← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 157

Sashe 98

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Not too long aka kawo mata breakfast ta zauna da nufin farawa sai dai abin mamaki banda tuno fuskar Zaid a lokutan da suke cin abinci tare babu abim da take yi ƙarshe ma da abin yayi yawa sai ta hau hasaso sa tare da ita a yanzu ma har dai fuskar sa ya fara yi mata gizo bata ankara ba ta ji abu na bin fuskar ta ko da ta kai hannun ta sai ta ga wai hawaye ne ke bin fuskar ta sai ta mayar da cokalin ta jingina da gadon ta ta shiga rafka kuka ba ji ba gani tana ta maganganu marasa ma'ana
"Duk kai ka janyo mana,na gama tsara mana yadda rayuwar mu zata kasance yadda zamu rinƙa gudanar da activities ɗin mu amma ka wargaza mana duk laifin ka ne duk kai ka jawo mana wannan abin yanzu ina wannan halin amma babu kai kusa da ni duk pains ɗin ni kaɗai nake ɗaukar sa kai babu ruwan ka baka ma san ina yi ba and i believed you i trusted you i gave you my body,my heart and my soul i thought you will take care of it amma i was very wrong na tafka babbar kuskuren da na daɗe ina gudun tafka sa a rayuwar aure na,my dignity my virginity i gave it all to you thinking that you will respect me after that but sai kayi proving min cewa kai ɗin cikakken namiji ka kira min sunan wata a daren farkonna da kai ka rinƙa faɗin kalamai masu taushi akan ta gaba na fah,gaban ido na ina kwance a jikin ka ko shakka ta baka ji ba baka yi respecting ɗi na ba ka raba ni da mutunci na sannan ka juya min baya me ya sa Zaid?why??why did you choose to punish us in thus hard way?sarai ka sani na ƙi jinin jin sunan yarinyar nan amma ka rinƙa maimaita sunan ta kamar abin bautar ka"!!!..kuka take yi tuƙuru duk idanun ta sun kumburo sun yi ɓulu ɓulu kamar an daɗa mata girmar su ba ƙaramin raɗaɗi take ji a ran ta ba dan ta gama mafarkin washegarin daren farkon ta zai dasa tarihi mai tsafta a zuciyar mijin ta she endured the pains of a virgin lady wacce karon ta na farko da haɗuwa da namiji zata ji raɗaɗi ta kasa riƙe zafin har sai ta fitar da muryar ta fili amma ita ta danne ta bar wa kanta duk dan ta saka sa yin alfahari da ita amma ga abin da ya mata bai ma damu da abin da ya mata ba ya zage ne kawai yana maganganu akan wata Asma'u

Tsabar baƙin ciki a nan ta kwanta har baccin azaba yayi gaba da ita wanda har cikin baccin ma banda blaming Zaid babu abin da take yi a ganin ta duk shi ya ruguza masu rayuwar auren su da ta jima tana tanadi.
Uwa uwa ce duk fushi faɗa da rigimar da zaku yi da ita dole ta damu da son sanin lafiyar ka,.ko a jiya danne zuciya Umma tayi ta fita harkar Bilkisun har zuwa wayewar yau da za'a yi breakfast aka ce za'a kirawo ta amma ta hana ta ce a bar ta yarinyar da bata iya zama da miji ba ai har iyayen ta ba iya zama da su zata yi ba dan haka ko bayan sun watse sun tafi wuraren aikin su ya rage daga ita sai ita a gidan ta rinƙa saƙawa tana warwarewa ƙarshe dai ta yanke hukuncin zuwa ɗakin ta dubo ta in yaso sai ta ce faɗa ta zo yi mata dan kar ma ta ɗauka ko damuwa tayi da ita.
Zuwan ta ɗakin ke da wuya sai ta gan ta kwance a ƙasa fuskar ta duk ga alamar hawaye nan sun bushe gefe ga abincin ta nan bata taɓa ba sai kuma ta dawo jin tausayin ta she knows that she overreacted yesterday and today amma dole ne ta nuna mata rashin gaskiyar ta ba wai dan tana ɗiyar ta shikenan ta rufe ido ta ce zata goyi bayan ta ba as a good mother she have to correct her daughter's misconception akan zaman ta da mijin ta..
Hawaye ne ya cicciko idanun Umma sai ta miƙe ta bar ɗakin dan ita ta san raɗaɗin kishi saboda a fagen kishi sam Bilkisu bata kamo ta ba amma yanayin rayuwa ya sa dole ta sassautawa kan ta sai gashi duk addu'ar da ta rinƙa yi akan kar Allah ya sa Bilkisu ta yo gadon ta sai da ta yi nata kuma har da son taɓa mata ƙwaƙwalwa yake dan ko a baya da ita tayi nata kishin Allah ne kawai ya taimake ta ya sa har yanzu suke tare da Prof ba dan haka ba da ba'a ma haifi Lukman ba dan her past was a hectic one sai dai yanzu ya zamo past kuma tana fatar Allah ya yayewa Bilkisu wannan mummunar kishi da ke ɗibar ta dan mazan yanzu basu da tabbas ba kowa zai ɗauki shashancin ɗiya mace ba bare ma a ce tana ƙarƙashin sa sai yadda ya ga damar yi da ita..

*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀*
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

*_Munafukan zaune masu ci da gumin wasu Allah ya tono ma duniya asirin ku amma ku sani matuƙar muka taso ku gaba sai duniyar ta maku raɗaɗi alƙawari ne wannan.._*

*_Sannan gare ku readers ku sani babu wani littafi da yake mallakin Brilliant Writers Association da zaku gani a ce da ku na kuɗi ne ku yarda da hakan ba,duk wanda ya ce da ku littafin Association ɗin mu na kuɗi ne toh ƙarya yake maku dan mu bamu littafin kuɗi be warned and stay alert coz criminals get smarter by the day.._*

  *30*

Da suka shiga cikin gidan ne Hajiya Madina ta fara jin raɗaɗin sanin inda ƴaƴan su suke sai kawai ta danne ta barwa kanta har dai suka ƙarasa shiga ciki yayin da mai gadin nan bakin sa ya rinƙa mai muimui yana son sanar da su amma sai ya ƙyale bai yi maganar ba.
  Har suka isa bedroom ɗin su gabaɗaya bata jin kamar tana tare da Dr Maher kawai calming nata yake yi tana sauraron ta amma sam ba shigar ta zantukan nasa ke yi ba.

Zama tayi saman gadon ta rafka tagumi tana jiran jin sakamako dan jikin ta ya fara bata wani abin marar daÉ—in ji addu'a kawai take yi cikin ran ta dan bata son ta ji wai tunanin ta zai rikiÉ—e ya zamo gaske.
  "Dr,ban san me ke shirin faruwa da mu ba but ina ji a jiki na kamar ba lafiya ba"ɗan rungumo ta yayi ya ce
"Common darling,ki daina wannan tunanin ki kyautata zaton ki please yaran nan na nan lafiya just calm down"!!É—an ture sa tayi kafin ta ce
"Dr baka san me ke dami na ba baka san irin tsoron da ke shiga ta ba,ni uwa ce dole in tsorata ba zan iya sanin sukuni ko kwanciyar hankali ba har sai na ji na kuma na san halin da suke ciki"..
Ajiyar zuciya ya sauke ya buɗe baki zai yi magana sai ya ji sallamar Afzal dan haka ya bashi izinin shigowa,.bayan ya shigo ne ya durƙusa har ƙasa sannan ya fara magana
"Abba ina ga matsalar nan ta zo ƙarshe"..cikn sauri Hajiya Madina ta ɗago kan ta tana kallon sa a rikice ta ce
"Me kake nufi Afzal"?sai ya ce
  "Na ji daga wun mai gadi shi ya sanar da ni komai ya ce da ni tun ɗazu kusan two hours da suka wuce yaya ya dawo gida kuma a yadda ya lura da shi kamar bai da lafiya dan haka da zuwan sa ma wai ɗakin sa ya tafi and he..."ai tun kafin ma Afzal ya kai aya Hajiya Madina ta miƙe cikin sauri da azama ta bar ɗakin tana mararin ganin ɗan ta da ta fi ɗaukaka son sa fiye da sauran ƴaƴan ta dan irin son da take wa Zaid ko mahaifin sa ba zai nuna mata son Zaid ba sai dai ma ya daɗa ƙarfafa mata gwiwar son Zaid ɗin son nan nasa da take yi ha haɗu har da kwaso ta da yayi a kamanni dan komai nata bai baro ba banbancin shine ita mace ce shi kuma namiji sai ɗan shekaru da ya fara nunawa wanda ya zamo wata ƙaramar banbancin..
Chapter 98 · 0% Book details