← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 157

Sashe 10

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bilkisu am so sorry please forgive me ban san abin ya dame ki da yawa har haka ba ni duk a tunani na maybe kun sami masalaha ne a tsakanin ku but believe me apple wallahi wallahi ban san har yanzu akwai matsala a tsakanin ku ba but since it turns out to be this way ki zo mu je wun Abba a san na yi dan shi kan shi ba zai yarda ki tafi outreach ɗin da hankalin ki bai kwanta da shi,lets go"! ya miƙe tsaya yana ƙoƙarin jan hannun ta su tafi dan abin ya ƙona mai rai.

Dakatar da shi tayi ta hanyar dawo da shi ya zauna ta fuskance shi ta ce
"Bilal duk duniya ban da wanda nake da burin farantawa kamar Abba,zuwa sanar da shi wannan maganar kamar janyo mai ɓacin rai ne wanda hakan na iya janyo masu saɓani tsakanin su da daddy Maher wanda duka iyayen namu ba za su so ba dan haka ka bar maganar kawai i accept defeat zan tafi tare da shi muyi outreach ɗin mu dawo kuma inshaAllah zan rufe idanuna kuma in rufe kunnuwa ta ga duk wasu abubuwan da zai min a garin har mu dawo ban san dalilin shi na ƙi na ba but ko ma dai menene ba zan taɓa ɓatawa mahaifi na rai ba"ta ida tana share hawayen da ke tsilalowa daga idanun ta wanda ya kuma karyar da zuciyar ɗan uwan nata.

"But apple are you comfortable with the decision you just made"?? Kallon shi ta yi tana jinjuna kai
"Alright,just always remember that am with you ko ina kusa ko bana kusa da ke huh"? jinjina kai tayi tana jin sanyi a ran ta ɗan uwa ɗan uwa ne dan tun da maganar ta taso bata taɓa jin sauƙi da sanyi haɗe da kwarin gwiwa ba sai yau da ta fitar da abin da ke ɗawainiya da ita a ran ta.

"Thank you apple"comforting smile ya mata ya raka ta har ƙofar ɗakin ta suka yi sweet dreams har sai da ta rufe ƙofar ya koma ɗakin shi ya kwanta koh Bahajjatun bai kira ba da kyar yayi bacci yana tsoron tafiyar twin sis ɗin ta sa.

A nata ɓangaren ma haka ne dan ta sami courage ba laifi a haka ta harhaɗa abubuwan da zata buƙata a trip ɗin ta gama ta kwanta bacci with less worries...

*************
Tun 9am suka gama packaging kayayyakin tafiyar ta su wanda Hajiya Zeenat ta haɗa mata kayan cime cime kala daban daban dangin su dambun nama alƙubus cupcakes plantain chips dried smoked fish da dai sauran kayan fast food da ba zai wahal da ita wun dafawa ba.

Bayan breakfast suka ranƙaya gabaki ɗaya har da yaya Lukman suka raka ta dan zuwa airport inda a nan suka haɗe da su Zaid suka ƙarasa har airport ɗin dan by air zasu yi tafiyar saboda sauƙaƙa gajiyar hanya.

Sosai Hajiya Zeenat ta nuna jin kewar ta ga ɗiyar tata haka Hajiya Madina ma duk ta damu saboda pneumonia ɗin ta shi yasa ta jadadda ma Zaid akan ya tabbatar ya kula da baby doctor though bata sanar da shi cewar tana da pneumonia ba but ta ja mai kunnen ya rinƙa kula da ita sosai ya amsa mata da cewar inshaAllah..

Bilal kamar kar ya rabu da ƴaruwar sa haka ya rinƙa ji.wata ƴar drama aka yi a airport ɗin dan wani koke koke iyaye matan ke yi yayin da iyaye mazan ke rarrashin su abin sai ya zama abin dariya ga ƴaƴayen nasu Lukman da ke kallon su ya kasa haƙura ya ce

"Alright drama over a tafi gida haka nan"hararar wasa Hajiya Zeenat ta aika mai da shi suka kuma yin dariya da haka suka shige jirgin ya ɗaga zuwa ƙasar Adamawan Yola su kuma iyayen suka koma gida.

Tun da suka shiga jirgin nan babu wanda ya kalli juna a cikin su kowa harkar gabar sa yake yi har jirgin yayi landing safely suka shiga taxi zuwa inda zasu tafi uhum bai shiga tsakanin su ba shi da ya san wuri shi ya rinƙa kwatance har suka yi tafiyar kusa 2¼ hours kafin su kai ciki cikin yankin _koma_ inda aka masu masauki a gidan mai gari tuni labari ya zaga gari bokan turai ya zo tare da wata wacce ake tsammanin itama bokar turai ce ai kuwa aka fara tururuwar zuwa ganin su dama shi ɗan gari ne ita ce sabuwar zuwa dan haka suka rinƙa zullumin ko likitar ce ita ko dai ƴar rakiya ce ita dan haka suka rinƙa tambayar samarin garin wanda suma jira suke washegari yayi su ji cikalen labari daga bokan turai sun so yin takakkiya su tafi har gidan mai garin dan jin rahoto amma mai gari ya hana ya ce a bar su su huta har gobe dan haka suka haƙura.

Matan mai gari suka karɓe su hannu bibiyu tun ma ita baby doctor wacce ta kasance mace ta ji daɗin tarbar da suka mata har da dai basu da wani ƙarfi amma sun yi ƙoƙarin su abinci kala kala daidai ƙarfin su shi da ya zama ɗan gida ya ma manta da wata wai Bilkisu dan samarin gidan mai gari sun ja sa da hira kuma yanayin sauƙin kan sa ya sa suke son sa har suke mai kirarin bature ya ƙi halin turawa dan su sun san ƴan birni na da ƙyanƙyami da tsantsene akan ɗan kauye amma ta fannin bokan turain nasu ba haka bane.hira sosai suka sha har aka kawo mai abinci suka ci suna hira har lokacin sallah yayi suka tafi suka yi daga nan ma ɗan zaga gari suka ui har sai bayan sallar isha'i suka koma gida inda a nan mai garin ya ce a bar shi ya huta haka nan dan haka suka bar shi akan gobe zasu dawo.

A gefen ta kuma haka dai suka so sakewa da ita amma ganin kamar bata saba da hayaniya ba yasa suka rabu da ita sun fi dangana hakan da gajiya akan gobe zasu yi hira itama hakan ya fi mata dan so take ta huta gyara mata wurin kwanciya aka yi a ɗaya ɗakin matar mai gari wacce ita ce ta fi su wayewa dan ita ce ƴar gaban goshin mai gari kasancewar ta amarya kuma ɗiyar mai kuɗin garin so komai nata tsaf tsaf yake watannin ta 8 kawai da aure bata kuma da ciki bare ɗa ko ƴa.lafiyayyen gadon ta da ya sha gyara da zanin gado mai kyau ga blanket mai kyau ga ƙamshi na tashi a ɗakin,kwantawa ta yi tana tunanin gida dan tun da ta zo babu network a garin shi yasa bata sami damar yin waya da ƴanuwan ta hakan ya dame ta sosai gashi shi ɗin da ya kawo ta garin bai ma damu ya san halin da take ciki ba which hurt her a lot but bata cire rai ba akan gobe zata kuma ƙoƙarin ganawa da ƴanuwan ta...

*************
Basu tashe ta ba sai wuraren ƙarfe 6 na safe godiyar ta ma ba sallah take yi ba dan haka tashin farko ta ankara da cewa gidan nan akwai ƙarancin ilimin addini dan haka shima yana cikin aikin da zata yi a garin ba ma a gidan ba kawai,

Komawa tayi ta kwanta bayan ta sanar da su cewa fashin sallah take yi ai kuwa tun lokacin da ta koma basu tashe ta ba sai da ta tashi dan ƙashin kan ta which is 1:45pm ta ji mamaki ba kaɗan ba su kuma haka suke rayuwar su.

Ita amaryar mai garin wato zulfa'u ita ce ta kai mata ruwan wanka a toilet ɗin ta na ɗakin wanda ya sha gyara ba laifi yana ƙamshi dan dama zulfa'u ba laifi wun gyara da ajiye ƙamshi a sashen ta,wankan ta shiga ta yi ta fito ɗaure da towel a ƙirji tana goge fuskar ta cikin sakin fuska ta karasa wun zulfa'u ta ce mata
"Ina yini"amsa mata tayi ta na ce mata

"Likiciya ya baƙunta"?murmusawa tayi dan jin sunan da ta kira ta da shi wai _likiciya_

"Alhamdulilah kuma sai kika bar ni ina ta barci madaÉ—in ki tayar da ni in taya ki aiki"hangame baki tayi kafin ta saka dariya tana cewa

"Likiciya rufa min asiri ina ni ina saka Æ´an birni aiki likiciya?a'a wallahi ni jira ma nake ki ci abinci ki koma barcin dan gajiyar hanyar kamar bata sake ki ba likiciya"É—an darawa ta yi ta ce

"Ki kira ni da Bilkisu sunana kenan ba likiciya ba "shiru tayi kafin ta ce

"Toh ai ba zan iya kiran sunan ba ne tun jiya na san sunan amma ya min nauyin kira shi yasa nake kiran ki da likiciya"da mamaki ta dakata da shafa man da take yi ta ce

"Me yasa ba zaki iya kiran sunana ba"?ta ce
"Sunan mahaifiya ta gare ki likiciya"É—an darawa ta yi ita fah wannan sabuwar suna nata na bata dariya

"Kin san me"?ta ce a'a sai kin faÉ—a

"Ki kira ni da wani sunan ba likiciya ba"É—an shiru ta yi tayi sukui alamun tunani kafin tace

"Ni kuwa jiya bokan turai ya faɗa mana ɗayar sunan ki amma da yake sunan dai kamar ta ƴan nasara ne ban riƙe ba ni ko me ma ya ce sunan naki"??ta cigaba da nazari

Tsaf ta san da baby doctor ya yi introducing ɗin ta shi yasa suka kasa riƙe sunan wannan wace irin wulaƙancin ne kuma shi bai neme ta ba hmm a haka ta shirya cikin atamfa wanda ya mata ɗas a jiki har ya sa zulfa'u kasa ɓoye maganar ta tace

"Kaii amma kin yi kyau dama kuma kuna saka atamfa har haka likiciya"? Ohh matar nan ba zata kashe ta da kayan dariya ba a iya zaman su daga jiya zuwa yau ta lura matar akwai son jan mutum a jiki kuma duk tafi wayewa a cikin matan maybe dan itace amarya shi yasa

"Ai muma kamar kowa muke duk abin da kuke yi muna yin shi muma"sai ta saka dariya ta ce
Chapter 10 · 0% Book details