← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 157

Sashe 135

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chan cikin dare ana washegari zasu wuce ta yi satar hanya ta fita ta yi tafiya mai É—an tsayi sannan ta isa gidan su Mudan,luckily enough sai ta ga mahaifiyar sa na fitowa daga É—akin sa da bokitin ruwa a hannun ta sai ta ji kamar ana motsi dan haka ta haska fitilar hannun ta sai ta ga Asma'u
"Wa nake gani haka kamar ma'u"cikin fitsara da rashin kunya ta ce
"Ni ce mana baki gani ne da dare"?cikin tsinkewa da lamarin Asma'un ta ce
"Ke kuma me ya jefo ki gidan mu cikin daren nan ko dai yawon ta zubar ɗin kika zo yi a nan toh ai sai ki ƙara gaba dan kin jefa min rayuwar ɗa cikin matsala da damuwa"ai kuwa buɗar bakin Asma'u sai cewa tayi
"Ke kama kan ki wallahi ba sanyi nayi ba har yanzu ina nan da rashin mutunci na kamar da,sannan da kike faɗin yawon ta zubar har ke kina da bakin gaya min ina yawon ta zubar?tsaf kin san ni kin san gidan mu kuma kin sa bamu da shegu a gidan mu da tarbiya ta na taso amm wannan macuci azzalumi maci amanar wanda ya yarda da shi ya san yadda yayi ya tozarta ni ya ɓata min sunan a ƙauyen nan ya ɓata min sunan a gidan mu ya ɓata min tarbiya ya gama lalata ni ya maida marar kunya sannan zaki zo kina faɗin ni ce na jefa mai rayuwa cikin matsala har akwai babbar wacce ta shiga matsala sama da ni ne?ni da aka zalinta aka yiwa cikin shege?toh wallahi bara kiji in gaya maki baba lantana kin san Allah ɗaya,,birni zan tafi ina tafiya Allah ya sa na haife wannan asararen cikin turo maku shi zan yi in yi aure nan kuma bana fata Allah ya ba ɗan ki lafiya ubangiji Allah ya dawwamar da shi cikin wannan baƙar hali da yake ciki kuma Allah ya kawo ajalin sa bayan ya gama azabtar da shi da wannan ciwo da yake yi"...baki hangame idanun waje mahaifiyar Mudan ta ke bin Asma'u da kallo dan bata san rashin kunyar ta zai kawo kan ta ba.
Kaf abin da Asma'u ke zazzagawa mahaifiyar Mudan duk a kunnen sa yana ji kuma yana nadamar rashin abin kirkin da ya aikata a rayuwar sa gani yake yadda Asma'u ta juya mai baya ta zaɓi ɗan birni abin da ya mata a ganin sa shine daidai sai dai kuma abin da shi aka mai sai ya ga kamar haƙƙin ta ne ke bibiyar sa hakan ne ma ya sa yake roƙon Allah ya bashi lafiya dan ya je ya bata haƙuri ya kuma ce da ita ya amince zai aure ta tunda shi ya lalata ta..
"Ma'u ki dubi girma na ki dubi shekaru na ki gasa min maganganun rashin É—a'a haka"?kallon hadarin kaji ta mata ta ce
"Ban sani ba"tana gama faɗin haka ta ja doguwar tsaki ta yi kamar zata bangaje ta ta wuce cikin ɗakin da Mudan ke ciki yaye labulen tayi ta riƙe ƙugu tana karkaɗa jiki tana aika mai da kallon tsana.
Duk ya zabge ya rame ya zama wani iri kwance kamar marar rai sai dai bakin sa ya fara buɗewa yana iya buɗewa yayi magana ƙasa ƙasa.
Kallon sa tayi ta ja tsaki kafin ta fara zazzaga mai maganganun da suke kamar garwashi ne a gare shi duk abin da take gaya mai ya san laifin sa ne shi ya janyo hakan kuma babu ƙarya cikin bayanan ta..
A ƙarshe ta ce da shi
"Baka fah ga komai ba Mudan sai rayuwar ka ta fi haka salwanta sai rayuwar ka ta ɗaiɗaicr sai ka wulaƙanta fiye da yadda ka wulaƙantar da ni sannan ka mutu mutuwar wulaƙanci mugu azzalumi maci amana Allah ya isa tsakani na da kai Mudan"kamar zata yi kuka haka ta ƙarasa maganar sannan ta bar ɗakin mahaifiyar sa na kallon ta tana jin wani iri sai yanzu take jin rashin daɗin da Asma'u ta daɗe tana ji sai ta rasa me ya hana ta ganin hakan tun fari....

Tana kuka tana haɗa ƙafar ta haka ta nufi hanyar titi ta tari a daidaita ta nufi gidan mai gari dan yi mai bayanin abin da ya faru da ita da kuma asalin abin da ya faru wanda bata sanar da shi ba a baya da take zaryar tafiya gidan..
Goma saura na dare ta iso gidan mai gari abin ya basu mamaki ganin ta cikin wannan dare kamar tayi ɓatar hanya amma abin da ta tafi masu da shi ne ya jijjiga su suka gane cewa lallai bata da laifi a matsalar da ya sami likitocin birnin da suka taho masu rashin wayo ne ya saka ta aikata abin da tayi dan haka mai gari ya mata fatar alkhairi akan Allah ya sa iyakar matsalar ta kenan kuma Allah ya inganta mata rayuwar ta,bari masu magana tayi akan duk ranar da ɗan birni zai zo a sanar da shi gaskiyar lamarin sannan a nemar mata afuwar sa a bashi haƙuri akan gazawar ta wurin kuɓutar da shi daga faɗawa tarkon Mudan.
Abin gwanin tausayi haka ta bar gidan tana kuka ta kama hanyar gidan su ba wata tazara bace tsakanin gidan nasu da na mai gari ba shi yasa ko da ta fito bata sami adaidaita ba ta taka da ƙafa ta koma gida...

A saɗaɗe ta shige gidan godiyan ta ɗaya babban yayan ta bai dawo daga cikin gari da ya tafi ba tun safe dan haka ƙofar gidan a buɗe yake an bar shi saboda da shi,a ɓoye ta shige ta kwanta bisa katifar ta tana jin wahalar ta ya ɗauke daga washegari in suka bar ƙauyen bata kuma waiwayo ƙauywn sai har ta zama wani abin a rayuwa ta yadda in ta dawo mahaifiyar ta zata san cewa ta gyaru ta natsu....

A ranar da zasu tafi ta shirya cikin shigar mutunci ta saka kayan ta wanda ta fi so fiye da sauran kayan ta ta É—an yi ado ta saka hijabin ta sabuwa wanda yayan ta ne ya É—inka mata akan in zasu tafi ta saka shi...
Ɗakin mahaifiyar su ta tafi ta tsugunna har ƙasa ta gaida ta,kamar ba zata ansa ba sai ta amsa da ƙyar,kuka ta saka mata tana roƙon gafarar ta akan ta yafe mata ƙilla tafiyar kenan in bata dawo ba ta yafe mata sai tausayin ta ya kama mahaifiyar nasu har dai ta ji ya kamata ta tausaya mata dan duk abin da ya faru da bawa muƙaddari ne ba shirin bawan ba..
Jan ta a jiki tayi ta shiga rarrashin ta itama tana kukan da ƙyar dai suka yi sallama ta raka su har wurin shiga mota dan a ƙofar gidan su motar da suka yi shata ya zo suka loda kayayyakin su ciki suka yi sallama da mahaifiyar su suka shige ita kuma da sauran yayyen Asma'u suka koma ciki..

Tafiyar awowi uku da rabi ne ya kawo su cikin birnin Adamawa inda suka ɗau mota ya kai su har anguwar da zasu tafi gidan ba wani babban chan chan bane tsaka tsakiya ne amma yana da kyau kallon gidan Asma'u ta rinƙa yi tana jin daɗi itama zata zauna a birni ko goge goge ne ta amince zata na yi a gidan muddin zasu bar ta ta zauna a gidan..
Ƙarasawa ciki suka yi da yake shi ɗin ɗan gida ne an san shi suka yi gaisuwar sannaya ya masu bayanin ko wacece Asma'u a gare sa ta gaida su gaisuwar mutunci suka shiga ɗakin sa na gadi ya nuna mata inda zata zauna ta shige da kayan ta ta ajiye ɗakin mai ɗan girma ne ba laifi akwai tsari daidai gwargwado,akwai wani katifa kamar sabo ne sai dai ba fil ba amma bai ji jiki ba..
Shigowa yayi ya ce da ita ta fito su tafi cikin gidan su gaisa da ƴan gidan,tashi tayi suka bar gefen nasu suka tafi ciki aka masu iso suka shiga cikin falon mai kyau da fasali suka zazzauna a ƙasan kafet ɗin inda babu jimawa Hajiyar gidan ta sauko fuska ba yabo ba fallasa suka gaisa ya mata bayanin wacece Asma'un da kuma matsalar da yake tattare da ita amma ya ɓoye mata rashin jin da Asma'un tayi a rayuwar ta a ƙauyen su, kuma gaisawa suka yi da Asma'un ta karɓeta a matsayin ƴar aikin da zata ɗauka a cikim gidan dan duka ƴaƴan ta mata sun yi aure sai dai jikoki da kan zo mata hutun ƙarshen mako su tafi ranar lahadi toh shine ta ɗauke ta a matsayin wacce zata na kula da yaran in sun zo sannan on normal basis zata na yi mata ƴan share share da goge goge amma banda girki dan ita ke girkin ta da kan ta...
Godiya sosai suka mata daga Asma'un har yayan nata da karramawar da ta masu..

Tun daga ranar Asma'u ta ke aikin ta a gidan tun ƙarfe 7 na safe zata bar gefen su ta tafi sashen Hajiyan ta mata aiki da yake mijin Hajiyan ba zama ya cika yi ba yana yawan tafiye tafiye dan haka ta waya Hajiyar ta mai nayanin Asma'un ya nuna in har ita hankalin ta ya kwanta da yarinyar toh ta bar ta ta zauna...
Chapter 135 · 0% Book details