← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 157

Sashe 19

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"No Ammi"a nan ta sanar da ita dalili sai ta ce
"Alright na fahimta yanzu dai zan sanar da ke saƙobn in kun haɗu sai ki sanar da shi"
"Okey Ammi"
"Kina ji na,in kun haɗu ki ce da shi na ce amanar nan da na bari mai kar yayi wasa da ni ya riƙe da kyau dan in ya bari na san yayi wasa da amanar toh har abada amanar ta suɓuce mai kenan kuma ba da wasa nake ba".

Cikin É—imuwa da zancen dan she was very serious while saying it sai ta ce
"Ammi why me?me yasa ni zan yi conveying mai wannan saƙon"?
dariyar manya ta yi ta ce
"Bilkisu ki sanar da shi jakan dan le kaÉ—ai gare ni a garin da zan iya aika zuwa wun My boy ba tare da na sami matsala ba dan haka ki sanar da shi shi zai gane me nake nufi"daga haka ta ce
"Alright Ammi zan faÉ—a mai ki gaida mana su Abba"
"Za su ji baby and don't forget to take care of yourself humm"
"Yes Ammi i will"
Suka yi sallama ta kashe wayar tana mamakin wannan saƙo da aka bata,
Fitowa ta yi ta ga zulfa'u ta daÉ—e da yin barci dan haka itama ta kwanta ta yi addu'ar barci ta rufe jiki sai barci..

A fannin su Asma'u kuwa ashe laɓe ta yi ma su Dr Zaid Maher tana sauraron duk wasu kalaman su tana jijjiga kai suna tafiya ta fito tsakar gidan da ɗaurin ƙirji ta saka kuka tana ta ja kamar jiniya mahaifiyar ta dai shiru ta mata tana kallon ta tana jiran ta gama darun ta ta kuma assasa mata nata ƙudirin dan haka ta gama birgiman ta tana surutan ta.

"Kee Asma'u ji ni nan wallahi wallahi kin ji na rantse maki babu makawa babu kaffara sai kin fara halartar karatun nan na rantse maki ba ki isa ki take doka ta ba ni na haife ki ba ke ba..

Daga nan tayi shigewar ta ta bar ta tsaye nan tana ta birgima..

**************
Washegari wanda ya kasance asabar wuraren ƙarfe 9 na safe suka shirya zasu tafi wurin outreach sun yi sallama da jama'an gidan sun fito suka shiga taxi a ciki ta fara sanar da shi saƙon mahaifiyar sa kallon ta yayi sai ya mata shiru kawai itama sai bata kuma cewa komai ba har suka iso..

Da zuwan su babu ɓata lokaci suka fara da masu rashin lafiya suna ba su magungunan har dai ƙarfe 2 ya kai suka rufe session ɗin ranar suka dawo gida.
Abin mamaki sai ga Asma'u da mahaifiyar ta sun zo wai an kawo ta koyon karatu dan haka babu tsangwama bare hantara baby doctor ta yi welcoming É—in ta faram faram.
Mahaifiyar ta ta tafi ta bar ta ita kuma ta zauna nesa da yaran,ba'a takura mata ba ana karatun hankalin ta na wani wajen sai da aka gama sannan baby doctor ta ja ta gefe ta fara mata nasiha..

"Asma'u kina ganin wani za ki cutar in kika ƙi mayar da hankalin ki a karatun nan?babu fah wanda za ki zalunta sama da kanki,sarai kin san da a ce mu ma irin halin ki muke yi toh ba mu isa mu zo nan muna karantar da mutanin garin ku akan abin da zai taimake su ba babu yadda za'a yi mu zo nan mu tsaya har a saurare mu kin ga duk hakan ilimin mu ne ya janyo mana hakan ke ma ba za ki so ganin kan ki haka ba Asma'u"? A yanayin yadda ta yi maganar sai ya sa Asma'u ta ji jikin ta yayi sanyi dama chan tana da hankalin ta kawai dai rashin samin kyakyawar foundation ne ya sa ta bi ta taɓarɓare.

"Ina so mana amma kun ga Mudan baya so dan ya ce Æ´an birnin nan cutar da mutani suke yi kuma karatun boko ai dan a sami abin dogaro ne kuma ya ce shi zai tsare min komai ba sai na yi wani kartun zamani ba na je na koyo nasaranci shi ya sa ban yarda da son karatun ba tun farko"!

tirkashi lallai wannan Mudan É—in azzalumi ne wato shi bai yi itama kar ta yi Allah ya raba mu da mugunta,cewar baby doctor a zuciyar ta

"Amma ke kina son yin karatun"? ÆŠan shiru ta yi kafin ta ce
"Ai ko ina so Mudan baya so kuma in kuka tafi ai shikenan ba cigaba zan yi ba kin ga ai bai da wani amfani"ta yi shiru daga yadda ta yi maganar mutum zai gane cewa tana da zeal É—in yin karatun amma hindrance na Mudan ya sa ta ke withdrawing..

"Hmm Asma'u kenan ai sai dai in baki ba da haɗin kai ba amma muddin kika amince ni na maki alƙawarin saka ki a makaramtar birni chan cikin Yola ki yi karatu mai zurfi har inda ran ki ke so dan kema ki zo nan ki faɗakar da mutani su ƙaru wannan alƙawari ne daga gare ni kin yarda"?? Kamar bazata ce komai ba sai ta ce

"Na yarda amma ina tsoron Mudan kar ya cutar da ku"É—an dariya baby doctor ta yi kafin ta ce
"In dai Mudan ne babu abin da ya isa ya mana sai dai in Allah ya tsara hakan zai faru kar ki ji komai kawai ki bamu haÉ—in kai"!!
Girgiza mata kai tayi kafin ta ce

"toh na yarda zan yi karatun"daÉ—i ne ya kama Bilkisu dan haka ta ce

"Yauwa Æ´ar gidan Mudan toh yadda za'a yi ki rinÆ™ zuwa kafin lokacin sai in koyar da ke in kuma lokacin koyarwar ya kai sai mu yi tare ko ba haka ba"?girgiza kai ta yi tana murmush.

Ita dai bata sanar da ita cewa Dr Zaid na son ta ba dan kar ta yi amfani da wannan ta ƙi yin karatun ko ma ta fara jin wani iri kuma in har suka bari Mudan ɗin ya san cewa Dr Zaid na son ta toh lallai za'a yi ƴar ƙaramar yaƙi su kuwa ba abin da ya kawo su ba kenan..

Dan haka tsara komai suka yi tun a ranar har dai aka fara karatun rumui rumui kafin 6:30pm suka dakata a inda baby doctor ta tafi kiran Dr Zaid dan shi bai ma san cewa an kawo Asma'un ba,da ya fito ya gan ta sai ya ce
"Ya aka yi ba dai kuma aiko ki aka yi ba"? Sai ta É—an murmusa dan ta ga changes a tattare da shi sosai zuwan su nan É—in a da ba su ga maciji da juna har ji suke kamar su kashe juna dan haushi but now just a week + wai har suna iya tsayuwa su yi doguwar maganar fahimtar juna sai ta ce

"A'a ba aike na aka yi ba dama sanyin idaniyar ka ce ta zo muka yi karatu i tried and convince her kuma ta amince"she explained everything to him murna yayi at least koh ba komai ta nan zai raba ta da wannan Mudan ɗin sai ya sakarwa Bilkisu murmushin da ya saka ta ɗauke wuta dan bai saba ba bai kuma taɓa yi mata ba hasali ma ba su jituwa so duk wata murmushin da zai mata na ƙeta ne ba na tsakani da Allah ba amma yau saboda Asma'u har yayi murmushin gaskuya da gaskiya hmm lallai yana son yarinyar koh da ma mix feelings ne gare shi a kan yarinyar ba pure love ba he still feel something special for herdan haka itama murmushin ta mai ta ce

"Ga ta chan sai ka raka ta gida".
Godiya ya mata by saying
"Thanks"daga haka ya wuce ta tana ysaye tana mamakin halayar sa ta burgaggen mutum yanzu sanyi anjima zafi girgiza kai tayi ta wuce abin ta.

Koh da ta zo zata shiga daga cikin sashen zulfa'u sai ta gan su suna tafiya he felt something strange sai dai ta bar wa kanta ta shige ciki,.

Abincin daren ta ta ci ta yi alwala ta yi sallah zama ta yi ta karanta Qur'anin ta a wayar ta daga nan ta tayar da sallar isha'i ta yi azkar kafin ta É—ora da shafa'i da wutri ta yi doguwar addu'oin ta kafin ta kwanta sai juyi ta ke yi ta kasa barcin duba time ta yi ta ga past 9pm sai ta fito waje ta tsaya a tsakar gidan tana jiran jin dawowar shi dan bai dawo ba ga abincin sa nan ba'a kai masa ba zulfa'u kuma ta wuce turakar mai gidan ta a haka ta cigaba da tsayuwa har dai 9:30pm kafin ta ga shigowar sa zai wuce ta kira shi cikin sanyin murya ta ce

"Sai yanzu kake dawowa a cikin daren nan bayan ka san yanayin garin nan"!! Dakatawa yayi ya juyo a hankali suka haÉ—a ido sai ya ga damuwa a cikin idanun ta he became confused takawa yayi zuwa kusa da ita ya tsaya yana nazarin ta na wasu lokuta before he otter a word.

"Are you disturbed"? Shiru ta yi kafin ta ce

"Am not am just concern"ganaÉ—ayan su shiru suka yi kafin daga bisani ya ce da ita

"Go to bed tomorrow is a new day akwai ayyuka da yawa a kan mu goodnight"daga haka ya wuce ta ita kuma ta tsaya a wurin tana tunanin abin da ta yi is she scared of Mudan that his violence might affect Zaid?koh dai wani abin ne na daban? Babu mai bata amsa dan haka sai ta wuce zuwa É—akin ta kwanta but still barci bai É—auka ta ba sai around 12 na dare bata ma san lokacin da barcin ya É—auke ta ba..

*************
_two weeks later_
Chapter 19 · 0% Book details