← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 157

Sashe 55

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 9 min read

Rarrashin ta Bahajjatu ta ke yi a lokaci guda tana mamakin irin mummunar so da ya kama aminiyar ta wanda yake fizgar ta ta ko ina amma ita ɗin ta ƙi yarda da hakan hasalima har yanzu bata gane cewa son Zaid ne da kishin sa ya mata dabaibayi haɗe da kane kane a zuciya ba dan alamu sun nuna ƙarara cewa mugun kishin Zaid ne ke barazana da zuciyar aminiyar tata.
Kallon ta tayi ta ce
"Beelove ba kya ganin kina wahalar da zuciyar ki da yawa akan zancen zuciyar ki"?É—agowa tayi haÉ—e da share hawayen ta da bayan hannun ta sai ta ce
"Baha ban sani ba,wallahi ban sani ba ni kaina ba son wannan halin da nake ciki nake ba sam ban san yadda zan yi ba"!!da cracking voice ta ida maganar wanda ya saka Bahajjatu girgiza kai kawai dan ta san ko shekara zata yi tana mata bayanin feelings da take da shi towards her brother ba ganewa zata yi dan haka ta É—an yi tapping shoulder É—in ta tana mai cewa
"Beelove zan bar ki ki gano abin da ke damin ki a zuciyar ki wanda ke faman wahal da ke"kallon juna suka yi kafin Bahajjatu ta fita daga É—akin tana alhinin irin wannan soyayya a da gani take ita da Bilal are the best couples but she has been proven wrong saboda yadda ta ga so da kishin yayan ta a idanuwan Bilkisu abin ba'a cewa komai amma ita sai ta ga kamar son da takewa yayan nata yana so ya mata yawa dan haka wun Ammi ta wuce straight dan shafa mata labarin komai.

**********
_NIGERIA_
_1:00am_

Kwance Hajiya Zeenat take tana ta juya juye ta matsu washegari yayi ta ga ɗiyar ta dan tun da suka dawo bata yi magana da ita ba most of the time tana bacci take kira shi yasa da Dr Muhammad ya sanar da ita cewa tunda komai ya tafi masu yadda ya dace ba sai sun kai one week ɗin ba ma just 4 days suka yi already kayan gyaran da Bahajjatu ta ce a karɓo mata ta aiki Bilal ɗin ya amso mata ita kanta ta gama haɗe haɗen ta da zata gyara ɗiyar tata dan an gama fixing ɗauren auren biki ne dai ba za'a yi kasancewar halin da ake ciki ba na wani shagali ko nishaɗi bane,a cikin kwanaki huɗu da suka wuce Dr Aslam yayi nasarar shawo kan iyayen sa akan batun su tafi nema mai auren Bilkisun a cewar sa suna son juna kawai halin ƙyaliyar ta ne ya sa bata iya expressing son ta but suna son junan su iyayen sa sai da suka kuma tambayar sa ko ya tabbatar tana mai so irin wanda yake mata ya ce eh shi yasa suka shirya da abokan baban nasa biyu making them three suka tafi har gidan Dr Muhammad Sulaiman dan nemawa ɗan su auren ɗiyar sa babu sanarwa babu komai hakan ma harzuƙa Hajiya Zeenat yayi har ta so magana sai prof ya hana ta ya ce shi zai yi handling nasu dan haka ƙyale ba dan ran ta ya so ba.
bayan gaisuwa ta mutunci da girmamawa prof ya tambaye su ko me ke tafe da su a nan amimin mahaifin Aslam ya mai bayanin abin da ya kawo su sai dai kash rashin sa'a amsar da ya basu ne ya sa suka kasa furta wani abin sai dai suka yi musabaha haɗe da godiya kafin su koma gida ai kuwa Aslam ya haɗu da fushin mahaifin sa ranar dan sai da ya ja mai kunne dan baya son irin hakan ya faru but ɗan sa ya janyo mai ko da Dr Aslam ya nemi sanin ko wanene mijin da aka ce an yiwa Bilkisu sai mahaifin ya sanar da shi wai ɗan gidan aminin mahaifin Bilkisun ne sunan sa Zaid sai ya ji gaban sa ya faɗi ran sa ya ɓaci dama wannan naƙasasshen har da halin da yake ciki sai ya mai shigar sauri ne wai,abin ba ƙaramin girgiza shi yayi ba dan haka ya rinƙa ƙiran layin ta amma bata ɗagawa ƙarshe ma message ta tura mai tana mai kashe mai warning akan ya fita harkar ta takaici ne ya ishe shi but bai haƙura ba ya san shi da Bilkisu are made for each other he saw it countless times in his dreams kuma an ce ai dreams can sometimes become reality shi yasa bai cire tsammani ba.
A kwanakin ne kuma Dr Hussaini ya kawowa iyayen Bilkisu ziyara haɗe da tambayar su jikin marasa lafiya suka sanar da shi halin da ake ciki har ma da dalilin su na dawowan dan amsar mai magani godiya suka mai da nuna kulawar sa kafin daga ƙarshe Hajiya Zeenat ta matsu ta tambaye sa ko ya san wani abin akan yaron da ya ma ƴaƴan su wannan abin sai ya ɗan murmusa kawai kafin ya ce da su
"Umma ai an wuce wurin tuntuni"!sai abin ya ɗaure masu kai dan ba su fahimci an wuce wurin ba sai prof ya tambaye sa dan ƙarin bayani
"Dr bamu fahimce ka ba me kake nufi da an wuce wurin"?sai ya sauke ajiyar zuciya haÉ—e da fara labarta masu abin da ya faru
"Wato bayan na dawo da su nan gida na kuma zuwa visiting na su after 2 days sai Bahajjatu ta tsare ni ta tambaye ni ko ina da masaniya akan abin da ya faru da yayan ta sai na sanar da ita komai da na sani ta min godiya muka rabu,bayan kamar kwanaki huɗu da haɗuwar mu da Bahajjatu sai yayan ta Hakim ya kawo min ziyara ta musamman a inda ya ce da ni in basa cikakken tarihin yaron da ya ma ɗanuwan sa wannan abin a iya tsawon rayuwa ta a ƙauyen koma ban yaɓa jin labarin tsagirin yaro kamar Mudan ba dan haka na sanar da shi komai sai na ga kamar ran sa ya ɓaci amma nayi calming nasa dan na san halin sa na zuciya a yadda muka rabu ya nuna min komai ya wuce ya kuma sanar da ni da zarar sun farfaɗo zai ɗaga ƙara ya shigar da hukuma cikin lamarin lafiya ƙalau muka rabu bai kuma nema na ba ban kuma ƙara jin wani abu ba a ƙauyen mai muni dangane da Mudan,kwatsam bayan tafiyar ku germany da kwanaki na sami kira daga wun mai garin koma wanda a gidan sa su Zaid suka zauna lokacin da suka tafi outreach shi ke sanar da ni wai akwai wasu yara biyu da suka tafi garin suka bi su har gida suka masu alheri daga ƙarshe suka nemi da a kai su gidan su Mudan a lokacin basu yi revealing identity ɗin su ba sai aka haɗa su da babban ɗan mai garin ya kai su har gidan su Mudan a nan ɗin ma alherin suka masu ba tare da sun sanar da su ɗin ko waye su ba sai suka nemi sanin inda shi Mudan ɗin yake akan wai sun zo ne daga birni dan taimaka mai da jari saboda ya daina halin da yake yi na rashin ji a cewar su ma daga hukumar yaƙi da zaman banza suke daga cikin garin Adamawa ai kuwa jin wannan sai mahaifiyar Mudan ta masu kwatancen inda yake zama wanda yake chan bayan gari cikin daji da taimakon babban ɗan mai gari suka yi tracing Mudan sun yi sa'a dan shi kaɗai suka samu a wurin yana shan barasa duk sauran yaran sa basu nan dan haka suka sallami ɗan mai gari haɗe da yi mai godiya har da kyauta ya tafi yana farinciki dan har yayi niyar kirawo samarin ƙauyen akan su zo ga masu yaƙi da zaman banza nan sun zo,sai da suka tabbatar ya tafi sannan Hakim ya cire suit ɗin sa ya bama Bahajjatu ta riƙe mai ya naɗe hannun rigar sa ya shiga jibgar Mudan ba ji ba gani each punch da yake kai mai gani yake kamar heaviness da ke ran sa bai raguwa dan sosai ya rinƙa kai mai punches bai bar sa ba sai da ya mai dukan da ya san dole ne ma ya kwanta jinyar sati ko bai kai wata ba da ya gama ya saka hannun sa a aljuhun sa ya fiddo da allurar kashe zafin gaɓa ya zuƙe kwalbar gabaɗayan sa ya danna ma Mudan a daidai cinyar sa inda ma bai kamata ba bayan ya mai ya kuma zuƙe wata kwalbar ya danna mai a ɗaya cinyar sa daga haka ya hankaɗa sa ya ja hannun Bahajjatu suka bar wurin a nan suka bar Mudan suka yi tafiyar su,toh according to mai gari wai da suke dawowa ne suka biya ta gidan sa suka sanar da shi cewa wai ai da suka tafi neman Mudan ɗin bayan sun gan sa sai tsagerun ƙauyen suka kawo masu hari da kyar suka gudu dan haka su zasu tafi tunda ba'a son taimakon su,sai mai gari ya ce da ni wai yayi yayi su tsaya ya kirawo masu na garin ƙauyen amma suka ce a'a su tafiya zasu yi a nan yake sanar da su labarin su Zaid wai suma da kyar suka sha da shi tsagerin da suka tafi taimaka wato Mudan su dai kawai sallamar su suka yi suka tafi ko ta kan ita Asma'un basu bi ba a cewar su zasu kai mata ziyara ta musamman bayan kwana biyu dan sanin dalilin ta na saka hannu a ta'addancin da aka yiwa ɗanuwan su"numfasawa yayi ya cigaba
"Duk wannan ƙarin bayanin daga bakin Hakim na same su dan sai da na kira sa na tambaye sa shin ko su suka aikata hakan sai ya tabbatar min da cewa eh sune kuma muddin yayan sa bai farfaɗo ba toh sai ya koma ya kasara Mudan dan yayan sa ba zai yi jinyar wahala shi kaɗai ba nikuma calming nasa kawai nayi dan dama mutanin garin na neman mai saita yaton ba'a samu ba not until when Hakim and Baha went there and deal with him,toh kun fah ji Hakim dai da goyon bayan sister ɗin su Bahajjatu sun ɗau fansar abin da aka yiwa yayan su ina ga ai ko a haka ma aka bar shi an kasara mai rayuwa dan a halin yanzu yana nan a gida an ma rasa ta yaya za'a fara da treatment ɗin sa duk jama'an ƙauyen murna suke yi yana gida ana gargajiya amma saboda ƙarfin allurai da Hakim ya mai ya sa ya sami temporal lost of function wanda sai a hankali zai warware but before then ya ji jiki gashi a buge yake bare ya ce ya gane waɗanda suka mai dukan dan haka shiru iyayen sa suka yi dan sun san sakayyar mutanin da ya cutar ne ya biyo sa".yana kaiwa nan yayi shiru ajiyar zuciya suka sauke su sun rasa me zasu yi murna ne kokuma akasin haka dan Hajiya Zeenat ta ɗau burin hukunta yaron sai dai yanzu ta sami sauƙi da relief tunɗa an ɗau masu fansa shi kuma prof godiya ya ma Dr Hussaini haɗe da miƙa mai hannu suka yi musabaha sannan suka rabu.
Al'amarin ya ba Dr Muhammad mamaki zuciyar Hakim ya kai har haka dama toh dole ne ma ya mai faÉ—a dan da a ce yaron ya rasa ran sa fa ai sai laifin su ya danne wanda yaron ne yayi masu.
Chapter 55 · 0% Book details