← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 157

Sashe 157

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranar suna aka bayyana sunan baby da inkiyar sa ranar Hajiya Zeenat da Hajiya Madina baki ƙin rufuwa yayi barin ma Hajiya Zeenat da tun da aka yi haihuwar bata ga babyn ta ba her baby is now a mother,sai a hoto ta gan ta dan Bilal bai rabuwa da saka ta ɗaukar mai hotunan babyn da nata kanta sometimes...
An yi suna lafiya an rabu lafiya sai fatar samin albarka da ribar ɗa..a ranar da aka yi sunan ne da dare Bilkisu ta sami sarari ta kira Zaid a waya ya zo ta falon bayan su suka keɓe inda take tambayar sa labarin Asma'u dan tana buƙatar nemar yarinyar ta bata haƙuri..
Nan ya bayyana mata ai tun da suka tafi ɗin nan ya saka Dr Hussain ya mata alkhairi daga gare sa ta hannun shi Dr Hussain ɗin dan kar ta gane taimakon kuwa shine ya rinƙa assisting nata financially har ta haihu lafiya after ta haihu kuma an kai ma Mudan ɗan sai ita a nema mata makaranta ta fara zuwa since she have the zeal and passion in ya so a hankali tana karatun har Allah ya kawo mata mijin aure...
Yake ce mata
"Unfortunately,,ta haihu amma babyn ba rai sakamakon yawan damuwar da ta sakawa ran ta so Dr Hussain ya mata bayanin ni na turo sa ya kuma nemi da ta amince ya saka ta a school dan rayuwar ta ya inganta and she agreed he was able to put her through ya ma yayan ta bayanin komai and they agreed after long argument akan abin yayi yawa so presently da nake magana da ke Asma'u ta fara zuwa school yanzu da haka tana aji biyar dan dama tayi da fari kawai rashin natsuwa ne ya sa bata cigaba ba dan dole yanzu aka mai da ta baya saboda ta tuno abubuwan da ta manta and she is leaving much more better and comfortable more than the way you think"tausayin ta ne ya kama Bilkisu sai ta nuna mai inshaAllah suna gama puerperiun nasu zai raka ta su gana da Asma'u she have to contribute positively to her life..
Hakan ya ma Zaid daÉ—i and he praised her for the zeal she got...

****************

Yau da gobe bai bar komai ba life was a success for Asma'u dan yanzu tana matakin ƙarshe a ajin JSS har sun rubuta Junior WAEC ɗin su sakamako kaɗai suke jira,sosai tayi concentrating tana karatun ta dan ta san shi kaɗai ne legacy nata da wanda zata bar wa ƴaƴan ta as for the relationship tsakanin ta da ɗan birni babu abin da ya sauya tana mutunta sa fiye da da shi da matar sa dan sun mata alkhairi ba adadi bata da abin cewa gare su sai addu'ar gamawa da duniya lafiya,sam bata sauraron maza a cewar ta ilimi ta fiye mata dan ta gwada sauraron ɗa namiji amma bai bar mata tambari mai kyau a rayuwar ta ba a kullum in ta tuno da rayuwar ta na da a ƙauye sai ta ji kamar ta tariyo lokacin ta goge duk kurakuran da ta yi a lokacin but nevertheless yanzu ma Alhamdulillah dan bata rasa ci,sha,lafiya da sutura ba tana nan dai tana aikin ta a gidan Hajiyar birni wato inda yayan ta yake aikin gadin sa lafiya ƙalau suke zaune babu tsangwama bate hantara she can say that life is extremely sweet for her bata da wata danuwa sosai yanzu....

As for Aslam kuwa ya rungumi matar sa suna zaman su lafiya yayi setting hospital É—in kan sa yana running kuma he has 1 kid and matar sa na da cikin na biyu shima kam bai da wata matsalar rayuwa apart from taking care of his family..

Lukman ya sami mata ya aura 2 years back kuma har Allah ya albarkace su da albarkar aure sun sami baby girl mai sunan Hajiya Zeenat abin sai Alhamdulillah.
Yayin da Afzal da Bilal ke da Æ´aÆ´a bibbiyu dan kamar kusan tare matayen su ke É—aukar ciki,su dai Ammi da Umma kam abin gaba ya kai su a tara masu jikoki..

Hakim was able to invent the mechanical electro machine mai kula da lafiyar bugun zuciyar ɗan adam yayi lunching machine ɗin a nan ƙasar tamu ta Nigeria kuma ya sami alkhairai da recognition ba kaɗan ba presently ana anfani da machineries ɗin a cases na cardiac patients wannan babbar cigaba ne a gare su shi da ahalin sa..he has a girl he wanna marry ba'a rigada an yi fixing date ba sai mu ce Allah ya sanya alkhairi..
Babban yaya jamil kuwa matar sa ta haifi wasu twins É—in after baby Zarah,abokantakar su shi da Dr Zaid sai abin da yayi gaba very smooth relationship..

Hajiya Madina da Hajiya Zeenat kuwa haɗe da mazajen su rayuwa ta masu daɗi sun tara jikoki ga ƴaƴa abin tubarkallah dama akan bar wani abin dan wani abin a yanzu kam sai su kai wata shida basu tafi yawon buɗe idon ba dan jikoki kam basu bari a kowani sati nan suke yini wasu ma su kwana masu ƙyuya ke bin iyayen su su koma gida so they can also say that life is comfortable with them...

***********
Gudu yake ana bin sa da wandon makarantar,haka kamar tayi kuka ta ɓata fuska ta shiga kiran sunan sa
"Khalifah ka rufa min asiri kar mamin ka ta fito ta ga baka shirya ta tsige ni"sai ya saka mata dariya yana gudu sau uku suna rounding parlorn ya ƙi tsayawa sai chan ga wata serious heavily pregnant woman na saukowa cikin shigar doguwar riga da gyale ta yi rolling a kan ta,flat shoe ne a ƙafar ta dan ƙafar baya amsar takalmin gayu sakamakon kumbyrin da yayi na masu nauyin ciki..
Tana kallon su har yaron ya haÉ—a ido da ita yana faÉ—in
"Mami kin ga Lauretta tana cewa in kika fito zaki tsige ta ko,,mami menene tsigewa"?yaron ba dai wayon tambaya ba komai ya gani sai ya tambaya ita kam bata iya mai dan ji da kan ta take sai dai in Abban sa na gida ya biye mai
"Khalifah ban sani ba ke kuma Lauretta zam dawo maki ne"sai ta kaurara murya tana faÉ—in
"And you,,,koma ka tsaya a ƙarasa shirya ka tun kan rai na ya ɓaci da kai"salin alim yaron ya kai kan sa aka saka mai kayan makarantar sa sannan aka ɗora mai da wata ƙaramar lab coat,pink paediatrics stethoscope aka saka mai round his neck aka sagala mai eye glasses kamar medicated amma ba medicated bane..
Sak yaron ya fito a siffar doctor sai mahaifiyar nasa ta zo kusa da shi ta duƙa da kyar ta manna mai kiss a goshi tana faɗin
"That's my boy let's go Abba is waiting outside"daga haka suka fito tare da shi suka doshi wata red tinted car da ke faman ƙyalli,..
Buɗe ƙofar aka yi daga ciki ta zauna ta ɓangaren da aka buɗe ɗin sai aka fito aka zaga aka buɗe fannin baya aka saka boy ɗin daga haka aka tayar da motar suka bar gidan..
"My girl amma dai wannan cikin ƴan biyu za'a sulluɓo mana ko kin ga tsakanin cikin nan da haihuwar khalifah is exactly 4 years"hararar sa tayi tana faɗin
"Hero in ka ishe ni da zancen twins ɗin nan ina iya barin ku ku tafi foundation ɗin nan ku kaɗai ka ga ba zaku sami abin teasing ba ai"ƙumshe dariyar sa yayi dan wannan cikin nata ba kamar na fari ba saurin masifa ne da ita ga saurin fushi ko a office yake in ta kira sa bai ɗaga ba ta rinƙa faɗa kenan gashi shi kaɗai ke running hospitals ɗin dan Afzal kam ya ce bai ga ta zama a nan ba Canada ya koma shi da matar sa toh taimakon sa Hakim ne in yana da time amma duk ayyukan shi ke handling nasu sannan yayi handling masifar ta da ita kan ta.

Daga baya yaron ya ce
"Abba haihuwa Mami zata yi"juyowa tayi ta ce.
"Ba'a sani ba"ai ko uba da ɗan suka saka mata dariya sai ta ɓata fuska alamar ran ta ya ɓaci cikin sauri ya ce
"Am so sorry Dr Hajiya Bilkisu Muhammad Zaid ki gafarce ni ni da ɗa na bamu ƙarawa"kwafa tayi daga haka suka cigaba da tafiya har suka zo inda zasu zo ɗin inda ya kasance wani NGO foundation ne da Bilkisu ta saka Zaid buɗewa saboda a rinƙa taimakawa mutani tun daga kan Asma'u she learnt to become more helpful and kind to people..
Wurin cike yake da yara kala kala sun saka kayayyaki na different fields lawyers,nurses,doctors,pilots,Engineers,Police,soldiers duk kowa da presentation É—in da zai yi shi yasa Maher junior wato khalifah ya saka na field É—in iyayen sa dan that is what he wanna become in future..
Sun yi presentation ɗin su lafiya an bada gifts da awards Bilkisu da mijin ta haɗe da ɗan ta suka kamo hanyar gida already ta gaji tausa take buƙata kafin tayi bacci dan cikin nan na bata ciwon kai..

Toh gashi nan dai ciki ya girma haihuwa yau ko gobe ko me za'a haifa wannan Allah ne masani....

*Alhamdulillah MashaAllah*

*_Allah nagode maka da ka nuna min ƙarshen wannan littafi mai taken IYA RUWA FIDDA KAI (The Love Saga)lafiya kamar yadda ka nuna min farawar sa lafiya ya Allah ka gafarce ni kurakuran da ke ciki ka sa an amfana da abin da ke cikin sa na alkhairi*_

*_Ni Siyama ibraheem nake maku fatan alkhairi sai mun haÉ—u a wani karon cikin sabon littafi na mai taken
BAMBANCIN ƘASA!!! InshaAllah but is not coming any moment soon amma zan ce da ku kar ku bari a bar ku a layin baya dan kuwa zai zo ne da salo na daban siga mai birgewa,till then,na barku lafiya.._*

*_S,Ibraheem_*
Chapter 157 · 0% Book details