← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 157

Sashe 69

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai wuraren 8:40pm suka iso gida already sun tsaya a Nature Reserve sun gabatar da sallar zuhur da asir dan haka da dawowar su kowa ɗakin sa ya nufa ya yi freshen up suka gabatar da sallar magrib da isha'i daga haka suka fito falon cikin shigar kayan barci nata coffee colour mai ƙyalli na sa red colour mai laushi duk da takalman su ita ta saka gyale ta yane kan ta shi kuma ya fito da wayar sa a hannu yana latsawa kamar dai waya yake son yi da wani ko wata.
Kusan a tare suka fito dan jubilation É—in da suka yi yau ya saka su deciding cin abincin dinner tare a falon shi yasa ma suka bar abincin a falon.
Saman centre carpet da ke shimfiÉ—e a falon suka zauna yayin da ya ajiye wayar sa a gefen su.
Shi ya buɗe well packaged pack ɗin ya yi unwrapping foil papers da ke lulluɓe da wasu abin ciye ciye,a gaban ta ya baje mata nata haɗe da miƙo mata spoons da ke nanaɗe a cikin toiletry yana mai ce da ita
"Bismillah"!É—an murmushi tayi sannan ta amshi spoons É—in ta buÉ—e bata wani tsaya jiran sa ba tayi bismillah ta fara cin abincin,shima sai ya fara ci.
Sun yi maintaining good table manner babu magana har sai da suka kammala sannan tayi clearing wurin shi kuma yana zaune ya É—au remote yayi booting plasma dake falon.
Kafin ta dawo daga disposing dirt ɗin already ya hakimce saman kujerar yana kallon wani program na shirin doctors suna surgery an kai tsakiyar shirin dan bai ƙunna da wuri ba.
Har zata wuce ta ma buɗe baki da niyar ce mai sai da safe sai ta ga abin da yake kallo,abu nasu maganin a kwaɓe su sai ta dawo da baya ta zauna kan ɗaya kujerar dake fuskantar nasa dama a tsakiya plasma ɗin yake sai kujerun a gefe da gefe.
Ko da ya ga ta dawo ta zauna sai ya kalle ta ya ce
"Ba zaki yi bacci bane?aren't you tired"??kallon sa tayi kamar ba tare suka yi yawon ba after all shi ke buƙatar hutun ba ita ba dan shine marar lafiya kuma gobe suna da zuwa asibiti wun doctor saboda zai fara checkup ɗin sa.
Da murmushi shimfiÉ—e kan fuskar ta ta ce
"No..not at all...in fact,kai ya kamata a ce mawa ya huta,dan gobe zamu fara zuwa checkup"!!sai a nan ya haÉ—a ido da ita dan she speak to him so nicely ga tausaya a muryar ta yayin da tale maganar.
Glance yayi sai ya gyaÉ—a kai ya cigaba da kallon kamar yadda itama ta mayar da hankalin ta kan plasma É—in suka cigaba da kallon.

Basu bar falon ba sai da suka ga abin da ya turewa buzu naɗi dan a idon su aka yi suturing komai aka gyare patient ɗin kafin a tafi short break wanda yayi daidai da ƙarfe goma shaɗaya da mintuna hamsin da biyar.
Kashe tv yayi ya juyo gare ta ya ce da ita
"Sai da safe"itama ta ce mai sai da safen,kowa yayi ɗakin sa dan barci ne cunkushe a idanun su kawai son ganin ƙarshen theater ɗin suke son yi shi yasa basu kwanta ba.
Da baya ta kwanta a kan gadon tana mai lumshe idanun ta sai hamma take ta yi akai akai tana son tambayar sa hotunan da suka yi É—azu but barci ya hana ta sai kawai ta bari akan washegari zata tambaye sa kafin su tafi asibitin.
Babu jimawa bacci yayi gaba da ita ai kuwa a yadda ta kwantan nan a haka tayi baccin hankali kwance ta ke baccin ko ƙofar ɗakin bata ƙulle ba iya turawa tayi ta bar shi a hakan..

A nasa ɓangaren ma kusan hakan ne ya kasance dan bayan ya shiga ya kwanta sai ya janyo wayar sa da nufin saka alarm dan so yake ya riga ta tashi dan tun da aka yi hospitalizing na sa bai dawo daidai ko ba sallar dare ba kasafai yake tashi yin ta ba hakan kuwa ya samo asali ne a sakamakon effect na maganin yamma da yake sha a kullum again ear device ɗin da ke sagale a kunnen sa ya taimaka wun saka shi yin bacci har fiye da misali dan sosai device ɗin ke taimaka mai wun rage jin sauti sai ya ke saminbacci sosai wanda hakan ke shagalar da shi.

Yana danna hasken wayar dama ba a security pin take ba,fuskar su ne ya fito a hoton da suka yi na ƙarshe a Nature Reserve wanda hoton ya kasance kamar selfie ne wanda ya ɗauke su suna murmushi sai ya shagala yana kallon hoton kawai sai kira ya shigo mai wayar kai idanun sa yayi ya sauke kan sunan mai kiran sai ya ga Ammin sa ce dan haka yayi saving sunan my Ammi ɗauka yayi yana mamakin ko lafiya cikin daren nan take kiran sa.
Kafin ya ce wani abin har ta riga sa ta hanyar ce mai
"My boy ina É—iya ta take ne wai tun É—azu nake ta kiran layin ta but bata É—auka kai kuma taka wayar bai shiga sai yanzu na yi sa'a ina fatan dai bata fara barci ba"?haka ya ji tambayar daga sama sai ya yi shiru yana tunanin me zai ce mata dan kam bata da masaniyar ba É—aki É—aya suke rayuwa ba shi da Bilkisu ba hala ma ta rigada ta fara baccin tun É—azu yanzu me zai ce da ita in ta nemi sanin ba'asin rashin haÉ—a É—aki É—aya da basu yi ba a matsayin su na ma'aurata,idan ta yi tunanin raina ta yayi fah me zai ce da ita dan ta fahimce sa..
Jiyo muryar ta yayi tana kiran sa
"Zaid kana ji na kuwa"?firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi cikin sarƙewar murya da ruɗu cikin zance ya ce
"Na'am na...aa.mm Ammi..Am..mi ina jin ki"..da mamaki ta ce
"Zaid lafiyar ka kuwa"??da sauri ya tari numfashin ta ta hanyar amsa mata da
"Ehh..Ammi,lafiya ta ƙalau"??sai kuma ta yi wani hangen a matsayin ta na babba tunanin nan ne yasa ta basar haɗe da sakin murmushin manya wanda ya fito fili har yana iya jiyo ta sai ta ce
"Oh common my boy is normal it happens guess what?i understand your state of being ba damuwa gobe ka haÉ—a ni da Bilkisun ok,goodnight my boy"zata sauka a kan layi sai yayi saurin hana ta dan ya gano abin da take nufi wanda sam baya jin Ammi ta ma san matakin auren su da ba zata yi wannan doguwar tunanin ba.
"Ammi tsaya bara na tashe ta dan ta fara bacci"a karo na biyu da ya ma Ammin sa ƙarya na fari akan Bilkisun ne dai ranar da ta kira sa a asibiti tana tambayar ko ya sha maganin sa ya ce a'a ta tambayi dalili dan ta san alhakin Bilkisu ne bashi nigh medications ɗin ta but sai yayi ƙarya ta hanyar cewa itama ai rashin lafiyar ta ne yake son tashi saboda sanyin da ake yi a garin gashi yau a karo na biyu ya kuma yi mata ƙarya all because of Bilkisu.
"My boy ku kwanta abin ku gobe zamu yi magana".sai ya ce
"No Ammi lemme wake her dan gobe zamu tafi checkup bana jin zamu sami time mu yi waya"..sai ta ji daɗi wato har closeness nasu yayi nisa haka hala ma ba fitan kaɗai suke yi zuwa asibiti ba maybe har zaga gari suke yi tare sai kuma ta ji wani excitement ya shige ta ko dai yaran nan sun kai wani mataki ne a rayuwar auren su??sai ta shiga juyi a ɗakin nata dan Dr baya kusa yana ƙasa suna zantawa da Prof ita kaɗai ce a ɗakin.
Yin wannan tunanin ya saka ta jin kamar ta janyo su su dawo nan kusa da ita ta rungume Bilkisu and thank her for introducing her Zaid to the real world..
Ko kafin ta sani har ya datse kiran ya tashi ya nufi ɗakin ta babu tantama ya turo ƙofar bai sauke idanun sa akan komai ba sai a kan kyakyawar surar jikin ta da ke ɗaukar hankali dan bata da girman jiki haka bata da ƙanƙanci sosai dan ta ƙara weight akan tiny structure ɗin ta na da.
Kasancewar rigar mai santsi ne sai ya É—an yaye sama kaÉ—an exposing her navel but iya nan kaÉ—ai ya fito waje sai gyalen da ke yashe gefen ta a saman gadon idanun ta luf sai sharar bacci take yi tana fidda numfashi a yadda ya kamata.
Zuba mata idanu yayi yana kallon fuskar ta da ke nan so smooth babu taɓo sai dai wanda ba za'a rasa ba eyelashes ɗin nan zara zara kamar lema suman kan ta dama a ɗaure yake da robber band ta naɗe shi ta yadda ba zai takura ta ba dama ba wani cikan cunkus bane da suman it is scanty and silk soft and tender to touch dan yana da tsayi daidai misali bai fi ƙarfin jikin ta ba dan a ƙiyastin masana an gano yawa yawan masu ƙananan jiki ko sirara sun fi albarkatun suma toh a wurin Bilkisu ma haka ne dan suman mashaAllah cika ne kawai bai da shi amma tsayi na nunawa kuwa akwai Alhamdulilah..
Chapter 69 · 0% Book details