← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 157

Sashe 61

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

  "Bilkisu calm down talk to me and stop crying me ya faru"??cikin kukan ta ce da shi
  "Yaya tambaya ta yayi in gaya mai abin da ya faru and i narrated everything bayan na gama ya ce bai yarda ba sai na sanar da shi komai,,,yaya ba zan iya ba akwai ugly parts da ba zan iya sanar da shi su ba amma ya natse sai na gaya mai Yaya i have to leave him all alone in that room dan ba zan iya cigaba da kallon sa yana cikin pains ɗin da ya shiga ba but i know by now su Ammi sun ba shi haƙuri na san zai haƙura in suka mai magana kaima in ka mai magana zai janye son sanin labarin please yaya help me na kasa composing kai na"!!tausayin ta ne ya kama sa dan duk a halin ruɗani take maganganun gashi bata da labarin dawowar iyayen nasu dan daga dukkan alamu bata san cewa sun kamo hanyar dawowa ba,daga ita sai Zaid a ƙasar germany babu wani ɗan uwa ko aboki dole su yi tolerating juna haɗe da nunawa junan su kulawa har Allah ya sa Zaid ya sami lafiya su dawo gida.
"Baby kina ji na"??ta ansa da
"Eh ina jin ka yaya"!!sai ya ƙara sassauto da mutyar sa ta yadda zata ji komai cikin sauƙi

"Baby kin ga su Ammi sun kamo hanyar dawowa gida already yanzu a ƙasar nan babu kowa naku daga ke sai shi kuma kin san shi ɗin ba lafiya ce da shi dole ya rinƙa samin kula daga gare ki dan ke kaɗai ya sani bai san kowa ba duk wasu lalurorin sa da ɗawainiyar sa sun komo hannun ki daga jiya har izuwa ƙarshen rayuwar ku kin chanza daga abokiyar aiki,makwafciyar sa kin zamo matar sa abokiyar shawarar sa abokiyar rayuwar sa,,nauyi ne ya ƙaru a kan ki ba kaɗan ba dan haka ina so kiyi concentrating wun bashi kula dan sai kin bashi isashiyar kulawa ne zai sami natsuwa ya warke yadda ya kamata ba tare da an sami mishkila ba,kar ki damu da individual differences da ke tsakanin ku duk waɗannan zaku iya mending nasu in har kuka cigaba da zama tare dan haka ina so ki sani in har kika saba mai da rayuwar ƙarya tun yanzu a kan sa zai ginu in ma na gaskiya ce duk a haka zai ginu so i guess tun yanzu ki sabar masa da faɗin gaskiyar lamari ko da kuwa ba zai mai daɗi ba gwara ya sani daga gare ki than ya ji daga wun wani ko outsider da fatan kin fahimci maganganu na baby sis"??ƙamewa tayi a zaunen dama sun tafi ne ba su sanar da ita ba??yanzu ita ya zata yi da Zaid?yaushe ta gama kula da kanta har da zata fara kula da Zaid all alone?me yasa suka mata haka ne yanzu ko Baha bata tsaya ba suka tafi suka bar ta ita kaɗai tayi nursig kanta sannan tayi nursig Zaid??ta ina zata fara?..

Duk a cikin zuciyar ta taje waÉ—annan tunane tunanen mantawa tayi da yayan ta na kan layi har sai da ya kuma yin magana
"kina ji na kuwa Bilkisu"firgigit ta dawo daga tunanin ta ce
"Eh na ji yaya,,amma yaya su Umma basu kyauta min ba ta yaya zan fara kula da kaina in kula da Zaid nima fah convalescence patient ce ba gama warkewa nayi ba ina buƙatar kula ta musamman daga wun wani ta ina zan fara i can't...i just can't do it all alone brother please do something"...sai ya rasa abin faɗa mata gashi sai kuka take yi
"Baby stop panicking stop crying komai zai zo maki a daidai da yardar Allah all ypu need to do shine ki natsu kiyi studying Zaid da kyau ki san abin da ran sa ke so da wanda baya so sai ki fara exhibiting but crying won't solve the problem ki natsu zaki iya handling komai baby sis you have to learn how to start leaving alone dan zaki fara family É—in ki ne so bai kamata ki fara da tsoro ba henceforth be back completely dan Dr Bilkisu Muhammad Sulaiman da na sani is a conquerer despite the fact that her tittle is Baby doctor but she is actually not a baby when it comes to fighting for her goal she ain't a loser she always win humm dan haka ki daina faÉ—in wai ba zaki iya ba sure you can kin ji"??
Jan hanci tayi tana jin ta sami ƙwarin gwiwa..
"Nagode Yaya Allah ya saka da alkhairi you are special to me nagode yaya bari in duba shi dan ban san su Umma sun tafi ba"
"Shikenan baby sis Allah ya shige mana gaba"
"Amin yaya nagode sai anjima"ta kashe wayar haɗe da sauke ajiyar zuciya ta kwanta da baya tana kallon sama.tunanin maganar su da yayan ta take yi sai t ga gaskiya ƙarara a zancen nasa tabbas dole a kan abin da ta ɗora sa zai ginu dan dama namiji da abin da ka sabar mai zai cigaba da gudanar da rayuwar sa.
A baya tayi tunanin jan jikin ta daga nasa ta so ne ta rinƙa guje mai ko da wani abin ne ya taso sai ta yi sama sama ta nisance sa sai dai yanzu da ta ji babu wanda ke tare da su da zai taimaka mai akan harkokin sa wanda ya haɗa da su lalurorin sa kama daga cin abincin sa kula da jikin sa shan maganin sa hira tare da shi ta yadda zai ƙara mai kuzarin farfaɗowa gabaɗaya sai ta ga ya kamata ta rinƙa ɗauke masa waɗannan abubuwan he have no one to do it sai ta ji tausayin sa na tsirga ta dan haka wuf tayi ta tashi tana duba jakar kayan shafawar ta ta fiddo ƙaramar abin powder ta buɗe mirror ta ɗan yi touching kwaliyar fuskar ta kaɗan dan bata so ya gane cewa tayi kuka sai ta ɗan shafa lip moisturizer ta kuma bin jikin ta da turaren jiki mai sanyin ƙamshi sannan ta ta chanza kayan jikin ta zuwa riga da wandon Dior pink colour ta ɗora after dress mai igiyar ɗaurawa black colour mai adon duwatsu ƙanana ta nemi ƙaramar gyale baƙa ta yafa a kan ta takalmin valentino na mata ta saka mai ɗan tudu kaɗan sai ta kuma bin jikin ta da perfs kala biyu kacal sannan ta ɗau wayar ta zata fita kenan ta hangi takardar da Ammi ta ajiye mata sai ta koma ta zauna ta ɗau takardar ta warware tana duba abin da ke ciki cikin natsuwa.
Har ƙarshe ta karanta wasu kalmomin da Ammin tayi amfani da su sun mata nauyi har take jin kunya ita kaɗai..
Most of the things contained in the later shawarwari ne akan zaman ta da Zaid haɗe da tunatar da ita matsayin ta a wun Zaid ɗin sai kuma shawarar kar ta yarda wani abu ya shiga tsakanin su muddin bata gama amfani da kayan da aka saba bata ba ta sanar da ita unda ta ɓoye mata su cikin trolley ɗin ta ne da ke waldrop na ɗakin chan cikin ma'ajiyar ƙarshe a nan ta ɓoye mata..
Da ta gama karanta wasiƙar sai ta nannaɗe ta nufi waldrop haɗe da budewa ta ajiye papern a back zip ɗin jakar sannan ta mayar ta rufe ta ɗan ƙara kallon kan ta a wayar ta sannan ta nufi hanyar waje,tunani ne fal a ran ta dan sai yanzu ma ta tuna wai bata sanar da shi matsayin ta a gare sa ba ko ya zai ɗau maganar Allah ne ya sani..

Da fargaba ta doso ɗakin tun daga ƙofar ɗakin take kallon sa ya jingina da pillow idanun sa a buɗe yana kallon gefe ɗaya so she felt awkward abin da ta mai bai dace ba shi kaɗai ta bari tayi tafiyar ta ba tare da ta tsaya ta saurari damuwar sa ba what if he hasn't taken his drugs mr kenan tayi a matsayin ta na matar sa ai wannan babban abin kunya ne a gare ta sai dai ta daure ta shiga ɗakin fuskar ta ɗauke da murmushin ƙarfin hali she is feeling clumsy already dan ta san bata kyauta mai ba wai ma tukun me ke damin ta ne haka she get confuse easily kuma duk saboda tunanin Zaid ne.
Tsaye tayi daga tsakiyar ɗakin ta ƙi ƙarasawa sai ya lura ya kira ta
"Bilkisu akwai wata matsala ne"??very calm and gentile yayi maganar and so he drove her crazy and insane ita dai bata san ya zata yi da Zaid ba sam she doesn't feel comfortable in har ya kira sunan ta kai tsaye haka kuma gashi yanzu kamar da gangan yake kiran sunan dan ya ga yana causing mata effect..

"A'a babu wata matsala dama so nake in sani ko ka sha magungunan ka na safe na ga har 11am na son gotawa"!!
Na sha magunguna na na safe??strange ya faɗa a zuciyar sa shi so yake ma ya san a wace ƙasa suke but bata yarda ta bashi opportunity ba hakan ba ƙaramin danuwa ya janyo mai ba shiru dai ya mata yana jira ya ga iya gudun ruwan ta.
Jin bai ce komai ba sai ta ji ta tsargu dan haka ta bar shi a É—akin ta nufi inda nursing personnel suke ta masu kwatancen É—akin sa haÉ—e da tambayar ko an yi serving masa morning drug nasa..
Dubawa suka yi suka tabbatar mata da cewa ba'a bashi ba dan bacci yake yi sai ta ji mamaki wani irin bacci bayan ta san idanu biyu ta bar sa kuma ta dawo ta tarar da shi a jingine alamar dai ba baccin yayi ba maybe he pretended to be asleep dan kar a takura shi,,umartar su tayi akan su zo su bashi ya farka dan haka É—aya daga cikin su ta bi ta har zuwa É—akin sa a inda suka gansa kwance shiru fara harhaÉ—a magungunan tayi har ta gama ta matsa zata nufe sa dan bashi ya sha ai Bilkisu bata san lokacin da ta dakatar da ita ba cikin kakkausar murya
Chapter 61 · 0% Book details