← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 157

Sashe 112

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Tun da hannun su ya haɗu da na juna ya rasa me yake mai sparking a kai amma haka y daure ya taya ta suka ciro babyn nan babyn ma har ya fara shan ruwa dan ana fito da shi suka ga sign ɗin hydrocephalus but midwife da ke jiran isowar baby ɗin tayi ƙoƙarin moulding kan babyn at least first week of life na babyn in ana moulding kan zai dawo daidai..
  Suturing tayi tana gamawa ta ce da sauran team ɗin su gyara matar a kai ta ɗakin hutu.
  Wucewa tayi zuwa ɗakin scrub ta cire hand glove ɗin tayi discarding ta wanke hannun ta sannan ta fito,yana tsaye yana kallon ta tana fitowa tayi wucewar ta bata tsaya ko ina ba sai office ɗin ta.
  Kai hannun ta tayi ga lock dan rufe ƙofar amma sai ta fasa ta bar ƙofar a buɗe ta wuce zuwa cikin nata scrubbing room ɗin a nan ta cire face mask ɗin ta cire scrub da ta saka tayi aikin da shi ta cire boot dake ƙafar ta hairnet da ke kan ta ta cire,wanke fuskar ta tayi ta goge da towel sannan ta fito ta zauna bisa kujerar ta.
  Janyo wayar ta tayi ta ƙunna ta ɗan tsimaye shi har yayi booting sannan ta shiga duba abin da zata duba dan ita bata yarda da Zaid ya rinƙa zuwa yin surgery ba mutumin da kan sa bai dawo daidai ba ana tura sa theater room ai wataran sai a tafka kuskure dan yana iya manta wani abin.
  Binciken ta tayi ta ajiye wayar ta ɗan yi leaning backward tana sauke ajiyar zuciya sai a sannan ta tuna bata yi  breakfast ba gashi da zuwan ta ta shiga cs room.
  Kiran secretary nata tayi ta sanar da ita abin da take buƙata sannan ta mayar da wayar ta ajiye ta koma tayi leaning da kujerar,ba jimawa ta ji wayar ya ɗauki ƙara sai ta buɗe idanun ta da ke lumshe ta ɗago,wayar ta ɗauka ta duba sai ta ga an saka _Apple_ ɗaukar wayar tayi ta latsa sannan ta kara a kunnen ta kafin ta ce wani abin har an riga ta
"Beelove am getting married"muryar ta is full of excitement sai Bilkisun ta É—an yi shiru tana mamaki kafin ta ce
"Married Baha?to who"?ko a jikin ta ta ce
"Who did you think Beelove?of course my apple"ta faÉ—a tana dariya kafin Bilkisun tayi wani abu har muryar Bahajjatu ya kuma echoing a kunnen ta
"Na so shihowa in sanar da ke but kunyar shiga na ji kin ga Umma sai ta ce ban da ta ido na taho zance gidan saurayi shi yasa ban shigo ba but thank goodness apple ya sanar da ni kin tafi wurin aiki i tried calling you but it wasn't going through sai yanzu"..
   Duk wannan doguwar zancen da Baha ke mata sam bata tare da ita hankalin ta na kan family ɗin ta a ce har an yanke bikin Bilal bata sani ba babu wanda ya sanar da ita su kwana gida ɗaya su farka tare amma a rasa mai sa ar da ita wannan wace irin silent wicked punishment ne ake bata..
  Toh ko ma dai menene ba zata bar gidan ba in sun gaji da threatening nata sai su haƙura.
Baha ce ta katse mata tunani by saying
  "Beelove na ji kin yi shiru aren't you happy for me?aren't you happy that i will be getting wedded with my love?huh"?da sad voice ta ida maganar sai Bilkisu ta girgiza kai wai her love toh ita ina ruwan ta wa Baha ke wa hausa?ita ce bata da love ɗin ko me?ƙwafa tayi sannan ta ce
"Not at all dear ni ke farinciki fiye da kowa believe me kawai farincikin ne ya saka ni yin shiru but am happy congratulations dear"haka tayi maganar in so suke su haɗe mata kai toh ita ma zata nuna masu abin bai dame ta wai har aunty Zee da ta mata alƙawarin dawowa washegari amma bata gan ta ba duk ita ce bad luck hmm

  Cikin ɗimbin mamakin reaction ɗin da Bilkisu tayi sai ta ce
"Thank you,my love is calling me i have to go"cikin halin ko oho ta ce
"Sure you have to,toh sai anjima"ita ta fara ajiye wayar tana furzar da iska bata son blame games É—in nan anymore she wanna move ahead dan haka ta natsu ta yi wani tunani da take ganin zai saka ta huce haushin ta.
  Abinci aka kawo mata sai ta duba time ta ga 11 har yayi sai tayi saurin cin abincin ta miƙe ta ɗau jakar ta ta yo waje tana fita Dr Aslam na shawo gaban ta shi so yake ya gane kuma ta sanar da shi in tana takura ne cikin rayuwar auren Zaid sai ya tsaya mata a ƙwato mata ƴancin ta su rabu shi ya aure ta dan yanayin da ya gan su ɗazu suna surgery ɗin nan abin ya saka shi tunanin wani abu daban..
Tana buÉ—e motar ta ya rufe ya tsaya a gaban ta yana faÉ—in
"Tell me baby kina da matsala ne da zama gidan Zaid?yana takura maki ne?is he rude or bad to you tell me"?cikin ƙosawa da ganin sa da jin muryar sa dan ita ba care and concern ɗin sa take buƙata ba ta ce mai
  "Please go away from here i am married so you should know what to say and what not to say to me"ta ynƙuro zata buɗe motar ya kuma tare hanya yana faɗin
"Stop pretending to be okey ni na san kina da damuwa is written all over your face wannan mai jijji da kan tsiyar shi ya saka ki cikin damuwa i know so just tell me saboda mu san abin yi Bilkisu i love you i do...i still love you please make him divorce you sai ni in aure ki i love you i can care for you,shower you with my love i will protect you i will give you everything i can be your cowboy i swear just leave that Zaid he is not worthy of you"iya gaskiyar sa yake wannan maganar sai ta ji ina ma reverse will be the case Zaid ya gaya mata haka ya ce zai rabu da Asma'u of a girl ɗin nan ya nuna mata so da ƙaunar sa gare ta da ta fi kowa alfahari..

  Kallon sa tayi daga sama zuwa ƙasa sai ta girgiza kai ta ce mai
"You are shameless Aslam"daga haka ta kai hannu zata buÉ—e motar ya sha gaban ta yana faÉ—in
"Yes na yarda i am shameless because i love you i know"hararar sa tayi ta ja tsaki dan ya gama kai ta limits É—in ta da shi ta fara getting irritated by seeing him.
Matsawa tayi zata shiga ya tare mata hanya ai kuwa kafin ya sani ya ji saukar marin da ya gigita sa a hankali hannu dafe da kumatun sa ya É—ago ya kai idanun sa ga mai marin abin sai ya firgita sa ya rasa me zai ce.
  Zaid ne ke mai kallon tsana dan yayi tunanin sun gama magana tun da ya ce da shi Bilkisu is all his amma bai ji ba dan haka dole ya fito mai a mutum.
  Kokuwar su ta ƙarshe ya gani sai ya ji in ran sa yayi miliyan ya ɓaci duk wata walwalar sa babu shi abu ne ya ji yana soƙin sa a direction na ƙirjin sa kawai ya ji in ba marin Aslam yayi ba ba zai ji sauƙi ba..
  Nuna sa da yatsa yayi rai ɓace dan baya ji baya ganin komai ya ce da shi
  "This is the least of what i can do to you,worst are yet to come if you don't kerp your dirty filthy feet 100inches away from my wifeee"cikin halin mummunar ɓacin rai yayi maganar sannan yana zuwa wurin furta wife ɗin ya ja kalmar dan wani haushin sa ne ya taso mata how on earth zai iya standing Aslam a ce mutum ya rasa abin da ya fi mai daɗi sai maganar da matar wani wanin ma shi,shi fah,matar sa,noo dole ya ɗaga maganar
  "Just wait and watch in kwartanci kake yi da matan wasu toh ni tawa matar ta fi ƙarfin ka ba sakaran namiji bane ni zaka faɗi haka ka ƙara lokacin da na hukunta ka"ran nan ɓace fuska a haɗe yayi maganar.
  Ita dai bata san kan magana da fushin sa ba sannan marin da ya ma Aslam me dalilin yin hakan me yasa yake iƙirarin ita ɗin matar sa ce alhalin bai damu da ita ba,.
BuÉ—e motar ta tayi ta shige ta ja ta bar su nan tsaye tana barin wurin Zaid ya bar nan É—in shima dan dama fita zai yi sai ya ci karo da mummunar gani abin da ya haitsina mai tunani kenan.
  Aslam da ke kalle kalle kamar wawa ya ce
"Na rantse da Allah in har na tabbatar da zargi na akan auren nan toh alƙawari ne sai na san yadda nayi na raba shi kawai ya rinƙa shigo min hanya ba dama in sami walwala sai ya ɓata mai toh zan saka ido na a auren nan sai na gano wani abin"da fushi yayi ciki kamar kububuwa.
Chapter 112 · 0% Book details