← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 157

Sashe 142

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Karo ta yi da kayan su da suka gama haɗawa akan zasu koma sai tayi ƙasa da murya gwanin tausayi ta ce
"Tafiya zaku yi"?riƙo t Hajiya Madina tayi tana mai jan ta har ta zaunar da ita saman gado kafin ta ce
"Tafiya zamu yi Bilkisu dan haka ki natsu mi kula da kan ki da mijin ki kin dai san yanayin da kike ciki damuwa duk ba naki bane concentrate and take care of yourself and your baby okey"?gyaÉ—a mata kai tayi tana faÉ—in
  "Yaushe zaku dawo"?abin sai ya basu dariya su biyu har suka dara kafin Hajiya Zeenat ta ce
  "Dama tare muka zo da ku?ku da kuka yo tafiyar ku ku kaɗai baku sanar da mu ba"..sai abin itama ya bata dariya amma bata cikin yanayin dariyan dan haka sai ta murmusa kawai kan ta ƙasa ta ce
  "Umma da yaushe zaku tafin"?amsa Hajiya Madina ta bata da
  "11am saura ma 30minutes mu tafi airport"cikin sauri ta ɗago ta kalli Ammin kamar zata yi kuka ta ce
"Ammi amma fah bai farka ba ku bari har ya farka"sai suka kalli juna kafin daga bisani Hajiya Madina ta ce. 
  "No tafiya zamu yi inshaAllah Allah na tare da ku zai farka very soon ko muna nan ko bamu nan zai farka da izinin Allah so don't worry okey"?shiru tayi ita dai tana jin har ta fara kewar su amma bata da bakin kuma tuhumar su akan dole sai sun tsaya...

  "Kin ci breakfast ne"?girgiza kai tayi sai Hajiya Madina ta buɗe ido
  "Anya Bilkisu kina kula da kan ki kuwa baki ci abinci akan wani dalili kin ga time kuwa"?sai tayi shiru haka aka haɗa mata tea ta karɓa aka miƙo mata toasted bread da aka ajiye mata na breakfast shima ta karɓa ba wai dan tana son cin su ba ta ɗan ci kaɗan sannan ta ajiye su gefe ai kuwa Hajiya Madina ta taso ta gaba
  "Ba dai iya abin da kike ci ki ce kin ƙoshi ba kenan Bilkisu"?sai ta kuma duƙar da kai ƙasa ai kuwa Hajiya Madina ta rinƙa yi mata faɗa ita kuma Hajiya Zeenat na kallon Bilkisun dan dai bata da ikon magana ne ta so ta yi maganar rashin cin abincin Bilkisun but Hajiya Madina na mata faɗa already dole ita tayi shiru
"Ammi wallahi bana marmarin shan tea ɗin ne"baki a buɗe su duka sai Hajiya Madina ta ce. 
  "Toh me kike marmarin ci yanzu"?tunowa tayi da mijin ta sai ta ji hawaye na son zubo mata dan shi kaɗai ya san me ya dace da ita shi kaɗai ya san irin abincin da take son ci wanda bai wuce quacker oat ba sai dai tana ganin in ta faɗi ra'ayin ta maybe ba zasu biye mata ba maybe su ce she is not serious
"Ammi don't worry anjima zan ci abinci masu irin wanda nake ci ne babu su a nan sai a chan masaukin mu"gyaɗa kai suka yi kafin suka miƙe suka hau shirin tafiya..
  Tsakani da Allah kamar tayi kuka haka ta rinƙa ji sai dai bata bari ya fito ba ta kwaɓi kan ta..
Tana ji tana gani suka shige cab da zai kai su airport,har sun shige Hajiya Madina ta leƙo ta yafito ta da sauri ta matso kusa da motar ta duƙar da kan ta wani magana ta mata a kunne wanda ya saka Bilkisun yin ƙasa da kai tana jujjuya kai gefe duk kunya ya gama lulluɓe ta..
  Ɗaga masu hannu tayi tana kallon su har motar ya tashi suka wuce ita kuma ta sauke ajiyae zuciya ta koma ciki,..
  Bata bi ko ina ba sai ɗakin Zaid ɗin wanda ke kan kwasar baccin sa hankalin kwance sai ta ɗan mai kallon sama sama kafin ta fita ta koma waje ta nufi hanyar office ɗin Dr da ya mai aikin..
  Izini aka mata ta ƙarasa ciki ta zauna jiran sa dan ya tafi ganin wani patient kusan mintuna goma sai gashi ya shigo fuskar sa ɗauke da fara'a ya gaida ta ta ansa haɗe da ƙara yi mai bayanin ko ita wacece sannan ta mai tambayar da zata wanda tambayar akan lafiyar Zaid ne dan ta matsu ta ga ya farka haka likitan yayi assuring nata akan any moment yana iya farkawa cikin ƙoshin lafiyar sa sai dai a hankali zai warke wanda zai ɗau sa at most 2 weeks or 3 ta kuma tambayar sa ko in ya farkan zasu iya komawa gida dan su rinƙa zuwa checkup kawai ba sai sun cigaba da zaman asibitin ba ya ce da ita sure muddin babu wasu minor damuwa suna iya komawa gida da haka ta mai godiya ta miƙe ta fita ta koma ɗakin Zaid ɗin ta tasa sa gaba da kallo kamar ta ce da shi tashi ya tashi...

  Tana zaunen ta ji abin bai mata ba sai ta tashi tsam ta koma saman gadon kusa da shi ta kwanta haɗe da ɗora kan ta saman ƙirjin sa tana mai jin kewar sa sosai hannun su sagale tana jin bugun zuciyar sa wanda yake bugawa a hankali kamar yadda ya kamata sai ta natsu tana sauraron fitar numfashin sa...  
  Bata runtsa ba tana nan kwance a jikin sa har tsawon lokaci sai kuwa kamar a mafarki ta ji yana motsawa bakin sa na motsawa kamar dai magana zai yi sai ta yi saurin tashi tana kallon sa...
  A hankali ya buɗe idanun sa ya sauke su saman fuskar ta da ke saitin nasa fuskar sai ya lumshe idanun sa ya kuma buɗewa a hankali duk tana kallon sa,jin kan sa yake ya mai nauyi da yawa kamar ba kan sa ba sai ya rinƙa jin ɗakin na juya mai ya ɗaga hannun sa ya ɗora bisa kan sa yana mai ƙanƙamewa,ganin haka tayi saurin dirowa ta zo ta gefen sa ta ɗora hannun ta saman nasa hannun tana mai taya sa riƙe kan..
  Tsawon lokaci sai ya natsu sakamakon nin ciwon kan ya lafa mai sai ya koma ya kuma kwanciya da kyau bisa ga yadda ɗazu ya kwanta...
 
Hawaye ne tab cike a idanun ta amma ta matse ta ƙi barin su su zubo ta danne su ta buɗe baki tana tambayar sa murya a karye
"Hero,ina ke maka ciwo faÉ—a min"!!bin a da ido yayi yana mata wani irin kallo wanda ya hargitsa ta ya rikirkita ta ta kasa samin natsuwa sai ta cigaba da bin sa da ido tana son jin amsar da zai bata amma bai bata amsar ba..
  Shiru shiru zai yi magana ba zai yi ba har dai ta gaji ta kai gwiwowin ta ƙasa ta fashe mai da kukan ban tausayi tana faɗin
  "Hero please talk to me silence ɗin ka na kashe ni slowly please say something ko baƙar magana zaka gaya min go ahead and say it am all yours ka min duk abin da zaka min amma kar ka min min shiru ka rinƙa bi na da ido"..da kuka ta ida maganar tana kallon cikin ƙwayar idanun sa tsantsar so da tausayin sa duk sun saka ta gaba sun hana ta sukuni...

  Inside him chan cikin zuciyar sa yana son yi mata magana amma ya rasa dalilin da ya hana sa furta mata komai har ya zuba ido yana ganin hawaye na wanke mata fuska..
  Juyar da kan sa gefe yayi dan baya son ganin hawayen nata suna taɓa sa a zuciyar sa sai dai bai san ta ina zai fara ba dan maganar ma nauyin fitowa yake mai..
  Ɗagowar da zata yi sai ta ga ya juyar da idanun sa gefe ai sai ta kuma fashewa da wani sabon kukan tana yi tana jijjiga gadon nasa tana maganganu marasa bearing tsabar ta ruɗe ta gama tsinkewa da lamarin tunanin ta fushi yake da ita akan abin da ta mai.
  "Hero please talk to me shirun ka azaba ce a gare ni wallahi,ni ko duka na zaka yi na amince ka tashi ka dake ni ba zan tambaye ka dalili ba komai ka yi daidai ne"..
  Komawa tayi kusa da shi ta ɗaya ɓangaren da ya juyar da fuskar sa,zuba ma juna ido suka yi suna kallon juna shi kallon tausayin ta yake yi ita kuma kallon son sa da tausayinsa take mai hawaye kuwa kamar an ɓalle kan famfo sai zubowa yake yi...
Ɗaga hannun sa yayi yana ɓari ya ɗora bisa hannun ta yana mai girgiza mata kai alamun tayi shiru sai ta tsira mai ido tana kallon sa ta rasa abin faɗa..
  Girgiza mata kai ya shiga yi yana mai zubda ƙwalla daga idanun sa,saurin kai hannun ta tayi gefen fuskar sa dake fidda ƙwallar ta goge mai tana girgiza mai kai jiki na rawa ta hayo gadon ta ɗaga kan sa ta ɗora bisa ƙirjin ta ta ƙanƙame sa ta saki wani marayan kukan tausayin kan ta da na mijin ta..
Chapter 142 · 0% Book details