Sashe 99
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Adnan kuwan sai bayan magariba ya dawo daga tafiyar da ya yi, ya tarar gida ba kowa har maigadi, ransa ya ɓaci, ya duba ɗakin Abra amma bata nan, dama yana yi yan tsantsame jikinsa dan baya son ya ganta da wannan abun na jikinta.
Ya duba kaf gidan bai ganta ba, a fusace ya fito harabar gidan, zai É—au mota ya fita sai ga mai gadi ya dawo.
"Daga ina kake? Dama na É—auke ka ne dan ka dinga tafiya yawonka kana bar mini gida a buÉ—e?"
"Yi haƙuri Yallaɓai, matar gidan ce ba lafiya an nemeka a waya ba a samu ba, an kaita Asibiti"
"Asibiti, kamar yaya waye ya kai ta?".
"Ni da maƙota ne, ana ta neman layinka ance aiki za ayi mata, sun ƙi taɓata saboda ba a biya kuɗn aikin ba".
A gigice Adnan ya ce "Wane Asibitin aka kai ta?"
Dan jim mai gadin ya yi alamun son tuno sunan asibitin.
"I'm asking you Malam, Ina kuka kai mini matata? Ka tsaya kana kallo na kamar yau ka fara gani na?" Adnan ya faÉ—a cikin tsawa.
Cikin girmamawa mai gadin ya ce. "Yallaɓai sunan asibitin nake tunowa, na manta amma kamar ko BULAMA mene ne?"
"What! Me ka ce?" Adnan ya tambaya cikin ƙaraji tamkar zai fasa gidan da muryarsa.
"Asibitin Bulama." Mai gadin ya ba shi amsa.
Wani ɗan ƙaramin ihu Adnan ya saki ya nufi Motarsa cikin sauri-sauri gudu-gudu kamar sabon kamu, mara masa baya mai gadin ya yi zuciyarsa cike da mamakinsa gami da tausayinsa.
Duk da uban gudun da yake tsalawa a kan titi tamkar don shi kaÉ—ai aka yi amma gani yake kamar ba ya tafiya baya ma yake komawa. Mai gadi kuwa addu'a kawai yake yi a cikin zuciyarsa Allah ya kai su lafiya.
Suna shiga asibitin ya yi parking a tsakiyar hanya ya fito ko kashe Motar bai yi ba. Cikin sauri mai gadi ya bi bayansa. Alhaji Nura maƙocin su Abra yana ganin Adnan ya gane shi, kamar yadda shi ma Adnan din ya gane shi, duk da ba sa wata mu'amala amma suna haɗuwa time to time su gaisa. Cikin jin daɗi da farinciki ya miƙe yana faɗin. "Ranka ya daɗe sannu da zuwa, tun ɗazu....."
"Uban wa ya kawo mini mata wannan tsinannen asibitin?" Ya faÉ—a cikin cika da batsewa.
"Subhanallahi! Me ya yi zafi ranka ya daÉ—e? Ni na ce mu kawo ta nan saboda muna da file, gudun kar mu je wani asibitin mu sha wuya, ganin mawuyacin halin da mai É—akin naka take ciki?" Cewar Alhaji Nura cikin tausasa harshe.
Cikin tsantsar tashin hankali da damuwa ya ce. "Where is she? Ina Matata? Me ya same ta?" ÆŠakin da take matar Alhaji Nura ta nuna masa, bai ce komai ya nufi É—akin.
"Ikon Allah, baban Rahama lafiyar mutumin nan kuwa ƙalau? Daga taimako zai zo yana mana masifa? Mene aibun asibitin nan? Kuma ko tsayawa mu yi masa bayani bai yi ba ya yi gaba."
"Ki yi masa uzuri, kin san mu maza muna da rauni a kan ku matanmu, idan kika lura ba ya hayyacinsa, a birkice yake."
Tsaki Maman Rahama ta yi ta ce. "Ya san da hakan ya tafi ya bar ta ita kaÉ—ai a cikin gida, kuma ya san ba lafiya ce da ita ba, ni wallahi duk haushinsa ma ya cika mini zuciya." Murmushi kawai Baban Rahama ya yi bai ce komai ba.
Nurse ɗin da ta yi wa Abra allura tana bakin ɗakin da take tsaye cikin tashin hankali, don ta rasa ya za ta yi ta tsayar da jinin da take zubarwa, kuma tana tsoron ta faɗa wa wani gudun kar ta fuskanci hukunci. A haka Adnan ya ƙaraso kamar wani mayunwacin zaki yana huci, bai bi ta kanta ba ya yaye labulen ɗakin zai shiga. Saurin shan gabansa Nurse ɗin ta yi tare da faɗin. "Malam ya haka? Daga ina? Who are you?" Mugun kallon da ya watsa mata ya sa ta yin baya ba shiri ta ba shi hanya ya wuce, zuciyarta cike da matsanancin tsoro, don ba ƙaramin firgita ta yi ba da jajayen idon Adnan.
"Abra! Abra! Abra!"
Shi ne abin da Adnan ya faɗa cikin matsanancin tashin hankali, lokacin da ya yi tozali da ita kwance cikin jini babu alamar numfashi a tattare da ita. A ɗimauce ya cicciɓe ta ya yi waje da ita, har ya yi gaba ya juyo ya dubi Nurse ɗin da jikinta ke ɓari ya ce. "Wallahi wallahi idan har na rasa matata sai na yi da Shari'a da ko ma wanne shege ne ya yi sanadin mutuwar ta." Da kallo kawai Nurse ɗin ta bi shi, cikin zuciyarta tana sakin ajiyar zuciya.
Ganin yanda Adnan ya dauko Abra jini na zuba a jikinta ya sa su Maman Rahama bin bayansa hankali a tashe, suna ƙoƙarin fita daga reception Doctor Bulama ya sakko daga sama. Wani irin kallo ya bi bayansu da shi, kafin ya taɓe baki ya dubi wata Nurse cikin yamutsa fuska ya ce. "Murja ku saka a gyara gurin nan yanzu-yanzu, ko wanne mara hankalin ne ya ɗauki patient jini na zuba daga jikinta ya ɓata mana wuri oho? Sometimes wasu mutanen they behave like animals." Ya ƙarashe maganar tare da jan tsaki.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Waye yake zubar da wannan jinin haka?" Nurse Jamila da ta fito daga wani É—aki ta faÉ—i haka cikin bin wajen da kallo."
"To uwar kwakwazo, sai ki bi su ki tambaya." Bulama ya faÉ—i haka tare da yin gaba.
Cikin damuwa Jamila ta ce. "Hasbunallu'wa'ni'imal'wakil, ba dai fita aka yi da wanda ya zubar da jinin a haka ba, ba tare da an yi masa wani taimako ba? Idan jinin nasa ya ƙare kuma fa kafin su je wani asibitin? Wannan wacce irin rayuwa ce? Ba na raba ɗayan biyu kuma don ba su biya kuɗi ba ne."
"To za a yi musu abu kyauta ne, ke fa wani lokacin kina da matsala."
"Haba sister Murja, amma ko taimakon tsayar da jinin aka ba su ai an yi wani abu, don ba É—an'uwanki ba ne ko ke ce shi ya sa."
Taɓe baki Murja ta yi ta ce. "Sai ki faɗa wa mai asibitin ai." Daga haka ta yi gaba ta bar ta a gurin. Girgiza kai Jamila ta yi tare da barin gurin ita ma, zuciyarta babu daɗi.
Wani Babban Private Hospital Adnan ya kai Abra, wanda anan take awo. Suna zuwa aka karɓe ta cikin sauri aka yi emergency ward da ita. Bin bayansu Adnan ya yi, amma wani babban likita ya hana shi shiga ɗakin da aka kai ta. Ba don ya so ba ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin, amma yanda yake jin zuciyarsa tamkar ya kutsa kai ya shiga.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Allah ka tashi ƙafaɗun matata, Allah ka ba ta lafiya, Allah na roƙe ka kar ka ɗauki ranta a yanzu, Allah ka ba ta lafiya ta koma gidana da ƙafafunta in nuna mata tsantsar soyayyar da nake mata, in nemi yafiyarta a kan muzgunawar da na yi mata, Allah na tuba Allah." A fili yake maganar cikin tsantsar damuwa da nadama, wasu hawaye masu ɗumi na zuba daga idonsa. Shi kaɗai ya san abin da yake ji a cikin ransa na halin ganin halin da Abra take ciki.
"Sai haƙuri Sp, mu za mu koma gida Allah ya tashi ƙafaɗunta ya ba ta lafiya."
Ko kallon Alhaji Nura Adnan bai yi ba, saboda gani yake duk abin da ya faru shi ya ja, sanadiyyar kai Abra matsiyacin asibitin Bulama. Jiki a sanyaye Alhaji Nura ya juya suka tafi.
Duk yadda mutum yake tunanin tashin hankali Adnan yana cikin wanda ya fi shi, bai taɓa tunanin abun zai kasance masa haka ba, kuka sosai yake yi tare da surutai tamkar wani zautacce, duk wanda ya zo wucewa sai ya kalle shi, don ba shi da maraba da mahaukaci, ga jini duk ya ɓata masa kaya amma ko ajikinsa. Likitoci kusan biyar ne suka rufu a kan Abra, sun yi nasarar tsayar da jinin da take zubarwa tare da saka mata oxegen don taimaka mata gurin yin numfashi, bayan sun yi mata allurar bacci suka fito suna share zufa. A haukace Adnan ya yi kansu yana faɗin. "Doctor ya jikin nata? Ta farfaɗo? Tana numfashi? Ba ta mutu ba?" Numfashi likitan da ya kasance babba a cikinsu ya ja ya ce. "Mu je office na maka bayani."
"Office ɗin me? Ka faɗa mini halin da matata take ciki a nan, ba zan iya ɗaga ƙafata ba, ba tare da na san a halin da take ciki ba." Ya yi maganar cikin tsawa.
"Ranka ya daɗe ka yi haƙuri dai mu je, and ka kwantar da hankalinka mun yi nasarar tsayar da jinin da take zubarwa."
Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da faɗin. "Is she alive?"
"Yes."
"Alhamdulillah." Adnan ya faɗa tare da tsugunnawa cikin sauri ya yi sujjada ga Ubangiji. Girgiza kai likitan ya yi cikin tausayawa sannan ya yi gaba, maimakon Adnan ya bi bayansa sai ya shige ɗakin da Abra take. Sai da doctor ya shiga office ɗinsa sannan ya farga Adnan bai biyo shi ba, ko tantanma ba ya yi gurin Abra ya tafi. Yana da numbern Abban Adnan saboda asibitin suke zuwa kuma already ya san shi, hakan ya sa ya ɗakko wayarsa ya kira shi ya sanar masa halin da ake ciki, domin su zo ya yi musu bayanin abin da yake damun Abra, don yanayin halin firgicin da Adnan yake cikin bai zama lallai ma ya fuskanci abin da yake nufi ba, sai dai ya ƙara hargitsewa.