← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 157

Sashe 83

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Bayan kamar awa huɗu a tsakani lokacin har an fara shirin bacci dan sun gama cin abinci har sun yi sai da safe sai ya ga kawai ba zai iya ba dole ya dawo ɗakin nata ya tura yana doka mata sallama daga kwancen da take ne ta amsa mai tana mamaki dan har tayi addu'ar bacci. 
  Lighting ɗakin yayi sai ya hango ta kwance ta ɗan leƙo ta blanket ɗin tana kallon sa,rasa abin faɗi yayi sai ya faƙe da cewar
"Dama zuwa nayi dan ƙara yi maki goodnight"da fara'ar ta ce
"Alright goodnight"sai ya tsinci kansa da waving nata yana murmushi itama martanin hakan ta mayar mai,ya ja mata ƙofar haɗe da kashe hasken ɗakin.
  Komawa baccin ta tayi shi kuma ko da ya isa ɗakin sa baccin kasa ɗaukar sa yayi dan haka ya rinƙa juye juye shi bai san me ke damin sa ba sam wannan baƙon al'amari bai mai adalci ko kaɗan.
  Da ƙyar da yaya baccin ya sace sa babu labari,baccin kusan baccin wahala ne dan kan sa ya kusa bugawa tsabar takura mai da yayi da tunani marasa mafita...

*7 days later*
  _*Last night in Germany*_

  Misalin ƙarfe takwas da mintuna ashirin da biyar na dare tana kwance da ƙaramar nightie tana tsara abubuwan da zata yi a washegarin in sun koma gida saboda daga Ammi har Umman ta sun gama zuzuta mata kyawun gidan ta sun sanar da ita yadda aka tsara masu gidan very portable kuma an gyare ko ina jiran zuwar su kawai ake yi dan har abincin da za'a masu washegarin an gama harhaɗa su a row suna kamo hanya za'a fara dafa masu,duk sun saka mata kwaɗayin gidan nata a ran ta ga ƴan uwan ta sun gama kwaɗaita mata jin daɗin rayuwar da zasu yi a gidan su dan gida ne mai tsarin gaske wanda yake situated a Apo Hills birnin tarayya na ABJ..
  Juyawa tayi bisa kan gadon tana ƙara tuno rayuwar da suka yi a gidan har zuwa goodnight da suka yi da juna cikin ƴar kwanakin nan da suka zauna inuwa ɗaya.
  Wato wano irin zama ne suka yi wanda ke tattare da tsantsar kulawa da daraja juna haɗe da taka tsantsan dan gudun ɓacin ran wani a cikin su ga so da ke girgiza su a karkace for her,she is aware amma shi kam bai ɗaukar hakan a bakin komai ya fi dangana hakan da zaman taren da suka yi wa da shi ya janyo masu jituwa mai tsananin gaske..

  Ita kaɗai ta rinƙa analysis ɗin ta sam babu wani abin da ya shiga tsakanin su tun da aka ɗaura auren har kawo yau da yake masu daren ƙarshe a ƙasar,kuma abin bai dame ta ba dan ta san duk wani abin da zai rikita sa ta mai kuma ta san ya ruɗe ba kaɗan ba..

  Tana nan kwancen ta ji ya turo ƙofar ɗakin dama akwai haske a ɗakin dan haka ya sami direct access na kallon ta,ƙare ma jikin ta kallo yayi sai ya ji wani abin na taso mai from nowhere sai ya haɗiye yawu haɗe da buɗe baki da nufin gaya mata abin da ya kawo sa amma sai me?kasa magana yayi dan kayan jikin ta have tempted and seduced him already.
  Tana kallon sa gaban ta na faɗi shi kuma ya ƙi cire idanun sa daga kan ta wani mugu mugun muguwar sha'awar junan su ne ya taso masu,strong desire ne ke ɗeban su but sun kasa aiwatar da komai sai idanun su da ke aikin aiken da sukewa junan su mai ɗauke da saƙonni daban daban masu girman gaske..

_*S,Ibraheem*_
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀*
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

  *26*

  Ɗaga ƙafar sa yayi cikin ɗar ɗar da tsantsar faɗuwar gaba na fara takawa cikin halin komai ma na iya faruwa da su su biyun dan abin da ke yunƙurowa yana taso mai ba abin da kowa zai iya fassara mai bane sai shi kan sa,each step nasa na ƙara mata babban tambarin sa cikin zuciyar ta ba kaɗan ba wani maganaɗisun son sa ne ke tunzira zuciyar ta tana jin kamar ko garwashin wuta aka ajiye a gaban ta akan ta taka dan nuna son da take mai tana iya aiwatar da hakan..

  Ko da ya kawo tsakiyar ɗakin sai ya koma da baya ya kashe hasken ɗakin hakan ya janyo hankalin ta ta mayar da duban ta gare sa har da dai duhu ya mamaye ɗakin amma hasken dake penetrating labulen ɗakin daga harabar hotel ɗin sai ya sa take iya ganin sa sama sama ba sosai ba,..

  Hankalin sa a tashe yake jin kansa yake kamar wani dokin da aka shayar wa maganin dawakai sannan aka tsikara ma allurar doki dan ƙara mai ƙarfi,bai san abin da ke faruwa da body system ɗin sa ba bai gane ba hala rashin lafiyar da yayi ne ke saka sa yin abubuwa haka kamar marar cikakkiyar lafiya,within him inside him a zuciyar sa yana jin wani sashe na danne sa daga aikata abin da yake shirin aikatawa gare ta amma wani sashen da ya fi ƙarfin ɗaya sashen na nuna mai a'a kar ya bi shawarar wannan sashen dan abin da shi wannan sashen yake nuna mai shi zai kawo mai sauƙin damuwar da yake ciki..
   Wannan musun da ya kaure tsakanin sashi biyu na zuciyar sa ya haifar mai da wani sabuwar damuwar dan kan sa kamar zai buga tsabar ciwo da sara mai da yake yi,,shi kam anya hankalin sa na jikin sa kuwa?..
  Ganin ya tsaya ya kasa yin gaba ko baya gashi ya kashe mata hasken ɗakin ta ya hana ta yin saƙata kuma ba gama shirye shiryen ta tayi ba kwanciya tayi dan ta ɗan huta saboda ta sami ƙarin ƙarfin jikin ta kafin ta cigaba da aiki amma shigowar sa ya sa bata iya taɓuka komai ba sai ma sanyin jiki da ya rinƙa sauko mata ita kaɗai abin ta ta rinƙa saƙe saƙen ta akan manufar sa na shigo mata ɗaki sannan bai ce mata komai ba ya kashe mata fitilar ɗaki kai tsaye..
  Daga kwancen da take ne ta ga kamar yana da damuwa amma bai san yadda zai faɗa ba hakan ne ya sa ta laluɓo falmarar rigar baccin nata wanda yake dogo ne har ƙasa sai dai shara shara yake duk a huhhuje yake kamar rariya dan ana iya ganin jikin mutum sak ta cikin rigar baccin,gyara mahaɗar rigar tayi haɗe da mai da sumar ta gefe ɗaya sannan ta miƙe tsaye cikin takun ɗai ɗai mai rikitarwa ta nufe sa.
  Tsab yake kallon ta tun daga yadda ta laluɓo rigar ta saka har yadda ta gyara suman nata kawo ga tashin ta daga kan gadon da irin yadda take takun ta tana nufo sa abin ya shige sa ba kaɗan ba sai dai ya daure ya tsaya yana jiran ta ya ga abin da zata yi..
  Tsinkewa da lamarin ta yayi a lokacin da ya ji saukar hannayen ta masu daɗin taɓawa saman fuskar sa,duka hannayen nata biyu tayi amfani da su wun riƙo fuskar sa tana kallon fuskar nasa,babu wadataccen haske a ɗakin amma kaɗan dake reflecting ya taimaka mata wun hango damuwar da ke tattare da shi,saukar hannun ta saman fuskar sa ya saka sa lumshe idanun sa dole yana kuma jin abin da ya addabe sa game da ita na ƙara asassa mai...

  Cikin daddaɗan kalamai da son sanyaya mai rai haɗe da nuna mai muhimmancin sa ta fara yi mai magana a hankali kamar dai bata son yi
"Ka sanar da ni damuwar ka wata ƙil in baka shawarwarin da zai amfane ka dan matsalar da ka faɗawa wani har ya baka shawarar da ka sami sauƙi shine matsala mafi sauƙi a gare amma in kayi shiru sai dai damuwar ta cigaba da takura maka so did you need my comfort"?sauke mata sanyayyun idanun sa yayi yana son ganin abin da ya bambantata da wasu matan dan dai bata kasance wata ɗaya daga cikin masu jin kan duniya ba haka bata cikin matan da zaka kalla ka ce da su suna da muni but menene wannan banbancin da take da shi a tattare da ita da har take iya saka sa jin wani irin matuƙar yana tare da ita..

  Da ƙyar ma ya iya harhaɗo kalmomi masu ma'ana ya furta kamar wani wanda ya so abu aka hana sa ya rasa yadda zai nuna rashin jin daɗin sa
  "kin ga......,,kamarrr..bana jin daɗi...ina ganin kamar wani abu na dami na ban san ya zan maki bayanin abin da ke dami na ba amma na san am not alright"
  'Wow"ta furta a zuciyar ta tana mamakin rashin kula irin na Zaid ace mutum na jin wani iri a zuciyar sa amma sam ya kasa tantance me ke damin sa ana haka??
  A zarihi kuma sai ta kawar da tunanin da ta yi ɗin a fuskar ta sai ta saka murmushi mai ƙayatarwa sannan ta sauke hannun ta daga kan fuskar sa ta mayar kan hannun sa cikin salon kwantar da hankali ta jawo sa tana tafe yana biye da ita a baya har suka kawo kan gadon ta ta zaunar da shi ita kuma ta zauna saman couch dake daf da gadon,bata bar hannun sa ba yana nan riƙe cikin nata.
  Bata mai magana ba ta bar sa ya dawo daidai dan ba a hayyacin sa yake ba,tunanin ta yayi kyau dan zaman da yayi hannun sa cikin nata ya samar mai natsuwa mai yawan gaske har ma ya dawo yana jin sauƙi a ran sa yana tunanin wata ƙil dama raahin mai bashi shawara ne ya sa yake jin babu daɗi a ran sa.
Chapter 83 · 0% Book details