← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 157

Sashe 38

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya jikin na sa"?a nan suka É—an yi jimm sai ta kalle su haÉ—e da ajiye kofin ta ce
"Is okey kar ku damu zai tashi nan ba da jimawa inshaAllah"daɗi suka ji lallai tana da ƙarfin zuciya ita da yanzu ta farfaɗo but har tana da ƙarfin reassuring nasu as a doctor,rungume ta Ammi ta yi ta ce
"Allah ya maku albarka ya kuma kare mana ku daga yau sai yau babu ku babu outreach ko da a nan asibitin ku ne ba ku kuma yi"!a halin jimami ake amma sai da maganar ta ya saka kowa darawa kaɗan ciki kuwa har da Bilkisun dan a nan ta fara tunanin shine fah ya natse na maganar outreach ɗin nan ita kuma shegen girman kai ya hana ta ƙin yarda akan ba zata bi shi ba shi dan ya hukuntata ya shirya tafiyan but at the end of the day abin sai ya juye masu he end at the receiving end ohh Allah ka bashi lafiya,,a zuciyar ta ta yi wannan analysis ɗin..

Ranar murnar iyayen baya misaltuwa dan haka a nan ɗakin na ta suka kai har dare ta ce da su zata tafi ganin shi suka ce a'a ta bari har washegari bata gama farfaɗowa ba dan haka ta haƙuran Bilal ne ya taya ta hira har dare wuraren 11 sannan ya mata goodnight ya tafi dan hutawa yayin da Ammi da Hajiya Zeenat suka kwana a nan dan a daren aka so yi mata wanka ta ƙi ta ce zata iya da kan ta har tsiya suke mata wai in bata yarda an mata yanzu ba ma ai akwai na jego dole ma ta yarda jin su ta yi amma ko za'a haɗa ƙasa da sama ba zata yi wannan wankan jegon miyatar da ake yi ba haka kawai ta janyowa kan ta matsala.
Da ƙyar ta yi wankan aka saka mata rigar bacci mai kauri da hula abinci ta ce sai washegari dan ta sha energy booster kafin su shigo haka suka ƙyale ta ta kwanta suma suka kwanta. Oh rayuwa wai su ne ke jinyar yaran su biyu a asibiti asibitin ma ta wata ƙasa lallai yaron nan ya guji haɗuwar su da shi...

************
Kwanaki biyu aka ɗauka ana koya mata tafiya dan joints ɗin ta duk na mata ciwo sakamakon doguwar kwanciyar da ta yi a course of minor exercise ɗin ne ta yi saloli wanda ya taimaka mata ta kuma jin jikin ta ya sake mata har take fatan Allah ya sa anjima su fita dan ta samu ta yi sneaking zuwa ɗakin Zaid because tunanin sa ya zame mata obsession tun da ta farfaɗo su kuma sun ƙi kai ta dan ganin sa..

A yammar ranar ne jirgin su Hakim ya iso dama Bahajjatu ta hana kar a sanar da Bilkisu zuwan su she want to surprise her dan Hakim ya sanar da Ammin su tare da Bahajjatun zasu taho har da faɗan kar ya kawo mata ita ta zo tana portraying masu madness a asibiti but sai ya mata bayanin ai ta shiru ƙyale shi kawai tayi..

It was a big surprise to her dan ta ga babbar ƙawar ta da zata iya sharing damuwar ta da ita.
After all the oyoyo and everything sai suka keɓe ta sanar sa ita damuwar ta dama ƴar taya ɓera ɓari ce sai ta nemar mata hanyar fita kamar ɓarayi ta yi directing nata zuwa hanyar office ɗin doctor kamar dai yadda Bilal ya nuna masu da suka zo dan bai bari sun ga Zaid ba dan gudun tashin hankalin da zasu shiga a ce da zuwan su sun riski matsala irin wannan bai kamata ba..

Thank goodness ta sami doctor É—in but he was amused ganin ta bayan ya san cewa ita patient ce sai ya ce ta zauna ta zauna
"How may i help you"ya faɗa feeling free da ita sai bata ɓoye mai komai ba akan tana son sanin komai ne game da ɗayan patient ɗin ta kira sunan sa at first the doctor was like can he tell her everything about the patient ko dai ya ɓoye ne da ta ga haka sai ta mai bayanin cewa daga ita har shi ɗin da ke unconscious doctors ne har ta ɗan kawo mai scenario da ya faru da yayi sanadiyar zuwan su,a nan hankalin sa ya kwanta sai yayi narrating mata duka findings ɗin su she was shedding tears but bata san cewa crocodile tears take shedding ba real tears ba sai da ta ji ɓoyayyen solution da likitan ya sanar da ita a nan ta yi zaman dirshan ta shiga risgar kuka ba ji ba gani haka ya rinƙa bata magana har dai ta tashi ta tambaye shi ɗakin da Zaid yake ya mata describing bai da nisa da office ɗin sa ta fita tana haɗa hanya da ba gama warwarewa tayi ba tana dafa bango ana kallon ta ana mata sannu bata amsa kowa har ta iso ɗakin ta hango shi ta waje under control of machineries and devices ta tuna da final solution da likita ya gaya mata sai kawai ta fashe da kuka tana yi tana jujjuya kai tana cewa
"Noo noo..Zaid please noo i can't witness that inalillahi wainaillaihir raji'un please Zaid don't accept the defeat fight it please"...

*_I guess this chapter is somehow wow and somehow oh no u need not to worry just keep on following sequentially you shall enjoy the love saga i bet you,catch yah tomorrow mi Amor_*

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
#vote
#comment
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

   *14*

  Giftawar ta kawai bilal ya gani sai yayi saurin bin bayan ta a hankali ya rinƙa tracing hanyar da ya hango ta har dai ya iso ƙofar ɗakin da take tsaye wato dai ɗakin Zaid,jim yayi yana kallon ta tana bashi tausayi dan duk maganganun da take yi yana jin ta rasa abin faɗa mata yasa yayi shiru har dai ya ga abin na son fita a kan dausayin mai hankali.
  She was crying with great agony and pains haɗe da hatred na Asma'u dan ita gabaɗaya ta ta'alaƙa laifin komai ne a kan Asma'u because if not for her babu ta yadda za'a ma Zaid wannan aika aikar dan haka with each passing seconds of her life yana tafiya ne da tsananin tsanar Asma'u a ran ta tsana ce mai ƙarfi wacce bata jin zata iya yafe mata saboda taɓa lafiyar Zaid da aka yi daidai yake da hukuncin takura mata walwalar ta da sukunin ta a duniyar ma baki ɗaƴa.

Any word she speak out rhyme with her heart wishes she just pray that he wakes up at the right time if not da akwai babbar tashin hankali a ƙauyen koma gabaɗaya ba ma gidan su Mudan da Asma'u kaɗai ba..
   Tana tsaka da kukan ta mai tsuma zuciya ta ji an taɓa ta sai ta dakata da kukan tana share hawayen ta kafin ta juyo ta kalle sa sai ta ga Bilal ne ba amfani in ta ɓoye masa damuwar ta sai ta cigaba da kukan tana nuna mai ɗakin Zaid tana kuka kamar ba ita ta farfaɗo daga jinyar sama da sati biyu ba jan hannun ta yayi dan su bar wurin saboda kasancewar su a wurin ba komai zai haifar mata ba apart from more heartache da increase hatred wanda is not good for her health.
  Tana kuka tana fincikewa yana jan ta da kuka da fixge fixge suka koma ɗakin ta inda a nan ne suka yi kiciɓis da Hajiya Madina dan dama daga neman ta ta fito ko da ta ga bata nan babu wanda ya fara zuwar mata rai sai Bahajjatu dan ita kaɗai ce marar jin maganar da zata iya fitar da Bilkisun shi yasa ta rinƙa trying line nata sai dai bai shiga dan ita ma Bahajjatun fita tayi dan neman apple ɗin ta because zuciyar ta fes yake and she is praying for her big bro to wake up as soon as possible,suna cikin hirar ne sai ya ga kamar gilmawar twin sis ɗin sa cikin tashin hankali sai yayi saurin biyo ta inda yayi discovering abin da take kallo har ya saka ta kukan da take yi shi ya sa ya ja ta suka bar wurin gudun kar Bahajjatu ta gano ɗakin da yayan ta ke ciki because he is sure ahe will definitely create a scene dan bai san dalilin da yasa Afzal ya bar ta ta biyo Hakim ba alhalin duk sun san halin ta.
  Ganin Bilal tare da ita ya sa Ammi sauke ajiyar zuciya kafin ta ce
  "Bilal ina ka kai ta ka san bai kamata ta rinƙa fita mai tsayi ba ba tare da guidance  na kowa ba kuma ka fi kowa sanim halin da take ciki i see no reason why you should take her out of the room"!!ita fah magana take yi ba tare da ta lura da cewa ita Bilkisun kuka take risga ba sai da ta fara wata maganar sannan ta lura
Chapter 38 · 0% Book details