← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 157

Sashe 139

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaɗan kaɗan ta buɗe idanun ta har ta gama buɗewa gabaɗaya sai ta sauke su kan Hajiya Zeenat da ke zaune idanun ta jazir fuskar ta ya ɓaci da hawaye duk kamar ba ita ba...
Daɗa girman idanun ta tayi sai ta ga eh da gaske Umman ta ne dan haka ta yunƙura zata tashi sai Hajiya Zeenat tayi saurin maida ta tana ce mata
"Kwanta baby,,kwanta please"idanun ta na ciccikowa da hawaye sai dai bata bari sun fito ba ta rinƙa riƙe su haka ta kwantan tana jin ciwon jiki gabaɗaya bata jin daɗin jikin ta sai yi mata wani iri yake yi gashi jiri ya saka ta a gaba...
Hajiya Zeenat ce ta saka hannun ta tana gyara mata sumar ta da suka É—an barbaje tana jan hanci tana faÉ—in
"Ya jikin naki baby"??kallon Umman nata tayi tana jin anya tana iya yin magana kuwa ko dai tayi shiru ne...sai ta ji muryar Hajiya Zeenat tana faÉ—in
"Go on speak out,kina iya magana yanzu,yi maganar ki kawai"..
Gwada gyara murya tayi sai ta ji throat É—in ta ya buÉ—u sai ta gwada yin magana
"Ahhh....ah"sai ta yi shiru sai Umman ta yi fara'a tana murna ta ce
"Yess yes cigaba"...da sauri ta buÉ—e bakin tana faÉ—in
"Umm..ummmm..Umma...Zaid.Zaid"sai kuka maganar ta ƙaƙare mata ta faɗa jikin mahaifiyar ta tana rusa kuka rarrashin ta ta shiga yi dan tun zuwan su ƙasar suke ta kula da ita dan so suke su tabbatar da bayanin da likitan ya masu akan dalilin aikata abin da ta aikatan dan gani suke maybe akwai wani dalilin ne na daban....
Almost 15seconds tana kuka Hajiya Zeenat tana rarrashin ta daga ƙarshe ta ɗago kan ta tana faɗin
"Umma Zaid fah,,ina yake,,,ina miji na Umma i almost killed him...da hannu na Umma da hannu na na kusa halaka miji na miji na the father of my baby Umma i want to see him"...duk a bauɗe take maganganun dan sam ba'a hayyacin ta take ba maganar sam a hargitse yake fitowa daga bakin ta ƙarshe dai kiran likita Hajiya Zeenat tayi tana hawaye aka zo aka mata abin da zai yiwu da maganar a bakin ta ta rufe idanun ta bacci ya ɗauke ta...

Fita daga ɗakin Hajiya Zeenat tayi ta zauna a kujerar dake kallon ɗakin ta rinƙa risgar kuka tana share hawayen ta dan ta rasa ainihin dalilin Bilkisu na yin hakan dan sun yi tunanin in akwai wani abin ya kamata likitan ya sanar da su amma bai sanar da su ya ɓoye masu sannan ya sanar da Bilkisu ita kaɗai alhalin suma ɗin families ne..

Dafa ta aka yi sai ta ɗago ta ga Hajiya Madina ce dan ita kaɗai ce ke da ƙarfin halin iya rarrashin aminiyar tata ba wai dan abin bai shige ta ba a'a sai dan son samin kwanciyar hankalin abubuwa saboda a ji dalilin Bilkisu na aikata hakan,,.da wata ce ta aikata ma ɗan ta hakakn ba Bilkisu ba toh lallai duk son da take mai da iƙirarin ita ɗin matar sa ce dole sai ta saka an kame ta hukuma sun hukunta mata ita amma wannan ɗin rainon su ne ko ba komai akwai amintaka mai ƙarfi tsakanin family ɗin su da na su Bilkisu dole a rinƙa yi ana dubawa...
Jiya da dare suka iso sakamakon kiran gaggawar da asibitin ta masu akan su zo suyi signing aka masu bayani sama sama tun a daren ranar da aka kawo su asibitin shi yasa su suka saka aka nemo masu ticket ɗin dubai su biyun in yaso daga baya in suka ga yanayin jikin nasu zasu sanar da iyayen nasu maza in na zuwa a duba su ne sai su zo in kuma da sauƙi sai a bar shi in sun farfaɗo sai su dawo nan Nigeria...
Toh a jiyan da dare aka masa aikin cikin gaggawa kuma an tabbatar masu da cewa zai farka cikin awowi 72-78 kuma ba zai daÉ—e kamar na farkon ba a jinya da zarar ya farka zai iya komawa baccin kwanaki biyu sannan ya farka gabaÉ—aya,toh jin wannan ne ma ya sanyaya masu zukatan su dan sun tsorata gani suke kamar wannan É—in ma zai kasance irin na farkon nan ne...

Zama tayi kusa da ita tana rubbing hannun ta bisa kafaÉ—ar ta
"Ya isa haka Hajiya Zeenat in kika tasa ta gaba kina kuka ta yaya ni zan sami ƙwarin gwiwar cewa zasu farka any time soon?uhum?ki daina kin ji"?..kallon ta tayi tana girgiza kai tana faɗin
"Ba wannan ba Hajiya..,me ya sa Bilkisu zata ɗau babbar risk haka ko da gani tayi yin abin da tayi shine daidai ai bai dace muna iyayen su suna ƙarƙashin mu duk wani wayo da dabarar su mu mun fi su mun riga su sanin menene duniyar ya zata ɗau hukunci irin wannan a hannun ta bata da tunani ne ko me"??ta share hawayen ta sai Hajiya Madina ta yi zugum ita kan ta abin da ta matsu ta ji kenan dan duk bayanin da aka masu bai wani gamsar da su ba..
Rarrashin ta kawai take yi itama tana rarrashin kan ta at the same time dan encouragement da assurance suke buƙata...

Daren nan haka suka yi shi baccin ma ƙaurace masu yayi bai zo ba saboda fargaba da zullumin ko meye mafitar su ina kuma makomar su da na ƴaƴan su,waya kawai suka yi ma ƴan gidan akan su kwantar da hankalin su very soon zasu farka daga Zaid ɗin har Bilkisun shi dai Bilal matsuwa yayi akan sai ya zo amma Hajiya Zeenat ta taka mai birki akan babu inda zai taho ya natsu a gida ya bi su da addu'a if not zata yi fushi da shi...

***************
_1 day later_

Da sanyin safiyar ranar laraba Bilkisu ta farka cikin ƙarfin jiki dan da ƙarfin ta farka ta dawo hayyacin ta sai ta cigaba da kwanciyar tayi shiru tana sauraron abin da zuciyar ta ke karanto mata a hankali ta fara recalling abubuwan da ya faru har kawo zuwan mahaifiyar ta da ta gan ta jiya sama sama..
Wuf ta miƙe ta yi hanyar waje kai babu ɗankwali,daga nesa da suke zaune suka hango ta cikin sauri suka taso suka nufo ta sai suka ga duk a hargitse take saurin mai da ta ɗakin suka yi suna rarrashin ta dan tuejewa take tana faɗin ita a bar ta ta tafi wurin mijin ta ta saka masu hauka da iya ƙarfin ta da ƙyar suka tanƙwara ta dan cikin da ke jikin ta is still unstable yana iya ɓarewa in aka asassa mai..
Danne ta bisa gadon Hajiya Madina tayi tana faÉ—in
"Ki natsu mana Bilkisu ya kike abu haka kamar wacce bata san ƙaddara ba ko so kike ki ce min kin manta jinjirin ciki ne da ke da kike wannan hayaniyar"sai a sannan hankalin ta ya ɗan dawo mata ta fara recalling cewa ranar da aka yi masu babbar albishir da cewa ciki ne da ita sai dai same day ɗin ne ta aikata babbar kuskuren da take regretting a rayuwar ta tun daga ranar har zuwa yau a yanzu...

"Ammi...Ammi Zaid É—i na Zaid,na mai laifi ya gafarce ni ya yafe min ban kuma yi daga wannan shi kenan daga wannan bai kuma experiencing wahalar rayuwar sa kuma please take me to him i..i want to see my husband"..kuka take yi babu ji su kuma dama abin da suke son ji kenan dan haka suka zaunar da ita da kyau fuskar Hajiya Zeenat babu wasa ta ce
"FaÉ—a min Bilkisu..muna jin ki yi mana bayanin dalilin kisar da kika yi niyar yiwa mijin ki are you that heartless or what speak up"??da sauri ta É—ago kan ta tana girgiza kai tana kuka ta ce
"No Umma ba kashe shi zan yi ba wallahi ina son sa ina son sa fiye da rayuwa ta amma ba zan iya ganin sa cikin halin da ya shiga ba a watannin da suka wuce ba i can't bear seeing him in great pains ba zan iya ba shi yasa nayi da kai na"by now Hajiya Zeenat is already losing her patience dan haka cikin daka tsawa ta ce
"Toh dan ubanki buɗe baki kiyi magana buɗe bakin ki ki mana bayani tun kafin rai na ya ɓaci da ke"saurin ja da baya tayi Hajiya Madina ta ɗan ɗaga murya tana dakatar da Hajiya Zeenat akan ta rage zafin da ta ke yi da Bilkisun su lallaɓa ta dai har su ji dalilin ta..
Tana jikin Hajiya Madina tana ɓari tana kuka mai shiga rai dan duk zafin da suke ji bai kai wanda ita take ji ba duk tashin hankalin da suke ciki bai kai wanda ita take ciki ba...
Masifar Hajiya Zeenat zata kuma yi Hajiya Madina ta É—aga murya tana faÉ—in
"Kina furta wata kalma toh gaskiya barin É—akin nan zaki yi kin ji na gaya maki bana son fitinar nan taki haba da wanne zata ji da masifar ki ko da halin da mijin ta ke ciki"shiru Hajiya Zeenat tayi tana faman hararar Bilkisu..
Kallon ta Hajiya Madina tayi tana faÉ—in
"Yi shiru ki mana bayanin abin da ya faru kin ji"??gyaɗa kai tayi tana jan numfashi yayin da Hajiya Madina ke rubbing bayan ta sai ɓari jikin ta ke yi kusan mintuna da yawa tana a haka har dai ta fara iya controlling kan ta suna sauraron ta sannan ta buɗe baki ta fara yi masu bayani kamar haka
Chapter 139 · 0% Book details