← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 157

Sashe 140

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

_"Ranar da Zaid ya farka har kuka tafi office ɗin doctor Gabby sakamakon kiran ku da yayi ya maku bayanin Zaid ya farka ya kuma tabbatar maku da cewa ya farka kenan kuka amince da hakan..toh ba duka bayanin ya maku ba ya ɓoye maku wani matsalar da zai zo ya faru da Zaid bayan wasu lokuta,ya ɓoye maku saboda ganin halin farincikin da kuka shiga...bayan kwanaki da sanar da ku sakamakon ne na koma office ɗin sa na mai bayanin nima relative ce na patient ɗin ya so ɓoye min gaskiyar lamarin sai dai na nuna mai ni ɗin doctor ce yana iya sanar da ni komai,,...bayanin da ya min shine....,,Zaid zai farka ya warke a fuska a ɗauka ya gama warkewa kenan har abada dan babu abin da zai yi da za'a mai kallon marar lafiya ko marar hankali sai dai babbar matsalar da ke cunkushe a kan sa ya fi wanda yake ciki aka mai magani a lokacin,,,da na nemi sanin ko menene wannan matsalar sai ya bayyana min komai kuma gaskiyar maganar shine bayan Zaid ya wartsake da kamar watanni takwas zuwa shekara ɗaya....Zaid na iya haukacewa sakamakon rashin tabbatar da komawar ƙwaƙwalwar sa inda ya kamata.....da na tambayae sa hanyar kaucewa hakan sai ya sanar da ni hanya ɗaya ce matuƙar muna son samim sa cikin yanayin mutani masu hankali,,hanyar ɗaya ce.,shine dole sanadin da ya saka sa cikin matsalar wannan sanadin za'a bi a kuma nemo makarin hakan...kenan dole wannan Mudan ɗin da ya bige Zaid a kai shine dai still zai kuma bige sa dan samin sauƙin sa gabaɗaya...,,a ranar da ya faɗi min haka hauka ne kaɗai ban yi ba dan har tambayar sa nayi da in akwai wata hanyar ya sanar da ni amma ya ce min in ba wannan hanyar ba toh sai dai mu kalle sa yayi losing mind ɗin sa dan in aka cigaba da ɗura mai magunguna da yawa wata rana yana iya zamowa resistant to the drugs and their effects..na rasa wa zan yi sharing matsala tare da shi tun ranar nake tsoron zuwar wannan ranar da zan yi witnessing Zaid na losing mind ɗin sa,ban sanar da kowa ba dan bana son ɗaga maku hankali bana so ku tsorata ku rasa kwanciyar hankalin ku tun ranar nake planning hanyar da zan taimaka mai dan ba zan taɓa barin sa ya koma ƙauyen nan ba bana jun zan kuma yarda ya ƙara haɗa ido da Mudan bare ya kuma repeating mai abin da aka ce sai an kuma yi,,i was hoping kafin time ɗin ya kai zan sami alternative other than wanda Dr Gabby ya ce sai dai har ranar da incidence ɗin ya faru ban sami mafita ba,a lokacin da Dr ke sanar da mu cewa i am 3weeks pregnant hankali na ya tashi weighing the fact that zan kai 9months ina ɗauke da cikin kafin in haife shi kuma zan yi rainon babyn and what Dr Gabby said was 8-12months later after the first surgery in ba'a yi abin da ya sanar da ni ba Zaid will definitely go mad,i never wished and pray to pass through my pregnancy all alone ba tare da support ɗin Zaid ba haka zalika ban taɓa mafarkin rising babyn mu ni kaɗai ba ba tare da Zaid ba,,a lissafe,mun kai wata ɗaya da kusan rabi which is equal to 6 and half months to expiry of cosmetic surgery da aka ma Zaid wanda in har hakan ya kasance kenan zan yi rainon cikin nan ni kaɗai kenan ba tare da Zaid ba saboda zuwa lokacin zai fara losing mind ɗin sa,,rasa abin yi nayi sai na kira likitan na mai bayani dan bana so in raini cikin nan ni kaɗai ba tare da miji na ba sai ya ce min toh mafita ɗaya ne in babu wanda zai aikata abin da ya ce min toh dole ni ɗin da nake kaucewa ni zan yi shi saboda a ceto sa daga shiga cikin halin da zai shiga nan ba da jimawa ba kokuma a yi transporting nasa zuwa chan germany su zasu yi exorcism ɗin nikuma na ƙi amincewa da wannan shawarar dan na san wahalar min da shi zasu yi sannan abin zai fito har ya dawo kunnen ku nikuma ba son ku sani nake ba dan ya sanar da ni jinyar ba zai daɗe ba so i thought if i should do it all alone kafin mu dawo gida zai farfaɗe gabaɗaya ba tare da Kun san da hakan ba shi yasa na ce mai zan yi ni da kaina...ba tare da nayi weighing wani side effect ɗin abin ba na aikata mai hakan saboda ya farka ya cigaba da rayuwar sa kamar kowani ɗan adam ta yadda ba zai sami fargabar faɗawa wani halin ba kp da nan gaba ne that was my only intension Umma i never intended to kill my husband i never planned to kill him i love him so much i can't bear seeing him going crazy that was why i did it please understand me i beg of you"_..

Da kuka mai matuƙar ɗaga hankali ta ƙarasa maganar saboda tana da ta sanin aikata wannan hukuncin ita kaɗai a nata tunanin sai ta ga kamar yin komai tsakanin su su biyun zai fi sirri da zuciya ɗaya ta yi hakan dan kar hankalin families ɗin su ya tashi bata san abin will turn out to be like this ba...

Daga Hajiya Madina har Hajiya Zeenat shiru suka yi kamar ruwa ya cinye su tabbas wannan abin da tayi akwai ƙuruciya cikin sa sai dai ita gani tayi kamar shine mafi sauƙin aikatawa fiye da fallasuwar abin sai dai kuma me ya sa Dr Gabby ya ɓoye masu ya ƙi sanar da su yau da a ce Bilkisu bata da ƙarfin imani tana iya kai sa wurin maƙiyin sa Mudan ɗin ya kuma yi mai kokuma ta kai sa germany ɗin su mai exorcism ɗin sai dai ita ta amince akan zata yi da kan ta tsabar son da take mai ba zata iya bari ya rasa abu mafi muhimmamci a rayuwar sa ba lallai wannan abin hikimar ubangiji ne..

ÆŠago ta Hajiya Madina tayi daga jikin ta ta kalle ta tsaf sannan ta ce
"Bamu ce kina son kashe mijin ki ba Bilkisu but kin san abin da kika aikata is risky what if the hotel receptionist didn't come on time?me zai faru?maybe da an É—ora maki alhakin rasa rayuwar sa muddin aka rasa ran sa,,,dan haka next time involve elders in your decision whenever you think of doing something as big as this okey"?gyaÉ—a mata kai tayi tana kuka so take ta haÉ—a idon ta da mijin ta amma babu halin yin hakan dan nauyin faÉ—in hakan take ji maybe a mata kallon muguwa mai son kashe mijin ta...

Kasa magana Hajiya Zeenat tayi sai dai bin Bilkisun da ido dan ta rasa me zata ce da ita game da abin da ta yi,kamar Hajiya Madina ta san abin da ke zuciyar aminiyar tata sai tayi karaf ta ce
"Kul Hajiya Zeenat na gama magana a bar ta haka nan ta huta ta ji da É—aya please"sai ta yi shiru tana kallon su,ganin Umman ta bata kuma É—aga mata murya ba sai ta kalli Ammin ta ce
"Ammi zan tafi wun Zaid please don't say no"...abin tausayi haka Hajiya Madina ta mata alƙawarin zata kai ta but under one condition akan sai tayi wanka ta ci abinci ta rama sallolin ta ta yi kwalliya ta amince ba dan ran ta na so ba sai dan tana gudun rasa damar da Ammi ta bata..
Chapter 140 · 0% Book details