakan ya sa ta shiga murmusawa ita kaɗai ba tare da ta san tana hakan ba mayar da idanun ta tayi zuwa kan suman kan sa da yayi yawa fiye da da sai ta ji kamar ta masife Hakim da ke kula da shi akan menene ba zai gyara mai fuska da kai ba gashi nan suman kan sa da na fuskar sa sun wuce misali ai hakan sai ya ƙara mai rashin lafiya,
  Zancen zuci take ta yi ita kaɗai daga bisani ta miƙe ta tofa mai addu'a sannan ta fara tafiya dan komawa ɗakin ta tana tafe tana juyowa tana kallon sa har dai ta kai bakin ƙofar kamar kar ta fita ta zuba mai idanun nan nata tana kallon sa cikin sigar da bata san yanda zata alaƙanta sa ba.
  Firgigit kamar an tsungule ta sai ta ga kamar baccin da take yi har yanzu bata farka ba haba in ba a mafarkin ta ba dama ta yaya Zaid zai yin yunƙurin yin wani abin ai sai dai a mafarkin dan haka ta saka kan ta zata fita ta kuma jin alamar faɗuwar abu wani juyin bori tayi a zafaffe ta buɗe idanun ta gaban ta na tsananta bugawa tana fargaban abin da zai biyo baya in har bai yi alama ba toh gaskiya ba zata taɓa yafewa zuciyar ta ba for making her imagination go beyond her limits.
Chapter 56 · 0% Book details