← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 157

Sashe 113

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Tun da ta hau kan titin nan ta rinƙa tunanin anya abin da take tunani ne kuwa ko dai kawai damuwa da tayi ne ya sa take ganin kamar shi ne?no so soon,,tukunna dai,..tunani barkatai ta ke ta yi har ta iso inda ta fito da niyar zuwa.
Buɗe mata gate aka yi ta shige ta nufi wurin parking ta gyara zaman motar ta sannan ta kashe ta fito ko jakar babu a hannun ta sai wayar ta,kai tsaye ta shiga  ciki,lifter na sauke ta ya buɗu ta ƙarasa ciki direct sashen sa ta nufa fuskar ta a haɗe shi kam bai san ta iso ba sai da ta tsaya daidai nashi cue ɗin yana gamawa da wanda ke gaba ɗago kan da zai yi ya ga next customer me zai gani..
  Baƙi na ɓari ya ce
"Apple me kike yi a nan"?halin ko in kula ta nuna mai ta ce ƙasa ƙasa
"Ka fito mu tafi waje kawai kafin in yi maka abin kunya"cikin sauri da tsatsarfa ya shig nodding mata kai harara ta banka mai sannan ta juya zata fita sai ta ji ana cewa
"Some one that looks like Bilal did you see her"sai aka juya ana kallon ta dan son tantance maganar ai kuwa suka yi nasarar gano tsantsar kamannin suk shiga al'ajabin abin sai suka dakatar da Bilal É—in suna tambayar sa
"Is she the apple you always talk about your twin sis"??murmushin yaƙe yayi yana mai girgiza ya ce
"Yes..,she is the one"!!suka ce mai
"She is cute you look alike"
"Thank you"sai É—aya daga cikin su ya ce
"I like her"gwalalo idanu yayi waje ya ce cikin yin ƙasa da murya
"Hey dude she is married"da mamaki ya ce
"She"?gyaÉ—a mai kai yayi yayi gaba dan ta É—an jima da fita.
  A waje suka haɗu ta ɗaure fuska kamar bata san dariya ba shi kam bai san da me ta zo mai ba Allah dai ya sa ba ritsa sa ta zo yi ba
  Buɗe motar tayi ta mai alama da kai sai ya shiga ita kuma ta zaga zuwa gefen ta ta shige ta ja ƙofar da ƙarfin ta kamar zata ɓalle har sai da hanjin sa ya kaɗa dan tsoron da ya ji.
Saka seat belt tayi ta ƙunna motar ta tayar,baki wangale yake kallon ta har suka fita da ya ga hanyar da ta ɗauka sai ya ce
"Apple ina zaki kai ni kin dai san a bakin aiki nake i might loss my job for leaving without a reason"harara ta maka mai tana faÉ—in
"In ka dawo a kore ka mana ina ruwa na"ta yi tsaki ta cigaba da jan motar rasa abin cewa yayi a zuciyar sa addu'a yake yi Allah ya fisshe sa daga masifar ta dan ya ga yau shi take jin yi.
  "Apple you are crazy what's all these"? Banza ta mai ta yi concentrating a jan motar ta.
  Daidai guest house dake kallon na Dr Maher ta ja wata burki har sai da yayi gaba yayi baya ya ɗago yana haki yana faɗin
"Are you trying to kill me or what"?
  Cikin masifa ta ce
"Da ma zan iya kashe ka da na huta dan haushin ka da nake ji kashe ka shi ya fiye min huce takaicin da nake ji game da kai"!!shiru yayi ya san bai kyauta mata ba shima yana jin wani iri ba daÉ—i a ran sa.
   Kuka ta saka mai a motar tana yi ne daga cikin zuciyar ta dan abin na damin ta wariyar launin fatar da ake mata na damin ta ba kaɗan ba,bai hana ta kukan ba sai da tayi mai isar ta sannan ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya for a while suka yi observing one minute of a silence sannan ya riƙo hannun ta yana faɗin
"Apple am sorry please forgive me na san na aikata maki laifi mai girma amma ki gafarce ni"muryar sa na rawa yayi maganar sai ta ji ɓacin ran ta ya ragu dan haka ta buɗe baki cikin sanyi ta ce
  "Bilal in za'a haɗe min kai har da kai cikin masu haɗe min kai Bilal?kana twin brother ɗi na?are you fair to me?did i deserve that from you"?hawaye ne suka silalo mata ta share tana jan hancin ta sai ya ce
"I know i wronged you amma ki gafarce ni dan Allah apple try to understand me ba da niya na yi ba su Umma ne suka hana ni sauraron ki ki yi haƙuri twinie"!!kallon sa tayi tana girgiza kai
"Not that alone Bilal...,a ce an saka bikin ka mu kwana gida ɗaya mu tashi tare har na wuce ku na fita amma baka iya sanar da ni ba sai da na tafi office Baha ki sanar da ni haka ka tsane ni kaima Bilal"??, tana hawaye ta mai tambayar sai kawai ya ji gaɓoɓin jikin sa ya mutu jikin sa ya matu tausayin twin sis ɗin nasa ya kama sa he can't continue with the plan he is out.
  "Ki yafe min twinie am sorry and deeply sorry please"kasa ce mata komai yayi shima duk kamar zai yi kuka kallon sa take yi dan ta san in kowa zai juya mata baya toh ban da Bilal shi yasa ta zo nan ɗin da shi dan sanin abin da ya saka sa yin abin da yake yi
"Fine na ji but just tell me something"gyaɗa mata kai yayi ya ce. 
"What is it"?sai da ta share fuskar ta sannan ta ce
  "Did you still love me"buɗe baki yayi da mamaki sai ya ce
   "Wani irin tambaya ne haka twinie?of course you know that i do"sai ta girgiza kai tana faɗin
"Ban yarda ba Bilal da kana so na da baka yarda an haÉ—u da kai an juya min baya ba"dafe goshin sa yayi yayi shiru kamar baya wurin sai chan ya É—ago ya ce
"Bilkisu kin san ban da Umma da Abba,ke na fi so dan kece blood twin É—i na i can't hate you i love and care about you"..shiru ta mai sannan ta ce
"Can i count on you"?da sauri ya girgiza mata kai sai ta yi shiru ta ƙunna motar ta tayar.
  Tun da suka fara tafiyar babu wanda yayi magana har ta dawo da shi office ɗin sa suka yi sallama ya shige ita kuma ta ja ta koma asibiti...

 
Shiga office É—in tayi ta kwashi abubuwan da ke da muhimmancin gare ta ta fito ta yi sallama da ma'aikatan sannan ta wuce ko da ta iso gidan ba Luk ba Bilal haka ma Umman ta sai tayi shigewar ta ciki ta kwanta ba jimawa bacci mai daÉ—i ya É—auke ta..

  A fannin Zaid kuwa abin ba sauƙi sai sauƙin Allah ba abin da ke mai yawo sai iskancin da Aslam ya wa matar sa shi gani ma yake in har bai hukunta sa ba toh zai cutu,gabaɗaya ranar a cikin duhu yayi sa dan da ya rufe idanun sa wannan event ɗin ke dawo mai abin ba ƙaramin bashi haushi yake yi ba gashi gidan ba ƙaramin faɗi ya mai ba dan daga shi sai shi hatta da ma'aikatan da aka zuba masu a gidan ya sallame su ya ce matar gidan bata zo ba sai ta dawo zasu dawo,abincin da yake ci shi ke preparing but he can swear that he misses his wife and he need her close to him but dole ya bata space dan tana buƙatar hakan..

 
*****************
 
_2 weeks later_

  Tun ranar da abin nan ya faru a asibitin Bilkisu bata ƙara zuwa asibitin ba sai ta koma ɗaya asibitin and she is serving as a head manager a chan ɗin while Zaid works at skyline shi da Aslam a irin zaman da suke yi ba su yin ga maciji da juna daga kallon kallon hadarin kaji sai jefar juna da magana da suke yi in sun haɗe a Theater room.
  Tun wannan rana Zaid ya fara sakawa Aslam ido dan hasan wawa ne sai ya ce zai nemar mai mata amma kafin yayi hakan yana so ya gyara mai tunanin sa..
  Mugun haukar kishin ta ke damin sa amma bai sani ba dan har da ma ba asibiti ɗaya suke zuwa ba amma yana zama very conscious na duk wani movements ɗin Aslam a asibitin hatta da zaman ofishin sa baya barin sa yayi shi cikin lumana ya rinƙa bumping mai office kamar office ɗin nasa ne.
  A wannan period ɗin kuwa Aslam ya gama binciko abin da zai binciko gameda matsayin auren Zaid da Bilkisu ya kuma rantse sai ya raba shi dan babu wani amfami zamam da ba tare ake yin sa ba in shi Zaid ɗin bai buƙatar ta shi yana buƙatar ta ba kaɗan ba..
  Ido kawai iyayen ke bin su da shi dan su kam sun san watan wata rana dole yaran su dawo hayyacin su but Umma tana matuƙar tausaya ɗiyar nata dan ta san ta gama antaya cikin mayen son Zaid ɗin amma rashin fahimta ya sa suka kasa gane matsalolin su.

Son Zaid sai abin da ya ƙaru a zuciyar Bilkisu dan a iya zaman nn da suka yi basu tare gani take kamar rayuwa take yi ba dan tana jin daɗin sa ba,rashin zuwan Zaid gare ta ya janyo mata yawan tunani ko wani lokaci ko aiki take yi a theater yana nan maƙale cikin ran ta ta kasa yaƙuce son sa,a yadda taji labari shine Zaid na tafiya aiki a skyline kullum kuma baya tashi da wuri sai yamma tun safe sai ta yi tunanin ko bai tafi ƙauyen koma bane ko kuma ya aika a tafi dubo Asma'un ne.
Chapter 113 · 0% Book details