← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 157

Sashe 91

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rasa abin cewa tayi tun da ya fara maganganun sa bata taɓa sanin baƙin hali irin na Mudan ya kai har haka ba a ce har ita kanta da take tare da shi yana neman salwantar da ita lallai mutani sun yi gaskiya da suke ce mata wata rana zata yi nadamar kasancewa tare da Mudan dan bai da halin kirki yanzu a ce har ita bai bar ta ba yana son takurawa rayuwar ta..
Wani ihu ya mata yana magana kamar taɓaɓɓe marar hankali
"Keeee Ma'u ina magana ne fah kina min eh ya ne ban gane ba ko baki ji na ne"?haÉ—iye yawu tayi tana jin wani mugu mugun tsoron sa na shigar ta sai ta daure ta ce
"Mudan me kake nufi me kake shirin yiwa É—an birni,ka san bai da laifi a duk wannan rashin haÉ—uwar tamu da kai duk laifi na ne wallahi bai da masaniya babu ruwan sa"wani dariyar Æ´an daba ya mata kafin ya tsuke fuskar sa ya fara magana
"Kin ji haushi kenan dan na yi magana marar kyau a kan sa,kenan ran ki ya ɓaci kenan dan na ce zan kashe wannan banzan gajan da yake son shiga tsakanina da ke"???tarar numfashin sa tayi tana son gyara mai tunanin sa dan ta san yana iya yin abin da ya ce ɗin
"A'a tsaya ka ji Mudan ni dai kawai ka rabu da zancen wai laifin ɗan birni ne ka mayar da laifin kai na kuma ina roƙon ka ka min rai kar ka lahanta sa ka yafe mai ni ka min abin da zaka mai bai da laifi ka ji"?dariyar bosawa yayi kafin ya ce
"Yanzu na gane nufin ki Ma'u wato dai kin amince ke in baki laifin da yaron nan yayi ko"?girgiza kai ta shiga yi dan tana gudun fitinar Mudan sam bata so wani halaƙa ta kuma shiga tsakanin su..
"Tsaya ka ji ni in za ka yarda madaɗin ka lahanta shi me zai hana ka ja mai kunne kawai amma ka san ɗan birni ne in ya zo ya kai ƙarar ka ka san babu wanda zai goyi bayan ka Mudan dan kaf ƙauyen nan tsine maka suke yi babu wani mai son ka ka rufa mana asiri"kallon uku saura kwata ya mata kafin ya ce
"In ja masa kunne kika ce"??sai ta girgiza mai kai kamar zombie sai ya ce
"Yayi..zan aiwatar da hakan...lallai zan ja masa kunne ta yadda ko hanyar da kika bi aka nuna mai aka ce ya kalla ba zai kalla ba...amma kafin nan tare da ke zamu tafi wun ja mai kunnen"!!tsoro ne ya shige ta ita sam bata so a ce ya ma É—an birni ta'addancin sa tana tare da shi ta fi son ya tafi yayi shi kaÉ—ai in ya so ko daga baya ne sai ta nemi afuwar É—an birni amma bata son bin sa..
Kiran sunan ta yayi irin na marasa tarbiyar nan sai ta amsa duk tsoron sa ya gama mamaye ta
"Yanzu ki tabbata kin daidaici lokacin fitowar sa kina ganin ya fito ki min alama zan tsaya a nan..ya faɗa yana nuna mata bayan gidan su wani ɗan loloƙi ne a wurin nan yake son fakewa dan kar a gan sa,kin gane ko"??ta amsa mai tana mai girgiza kai.
Daga haka bai kuma ce mata ƙala ba ya nufi hanyar loloƙin dan ya gama ƙudirar sai ya kawar da Zaid a hanyar sa saboda ya gama kai sa maƙura...

Bayan ya wuce ne ta shiga yin kuka ita bata san me yake damin Mudan ba ko tsoron kar a kama sa baya ji toh idan ɗan birnin ya fi ƙarfin sa fah?idan ya tashi shi ya lahanta sa fah me zai ce?sam ta kasa samo mafita ɗaya ta yadda duk wani rashin hankalin da Mudan zai yi ba za'a kira sunan ta ba dan ta gaji da zagin da ake mata cikin gari ana cewa tana ta'addanci tare da saurayin ta duk inda suka kutsa sai an zage su,yanzu tana son ta fita a harkar sa kwata kwata amma ta yaya gashi yana son taɓa lafiyar ɗan birni...

Tana cikin tunanin nata sai ta hangi giftawar su Zaid ta ja da baya kaÉ—an har ta ga shigewar su motar su kamar ta gudu ta bar Mudan a wurin sai dai da ta tuno maganar da ya faÉ— mata na cewa zai ja mai kunne ne sai kawai ta bi bango a hankali ta mai alama ta bayan gidan na su kamar dai yadda ta saba yi in sun tafi rashin jin su.
Fitowa yayi yana faman hararar motar yana ƙwafa ita kuma tana bin sa da ido har ta kama hanya zata wuce gidan su ya damƙo hannun ta ta juyo cikin tsoro ta ce
"Me kuma zan maka ba gashi nan na sanar da kai ba"sai ya aika mata da wani mugun kallo kafin ya ce
"Ce maki aka yi ni wawa ne da zan bar ki ki tafi ba tare da na ja masa kunnen a gaban ki ba"??gaban ta ne ya faÉ—i sai ta ce mai
"Yanzu me kake so in maka kuma"?murmushin gefen baki yayi kafin ya ce
"Biyo ni zaki yi mu tafi dan in ja masa kunne a gaban idanun ki"a rikice ta kalle sa tana girgiza kai sai yayi dariya kafin ya ce.
"Yarinya kin fi kowa sanin hali na au ki biyo ni mu tafi tare au kuma....."ya tsayar da maganar sa yana mata nuni da cikin gidan su sarai ta gane me yake nufi wato ko ta bi sa ko ya taɓa lafiyar maman ta.
Kuka ta shiga rera mai zata yi magana ya ingiza ƙeyar ta zuwa napep da aka faka gaba kaɗan da gidan su suna zuwa ya tura ta cikin ɗaya daga napep ɗin dan har biyu ne ɗayan ƴan daban sa ne ɗayan kuma daga shi sai ita sai mai napep wanda shima ɗan gidan sa ne shi ke kai sa duk inda zai tafi yin ta'addancin sa a faɗin ƙauyen nan...

Ko da suka hau kan titin sai faman razana ta yake yi da maganganun sa yana daɗa nuna mata in ta kuskura ta mai wasa da hankali ta kai sa inda ba nan Zaid ke bi ba da motar sa sai ya gyara mata tunani,ire iren maganganun da ya rinƙa gaya mata kenan ya ruɗa ta har ta ga da ta rasa ran ta da na maman ta gwamma a je a ja ma Zaid ɗin kunne kawai ai in an yi haka zai fi mata sauƙi in ya so sai su bar ƙauyen tare tunda ya ce da ita ai zai kai ta birni ya saka ta a makaranta..

Suna tafe tana nuna masu hanyar da motar ke bi dan shi kam Mudan ya sha ya bugu ba kaÉ—an ba kawai so ya ke ya ga gawar Zaid ko zai sami salama a zuciyar sa..

Suna kawowa daidai inda motar su Zaid ya tsaya ta gayawa Mudan amma ya ce ba ita zata gaya mai abin da ya kamata ba shi zai tsara abin da ran sa ke so,shiru ta mai tana ɓarin jiki dan bai mata kama da Mudan da ta sani ba a baya wannan Mudan ɗin mugu ne dan so yake ya gwada muguntar sa har a kan ta..

Sai da ya tabbatar tarkon sa ya ɗanu da kyau sannan ya ce da sauran su fito su yanki dajin sannan ya ce a ingizo mai Asma'u,tana turjewa dan sam bata son ganin abin da zai yiwa Zaid a gaban ta sai dai ƙarfin maza ya fi nata dan dolen ta ta natsu ta bi su har cikin dajin dan sai a nan ta gane cewa tarko Mudan ya ɗanawa ɗan birni ba wani jan kunnen da zai yi mai sannan ya raina mata hankali ne kawai yana so yayi ta'addancin sa a gaban ta in ya so ya ja mata baƙin jini..
Da kukan ta aka illata É—an birni a gaban ta ta kasa hanawa hasalima sai hukuncin da Mudan É—in ya mata dan ta nuna mai bai dace ba abin da ya yi.
Chapter 91 · 0% Book details