← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 157

Sashe 33

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Is okey apple ya isa haka nan i understand you are now safe ki yi shiru kar ki ce komai yanzu zan kirawo likitan ya zo ya kuma duba ki dan bana son ki kuma yin bacci bana so kin ji"?buÉ—e ido tayi ta lumshe alamun ta ji har da Æ´ar murmushin ta dan maganar tasa ta bata dariya haka yake da barkwanci ko da kuwa gathering na son juyewa ya zama boring shi zai maida wun ya zama lively dan haka sai ta cigaba da bin shi da ido har ya fita sai ta kuma runtse idanun ta daga nan ta fara tunano abin da ya faru da su kafin yau É—in yayin da ya fita dan kiran doctor dan wanda ke wurin ya daÉ—e da barin wurin dan ya ga tsananin kewan junan su and he thought that they needed privacy so he left there a course of tafiya kirawo doctor a hanyar su ta dawowa step uku ya rage su shiga suit É—in kawai suka ji wani irin razanannen ihu wanda ba kowa bane yayi wannan ihu fave Bilkisu.
  Tun daga kan iyayen har zuwa ga ma'aikatan babu wanda bai razana da ihun da ta fasa ba except waɗanda suka yi performing procedure ɗin waɗanda a wurin su alama ce ta nasara dan memory ɗin ta is restored back again tsoron amnesia da ake yi ya kau saboda haka likitan na ganin tense grimace a fuskokin su ya ɗan yi murmushi kaifin ya ce da su
  "Worry not,it went well and everything is now completely successful,congratulations she fought quit good it's a miracle"!!kaiwa nan yayi tafiyar sa zuwa ciki su kuma suka rinƙa juya maganar sa da mamaki meye kuma na congratulations alhalin su sun ji ihun ɗiyar su,bature dai bauɗaɗɗen mutum ne shi bai masu doguwar gamsashiyar bayani ba ya tafi ya bar su da incomplete speech wa zai warware masu?babu dan haka suka biyo bayan su dan tare suka tafi da Bilal a daidai main door ɗin suka dakata suna hango abin da ke gudana a ciki..

Setting mata table aka yi aka shiga goge mata fuska dan ta haÉ—a zufa sosai daga nan suna iya ganin yadda take magana a uzurce sai dai su da ke wajen basu san me take faÉ—a ba sai dai Æ´an cikin dan haka suka kuma natsuwa dan jin amsar da likitan zai zo masu da shi..

  Chan cikin kuwa masifaffen tambayoyi take masu akan ina ne nan ina yake rasa inda maganar tata ta dosa suka yi dan haka suka juya suka kalli Bilal suka ce da shi
  "Apple did you have any idea about all these questions we can't understand any of her words"saboda da yaren hausa ta yi tambayar bature kuma babu ruwan shi da apple ɗin da suka ji ta kira shi da shi suka yi addressing ɗin sa,sai ya ce

  "Year i do can you please give me just 5 minutes of privacy"?girgiza kai suka yi suka ce
  "Yeah sure".
    Daga nan suka fita suka bar su su biyun,da fari son rikice mai tayi sai da yayi da gaske ya fanne ta a kan gadon yana fincikewa yana kuma danne ta dan kanta da ta gaji ta yi shiru dan har lokacin effect ɗin ECT ɗin bai bar ta ba lokaci lokaci yake fixgar ta dan haka da ya lafa sai ta natsu ta yi shiru shima shirun yayi yana haki kamar wanda yayi dambe iyakan ta kenan amma duk ta jigatar da shi sai da ya ga ta sami kan ta sai ya durƙuso ƙasa yana facing ɗin ta ta zuba mai ido shima ita yake kallo for a while sai ya kirawo sunan ta
  "Bilkisu"!zuba mai ido tayi tana kallon shi daga bisani sai ga hawaye na bin gefen kuncin ta,saka hannu yayi ya share mata ya kuma kiran ta

  "Bilkisu kina ji na"?girgiza mai kai tayi dan by then ta fara dawowa hayyacin ta ta san cewa ta bar wild forest ɗin nan for good since tana tare da ɗan uwan ta.

  "Bilkisu you are now safe and Alhamdulilah kin farka daga baccin nan da kike ta yi that upset us please apple don't sleep again i don't like it"
  Bata ce da shi ƙala ba sai ido amma maganar ta sa ya shige ta dan da alama ba'ar da ya mata ya saba yin ta sai ta lumshe ido ai a 360 ya ce

  "Nooooo...apple kar ku mana haka please open your eyes"duk sai ya rasa natsuwar sa dan haka sai ta buɗe idanun ta mai facial grimace ɗin wasa ta ke mai a nan ya sami relief ya dawo ya zauna kusa da ita

  "Apple let me inform them am coming"ya miƙe da nufin fita sai ya jiyo muryar ta tana ce mai
  "Where is ge"?dakatawa yayi ya kasa juyowa toh ko ya juyo me zai ce da ita?kawai sai ya ce ai yana surgery room?inaa he can't toh me zai ce da ita?sai ya juyo ya ce
  "Apple me kika ce"?
Da ƙyar ta kuma furta mai
   "Where is he"?sai ya ce
  "Apple am coming let me call our parents they are waiting outside"..daga haka ya juya ya fita ba tare da ya bata chance ɗin kuma furta komai ba.
  Share hawayen sa yayi ya tunkari iyayen su da ke tsaye kamar an dasa su sun kasa furta komai dan tsoron jin me zai faru sakamakon ihun da ta tsala,da zuwan sa suka nufo shi suna rige rigen tambayar sa me ya faru,kasa cewa komai yayi sai ya nuna masu hanyar ɗakin a gurguje suka nufi ɗakin da zuwan su suka tsaya cak suna kallon ta kamar basu san ta ba itama ta maida kallon ta gare su kafin ta ɗan murmusa kaɗan hakan yasa suka ƙarasa ciki suna godiya ga Ubangiji da ya nuna masu wannan moment ɗin the cast the evil that intrude into their lives without invitation.

"Baby..baby you are back you are back to life"cewar Hajiya Zeenat tare da rungume ta tana hawaye itama rungume tan ta yi tana jin wani iri duk wanda ya rasa uwa gaskiya yayi babban rashi.
  Ƙin sakin ta tayi ta cigaba da kukan farinciki tana fatan Allah ya sa kar ta kuma komawa baccin kuma daga haka Hajiya Madina ta zo ta gefen ta ta rungume ta tana mata barka da farfaɗowa iyaye mazan dai kallon su suke yi at least an sani sauƙin ɓangare ɗaya saura ɗayan dan haka fita suka yi dan tafiya jiran jin outcome ɗin surgery da ake yi.
  Afzal ma fita yayi dan they are making him emotional already Bilal kuwa yana nan zaune bai bar ɗakin ba yana ta kallon ta kamar an hallice ta ne kamar bai taɓa sanin ta ba.

  Tana da tambaya a ran ta about him where is he?what happened to him?how did they get here?duk a ran ta tambauoyin su ke but sai ta kasa furtawa dan haka ta bar shi ma kanta akan in sun basu space sai ta tambayi ɗan uwan ta.ana haka Hajiya Zeenat ta tambaye ta
  "Baby akawo maki abinci ne"?shiru ta yi kafin ta amsa da
"Eh" da ƙyar ma muryar ke fitowa dan haka miƙewa suka yi su biyun cukun hanzari suka bar ɗakin hakan ya bata damar kiran ɗan uwan nata da ido cikin sauri ya karasa gare ta ya ce
  "Apple what did you need tell me please"ita tausayi ma yake bata she can tell tun da ta buɗe udanun ta shi ne first person da ta gani yake cikin tashin hankali dan haka ta kai hannu ta riƙe shi dan ya zauna saurin zaman yayi sai ta yunƙura kamar zata tashi wani intense pains ta ji a lumbar region ɗin ta wanda haka ya saka ta sake ɗan ƙara

"Auchh auchh"!! Saurin maida ta yayi yana ce mata
  "Sorry apple sorry kwanta baki gama farfaɗowa ba"gyara mata kwanciyar yayi kafin ya tambaye ta
  "Menene?tell me please"!!ya zuba mata idanu sai ta haɗa duk wani strength ɗin ta ta furta
  "Ina Zaid?ya dawo?yana ina"?tambayar kamar dirar dalma haka ya ji ta shi all hus thought ta manta da tambayar seeing their parents dan haka ya ce
  "Apple ki ji da kanki mana baki da lafiya"!!shiru yayi ta san shi sarai something is fishy dan bai saba ɓoye mata abu ba musamman in ita ta yi tambayar sai gashi a yau yana sauke kan sa ƙasa yana gudun haɗa ido da ita  toh me yake nufi?basu bar dajin nan tare ba?ko kuma an....bata bari zuciyar ta ta ƙarasa hasaso mata abin da ke yawo a brain ɗin ta ba ta kallo shi tana mai zazzaro idanu
Chapter 33 · 0% Book details