← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 157

Sashe 77

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

  _5:14am_
A daidai wannan lokacin ne ya juya da nufin gyara kwanciyar sa sai kuma ya dakata daga komawa baccin dan ya ji different scent ba kamar wanda ya saba ji ba in ya juya a ɗakin sa,a hankali ya shiga buɗe idanun sa har ya gama buɗe su duka sai a nan ya fara tuno abin da ya faru da shi a daren jiya,dafe goshin sa yayi yana mai lumshe idanun sa kusan mintoci kafin ya buɗe su ya juya ta ɗaya gefen sa sai ya ganta kwance lafiya ƙalau tana kwasar baccin ta juyawa yayi ya ɗauko remote ɗin air split na ɗakin ya rage yawan shi dan yana gudun wani abin da zai janyo mata ƙaruwar zazzaɓin da take ciki already.
  Tashi yayi daga kan gadon ya nufi hanyar fita daga ɗakin,ba sallah take ba bare ya tashe ta sai kawai yayi tafiyar sa zuwa ɗakin sa ya yi alwala ya zo yayi sallah..
  Wani baƙon lamarin da ya same sa shine yadda ya taƙarƙare ya rinƙa yi mata addu'ar samin lafuya haɗe da yi mata addu'ar tsari daga yin wani rashin lafiyar dan shi kaɗai ya san yadda ya ji a jiya da ta shiga halin nan sam baya so ya kuma witnessing..
  Sai da haske ya fara haska ɗakin nasa sannan ya tashi daga saman sallayar nasa ya dawo kan gadon sa ya kwanta daga haka ne wani session ma baccin ya kuma yin awon gaba da shi kuma a cikin wannan baccin nasa ne ya rinƙa mafarke mafarke marasa daɗi dan kaf abin da ya faru da shi ne a dajin nan ya shiga dawo mai sai ya shiga karkarwa yana haɗe jikin sa wu ɗaya at the same time yana karantar add'uar tsari da kariya bai farkan ba haka bai daina yin add'uar ba har sai da hotunan mummunar ranar takau daga baccin sa sannan ya cigaba da yin baccin duk ya gama haɗa zufa gashi ya rufe kan sa da blanket kuma ba ƙaramin zufa yake yi ba..

  Juyawar ta ke da wuya taji ƙarar wayar ta sai ta fara laluɓo wayar har da ta kai hannun ta kan wayar ba tare da ta duba sunan ba ta ɗauka haɗe da karawa a kunnen ta ta kwanto ta gefen da ta ɗauko wayar idanun ta rufe da ragowar magagin bacci cikin muryar ta ta ce
  "Hellooo"..haka ta ja kalmar wanda ya saka Umma kallon aminiyar ta Hajiya Madina sai suka ɗan yi murmushi dan dama sai da Ammi ta hana ta kiran ta ce da ita maybe fah basu tashi ba amma Umma ta ce ita kam tana jin yin waya da su..
  Jin ba'a ce komai ba sai ta kuma maimaita kalmar
  "Hello"sai a wannan karon ne aka amsa
  "Goodmorning Mrs Zaid Maher"muryar da ta ji ne haɗe da sunan da aka kura ta da shi ga kuma ƙamshin da ta ji su suka haɗu suka saka ta warewa da kyau ta tashi a birkice tana zazzaro idanu waje cikin rikiɗewa ai a sittin ta ce
  "Umma please can i call you back in the next 15minutes"??tayi tambayar gaban ta na faɗi sai Umma ta ce mata
  "Yeah...sure...why not...just..just take your time okey baby bye"wani irin ajiyar zuciya ta sauke idanun ta na daɗa buɗuwa da kyau kan ta na sara mata kamar ta kwana biyu tana rashin lafiya.
  Dafe kanta tayi ta zauna kam gadon tana son tuno abin da ya faru jiya..
Iya abin da take iya tunawa shine jiya sun yi sai da safe ita da Zaid kuma distance dake tsakanin su da ɗan tazara tana kwance ne shi kuma daga bakin ƙifar ya sallame ta but how come take jin ƙamshin turaren sa a saman gadon ta gashi nan dai babu alamun mutum ya shigo dan gadon is neat babu wani canji daga yadda yake..

Ganin zata wahal da kan ta garin nemo amsar da bata san inda zata samo shi ba ya sa ta tashi ta nufi hanyar bayi dan gyara kanta.
  Wanka tayi ta gyara jikin ta sannan ta fito ta buɗe closet na kayan ta duk ta ma rasa abin sakawa sai kawai ta ɗau wata bum short da one single hand shimi ta saka ko bra bata saka ba da ta gama saka kayan sai ta ɗauko wata doguwar riga mai hula orange colour blended with red touches ta saka ya kuwa sauko mata har ƙasa sai ta nemi room slippers ta saka kasancewar babi inda zasu tafi ranar dan next checkup nasa sai washegari zaman gida zasu yi a yau..
 
  Turare kala kala ta feshe jikin ta da shi sanna ta ɗau wayar ta tayi dialing digits na Umman ta,tana tafe da wayar a hannun ta har ta iso falon ta nemi wuri ta zauna haɗe da ɗauko remote ta ƙunna tv,tana ƙunna tv Umma na ɗaga wayar sai ta riga ta yin magana ta hanyar ce mata
  "Umma na ina kwana"dariyar manya Hajiya Zeenat tayi kafin ta ce
  "Bilkisu kenan shikenan cikin waɗanda zaki manta har da ni a ciki baby?,,ki ce kawai in kama baby Zara dan ina ganin in kuka yi naku ƴaƴan hana su zuwa wun mu zaku yi tunda gashi tun yanzu kun manta mu"murmushi tayi kaɗan kafin ta ce
"Umma ni na isa,,wallahi ba haka bane Umma kin ga jiya gabaɗaya ban yi baccin daɗi ba rashin lafiya duk ya saka ni gaba dama kwanannan kawai managing kai na nake yi dan bana so Zaid ya zama demoralize saboda ni but am really sick please Umma ki min haƙuri inshaAllah hakan ba zai kuma faruwa ba kin ji"?tun da ta fara wannan maganar babu gaɓar da ya taɓa Umma sai inda Bilkisu ke faɗin"jiya bata yi baccin daɗi ba kuma ganaɗaya satin managing kan ta take yi" what does that implies?
  Cikin jan wani irin ƙara Umma ta ce
"Baby you pregnant"tari Bilkisu ta shiga yi har tana wani shiÉ—ewa tsabar mamakin abin da Umma ta faÉ—i kuma ya zo mata ne kai tsaye daga sama.
  Sorry Umman ta shiga yi mata sai Bilkisun ta tari numfashin ta ta hanyar ce mata
  "Umma is not what you think,,ban da lafiya ne saboda monthly cycle ɗi na was about coming ne and jiya da na ce maki ban yi baccin daɗi ba,cramps nake ta experiencing a bacci na shi nake nufi ba abin da kike tunani bane"sai kuma anmashuwar fuskokin su ya kau Hajiya Zeenat ta kalli Hajiya Madina suka girgiza kai su duk tunanin su ko sun kusa zama grannies ne especially Ammi da yanzu ta ɗora buri akan babban ɗan ta Zaid tana bala'in son samin jika daga gare sa time is flying any moment za'a wayi gari babu su and she can't help her self but say it out to her friend wato Hajiya Zeenat and she made her a promise that inshaAllah ba zasu bar duniyar ba ba tare da sun ga jikokin su ba waɗannan kalamai kaɗai ke kwantar mata da hankali..

  "Kina nufin har yanzu baki fara jin alamomin masu ciki ba baby"?da mamaki ta ce
  "Strange Umma,,why are you asking me such question"??kamar jirar ta Umman take ta ce
  "Saboda na matsu in sami jika why are you people delaying it"??ya salam su kam Allah ya albarkace su da iyaye sai ta ce
  "Umma in dai har irin tambayar da zaki na yi min kenan toh i wi stop picking your calls i promise you"babu alamar wasa a muryar ta sai suka kuma kallon juna suka girgiza kai sai Hajiya Zeenat ta ce
  "Fine na daina kuma ba zan sake ba but ina dai fata baby ba planning kuke yi b?dan Allah kar ku bi hanyar yaran zamanin nan masu cewa sai sun gama enjoying honeymoon kafin suyi conceiving please kar ku mana haka mu muna buƙatar jikoki as soon as possible"shiru Bilkisun tayi tana sauraron mahaifiyar tata cikin rashin sanin abin da zata ce da ita dan abin nasu ya fara takura mata 2 days back Ammi ta yi nata part ɗin and now,,her mom is portraying her own pattern..

  "Oh ya Allah Umma,dan Allah ki daina ke da Ammi have to stop all these things you are doing,seriously kuna takura ni i can't please,,,sai anjima i will call you when the need arises"ɗiff ta kashe wayar ta ajiye saman kujerar haɗe da kwantar da kanta saman pillow dake bayan kujerar,shiru tayi tana tunani..
  She was lost in her thinking har ya fito bata lura ba tana kan tunanin abubuwan da ke faruwa da ita a ƴan kwanakin nan ga matsananncin son Zaid da ke juya ta ga asassawar iyayen su da wanne zata ji..
  Ya kai minti ɗaya tsaye kan ta bata sani ba shi kuma a nasa tunanin gani yake kamar she is still in pains shi yasa take zaune haka..
  Zama yayi a same chair da take zaune ya kai hannu ya taɓa gefen wuyar ta sai ta buɗe idanun ta a ɗan birkice sai ta ga shine hakan ya janyo mata baƙuwar yanayi tun ma bai tambaye ta ba kenan ina ga in ya tambayi health ɗin ta.
Chapter 77 · 0% Book details