← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 157

Sashe 92

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Share hawayen idanun ta tayi tana data sanin shawarar da ta bada Mudan ɗin dan ta san da a ce ta ƙi bashi wannan shawarar ta natse akan ita ya hukunta ta da babu abin da zai janyowa ɗan birni shiga halin da yake ciki kuma da a ce lokacin da ya ce da ita ta mai alama in sun fito ɗin nan bata mai ba da duk hakan bai faru ba,,yanzu gashi an ce mata an fitar da su ɗan birni daga ƙauyen rai a hannun Allah...
Kuka mai sauti ta shiga yi tuno da irin hantarar da aka rinƙa mata a washegari da abin ya faru dan an gano cewa tare suke da Mudan lokacin da ya aikata abin da fari ta so turjewa tayi rashin kunyar ta amma sai ta ga abin ya fi ƙarfin ta dan ko ta yi bata da mataimaki saboda a daren Mudan ya mata rashin mutuncin da bata taɓa mafarki ba..
Wani hawayen baƙin cikin ne ya silalo mata tunowa da tayi da abin da ta ji a matsayin sakamakon rashin lafiyar ta da ta kai sati tana yi.
Kuka sosai ta rinƙa risga dan ta tsani kan ta da in ana tsine masu a gari saboda rashin mutuncin da suke yi sai ta rinƙa ganin ai ba su ake tsinewa ba masu tsinewar su ke tsinewa kan su.
Ba zata manta ba akwai wata tsohuwar da Mudan ya saukewa mari saboda ita wai dan tana wucewa tana cin gyaɗa tana wurgi da ɓawon gyaɗar sai ya sauka saman fuskar tsohuwar sai tsohuwar ta ce da ita _*ƴar nan anya kina son gamawa da duniya lafiya kuwa,kina kallo na ki watso min ɓawon gyaɗa*_ shikenan kuwa Mudan ya ce da wa Allah ya haɗa sa in ba da tsohuwar nan ba ya shiga mata rashin kunya buɗar bakin ta ta ce da shi _*in duniya ce yara zaku gan ta ai*_ shikenan ya ɗaga hannu ya shararawa matar nan mari ya ce da ita ita kaɗai zata ga duniya su sun gama ganin ta har sun gama shawagi a cikin ta.suka yi gaba tsohuwar nan na kallon su har suka wuce ta ɗaga hannun ta sama tana roƙon sakayyar abin da yaran suka mata sauke hannun ta ne yayi daidai da juyowar Asma'u ta banka mata harara haɗe da jan tsaki tana faɗin wai fah addu'a take yi,sai suka saka dariya suka yi gaba abin su..

Kuka ta cigaba da yi dan a kullum sai ta tuno da ire iren rashin mutuncin da suka ma mutani a ƙauyen wanda a ko da yaushe cikin tsinuwar su suke ko da jama'an garin suka ji abin da ya faru suka shiga tsine mata wai har da baƙon da yake taimakon ta ma ta gwada mai rashin ɗa'ar ta toh ai ta ɗaga tuta gashi nan Mudan ɗin ya mata abin da ya dace da ita.
Labari bai ɓoyuwa tuni labarin rashin mutuncin da Mudan ya mata a daren ya karaɗe ƙauyen da rashin halascin da ta ma ɗan birni sannan ga gargaɗin da Mudan ya mata na kar ta kuma shaida sa a matsayin wanda ta sani babu shi babu ita,abin nan ya ma jama'ar ƙauyen koma daɗi suka rinƙa murna ai Allah ne ya fara sauko masu da aya kaɗan ma kenan suka fara gani,a nan gidan su kaf yayyen ta ƙyamar ta suke ji dan hani suke ai ita ta kai kan ta inda abin da faru da ita dan haka ba wani tausaya mata da zasu yi tun daga ranar suka fita harkar ta sao dai su bi ta da ido.
Dama mahaifiyar ta ba gamawa tayi da muzancin jama'a ba akan rashin tsawatarwa ɗiyar ta da bata yi akan tana barin ta tana fita suna ta'addanci tare da Mudan kuma ta zuba masu ido duk waɗannan kalamai su suka haɗu suka haifar mata da damuwa mai tsananin gaske toh da ta ga kwana biyu Asma'un ta fara hankaki har tana jan jiki da Mudan ɗin sai ta ji daɗi har take iya mayar da magana in ana mata habaici ko a waje ne amma ranar da ta ji abin da Asma'un tayi ta kuma ji ɗibar albarkar da Mudan ya mata sai ji aka yi ta faɗi ƙasa sumammiya ƴaƴan ta maza su suka taimaka aka kai ta wata ƙaramar PHC da ke chan nesa da gidan su a nan suka yi jinyar ta na tsayin kwanaki huɗu kafin a sallame su duk wannan jinyar ta hana Asma'u zuwa kusa da ita ta kuma ce matuƙar ta kusanto ta toh Allah ya isa ta je cjan ta sami Mudan ya zame mata uwa,uba da komai na rayuwa...abin ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba sai kuma a nata mentality ɗin ta ɗau hanya ta bi Mudan har gidan su wai ga abin da maman ta ta faɗa ya taimaka ya zo su je ya roƙar mata ita ta yi haƙuri ta bar ta ta je kusa da ita in ya so ma sai ya gayawa maman ta da yayyen ta maganar auren ta a masu aure tunda ga abin da ya faru,.
BuÉ—ar bakin sa sai ce mata yayi
_*"Ai ni banu abin da zai saka ni auren ki ba zaɓar wannan ɗan nasarar kika yi akai na ba har ni kamar ni Mudan in saka miki doka ki sa ƙafa ki take hmm ai babu abin da zan yi da ke ki je can inda na aika wannan garan ki aure sa amma ba ni ba dan ba zan aure ki ba*_"kuka ta saka mai tana faman roƙon sa amma ya nuna mata shi fah sam babu inda zai kai ta ta fitar mai a rayuwa kawai in ba haka ba itama ya san abin yi da ita..
Tun daga ranar ta shiga tashin hankalin da bata san ranar fitar ta ba sau uku tana zuwa gidan mai gari wai ko an ji labarin su ɗan birni amma amsar ɗaya ce su ma basu san inda yake ba,takan ƙulle kan ta a ɗaki ta ci kuka har bacci ya ɗauke ta kamar cikin ƙaya take tsabar tsangwamar da ake mata a garin a cikin gidan su ma ba zaman daɗi ake yi da ita ba.

Kamar bayan sati uku ta tafi wannan ƙaramar PHC da ke ƙauyen cikin dare ta je dan bata ganewa kan ta kwana biyu,ko da aka gwada ta aka sanar da ita matsalar da ke tare da ita,ji tayi kamar ta mutu a nan kasa kukan tayi sai zaman da tayi a wurin kamar marar rai,..
Tana barin wurin ta nufi gidan su Mudan ta sanar da shi abin da ya faru har da ma cikin maye yake amma sai da ya kashe mata gargaɗi akan kar ta masa wasa da ajiyar sa shi zai karɓi ajiyar sa kuma ta bari ya kama ta tana wasa da maganar sa sai ya nuna mata ɗaya grfen sa..da kukan azaba ta dawo gidan ta sanar da maman ta tana daga waje dan bata da ƴancin shiga ɗakin ma,amsat da maman ta ta bata shine halbin da ta mata da rediyo tana daga cikin ɗakin ta shiga sharɓe kuka tana data sanin haihuwar Asma'u da ta yi kalamai dai marasa daɗin ji ta rinƙa suƙar ta da shi.
Kwanar baƙin ciki tayi har ta fara tunanin kashe kan ta cikin daren kawai ta huta amma sai ta fasa dan ta san ƙila ɗan birni ya dawo ya zo ya fitar da ita daga cikin halin da take ciki..

Share hawayen ta tayi a karo marar adadi.ci da sha bata rasa ba amma walwala kam ya ƙaurace mata dan yayyen ta da suka ji hakan ma kasa yi mata komai suka yi sai ɗaya daga cikin su ne ma yayi ƙarfin halin zuwa har hideout ɗin su Mudan ya same sa ya lakaɗa masa dukan banza ya kuma ce da shi ko ya ƙi ko ya so dole in Asma'u ta haife abin da ke cikin ta ya aure ta in ba haka ba shi zai yi ajalin sa,..

Tunowa ta kuma yi da ranar da labari ya zo mata akan wasu sun ma Mudan dukar kawo wuƙa yana nan a gida rai a hannun Allah murnar da jama'ar garin suka yi bai kai wanda ta yi ba dan tun bayan faruwar abin bata kuma tsintar kan ta cikin walwala ba sai ranar dan har takawa tayi tsabar farinciki ko ba komai itama Allah ya saka mata da wulaƙancin da Mudan ya mata cikin ruwan sanyi...

Tashi tayi ta share hawayen ta ta shige koÉ—aÉ—É—iyar É—akin ta mai É—auke da katifa marar riga ta shimfiÉ—a zanin ta ta kwanta a kai tana tunanin ko me zai faru da ita kuma dan mai gari ya kira yayyen ta maza akan su zo yana son ganin su toh fitan su ne ta dawo tsakar gidan ta zauna zaman jiran su shine da ta gaji ta koma É—aki ta kwanta dan bata da jimirin yin doguwar zama tuni sai ta ji tana jin jiri sai dai kwanciya.
A ɗakin ma tana kwance ne amma tana tuno halin da Mudan yake ciki tun ranar da aka mai dukar nan an ce baya iya tashi kwance yake kamar matacce tunowa tayi da irin kukan da ta rinƙa yiwa mahaifiyar sa akan ta roƙar mata Mudan ya zo su yi aure amma sai tashi tayi ta bar ta zaune tsaƙar gidan tun daga ranar ita kuma bata kuma zuwa roƙar ta komai ba sai dai ba ranar Allah da zai wuce da ba zata saukewa Mudan kwandon Allah ya isa ba...
Chapter 92 · 0% Book details