← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 157

Sashe 78

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Good morning"da É—an murmushi ta ce
  "Morning"sai ya kuma tambayar ta yana mai kawo hannub sa kusa da goshin ta
  "How was your night"?imagine Zaid is a good pretender kamar ba ɗakin ya kwana ba sai ta bashi amsa da
  "Alhamdulilah"ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce
  "Your health"??sai a nan ta haɗa ido da shi dan shima abin da yake so kenan,so yake ya haɗa ido da ita ko zai sami wani amsa cikin idanun nata dan shi ya rasa gane abin da ke damin lafiyar tunamin sa.
  Cikin sanyin murya da ke tattare da tsantsar so da ƙaunar sa ta ce
"Alhamdulilah nagode"sai suka yi shiru suna kallon juna kafin daga bisani ya tambaye ta
  "Waya...da wa kike waya..na daɗe a nan baki sani ba"cire idanun ta tayi daga nasa tana gyara zaman rigar ta sannan ta bashi amsar tambayar sa cikin unexpected response
  "Hmmm i see,,me kuma ya sa kake son sanin ko da wa nake magana"?wani irin kallo ya mata mai nuna tsantsar mamakin sa da irin amsar da ta basa har ma da tambaya a ƙarshe.
   Bai so amsa mata ba but wani sashe na zuciyar sa na ingiza sa akan dole ya amsa mata dan haka ya ce
"Babu,kawai gani nayi hankalin ki ya koma kan wayar gabaÉ—aya"!!Æ´ar murmushi tayi sannan ta rausayar da kai gefe kafin ta ce
  "Da Umma na yi wayar"sai ya gyaɗa kai yana mai kai hannun sa kan teburin da ke mafi kusa da ita,landline ya kira ya masu ordern breakfast har ya ajiye sai kuma ya juya ya kalle ta cikin kulawa ya ce
  "Sorry ban tambaye ki abin da kike so ba na bayar da ordee,what would you like"??kallon sa tayi kafin ta miƙe tana tafiya a hankali zuwa ɗakin ta ta ce da shi
  "Abin da zaka ci shi zan ci ko ka manta a ƙarƙashin ka nake"??ta juyo ta mai kallon da ya saka jikin sa sakewa,kasala ce ta sauko mai a bazata ba zato ba tsammani ya ji kawai ita yake son kallo sai dai kafin yayi wani yunƙuri har tayi shigewar ta ciki.
  "Damn it...Zaid common man up man up..."ya furzar da iska mai ɗauke da ɗumi daga bakin sa dan hucin iskar alama ce ta yamayin da zuciyar sa ke ciki but why all these me ya sa haka me ya kawo haka he thinks he should visit a doctor seriously..

    Da dariya ta ƙarasa shigewar ta ɗakin dan ta san ta ƙunna sa dan dolen sa ma ya ji a jikin sa saboda ta san yanayin maganar da ta mai sai ya ji wani abin all she need is for him to realise and keep her in his head kuma ba zata iya yin hakan ita kaɗai ba dole sai da sanin sa da kuma yardar sa..
   Kwantawa tayi bisa kan gadon ta tana jin wani sassanyar annashuwa na  shigar ta from no where,juyi tayi tana tuno wasu moments da suka yi tare da shi most especially jiya da ya nuna damuwar sa gare ta,tunowa tayi da lokacin da ya ruɗe a jiyan yana ta tambayar ta ko me ke damin ta sai ta tsinci kan ta da yiwa kanta dariya lallai ta shiga sabuwar duniyar da bata san da akwai shi ba a duniyar nan the feelings is extraordinary abin ya mata nauyi da yawa tana buƙatar mai taya ta riƙon abin da take ji a zuciyar ta..
 
  Tana duniyar tunanin ta ne ta ji an turo ƙofar ɗakin kamar ba'a son turowa hakan ya tabbatar mata da Zaid ne dan shi kaɗai ke tare da ita a gidan.
  Tashi tayi daga kwanciyar riginginen da tayi tana mai kallon sa da murmushin son da take mai shi ko shagala yayi yana kallon ta yana jin wani abu na fizgar sa sai dai yayi ƙoƙarin controlling kan sa dan yana ganin kamar yana overreacting da yawa.
  Gyaran murya yayi game da riƙe ƙofar ɗakin yana mai sauke mata idanun sa cikin wani salo hakan kuwa yayi tasiri a kan ta dan kallon yayi affecting nata sosai sai dai itama tayi controlling kanta dan so take ta gama tabbatarwa ko shima yana jin abin da take ji ko ita kaɗai ke jin abin..

"an kawo mana breakfast zaki yi joining É—i na ne a parlor ko in kawo maki nan"?cikin salon jan ra'ayin sa ta ce
  "Hmm Zaid kenan..,ai duk inda kake nan nake duk inda ka zaɓar min nan zan zauna"
  Ya ilahi,me yarinyar nan ke son yi mai ne haka shin?sam yakan kasa ganewa kan sa in har tana kusa da shi shi dai ya san abu ɗaya ne tak wanda ya san ko a baccin sa zai iya shaidar sa sai ya sami mai warware mai..

  Kallon kallo suka shiga musayar yi da juna kafin ya ce da ita
"Toh ki zo mu tafi parlor in yaso sai mu kalli theater show"tashi tayi da fara'ar ta ta ce
"Hakan ma yayi"!!ta rigasa fita falon shi kuma yana biye da ita a baya yana saƙe saƙe..
Chapter 78 · 0% Book details