← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 145

Sashe 47

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune take akan ɗaya daga cikin royal chair ɗin dake parlour'n tana latsa wayarta, ta ci kwalliya cikin wani tsadadden farin less, idan ba faɗa maka aka yi ba za ka ce ta haifi Meenal ba saboda gayunta. Ɗaya daga cikin masu aikin gidan mai suna Asabe ce ta fito daga kitchen hannunta riƙe da plate, cikin sauri take tafiya har ta ƙaraso ta zube a gaban Hajiya.

"Ranki ya daɗe Barka da yamma, ga wainar nan na kammala." Asabe ta yi maganar cikin ƙanƙan da kai.

Wani wulaƙantaccen kallo ta ɗago ta wurga mata, cikin izza tamkar wata sarauniya ta ce. "Ubanki na ce ki dafa ne tun ɗazu ba ki gama ba sai yanzu?" Cikin kyarmar jiki Asabe ta ce. "Ki yi hak'uri Hajiya Saudat."

"Dalla Malama tashi daga gabana, kafin ki kashe ni da warin ƙashi, Idiot kawai." Ta faɗa mata haka cikin tsawa.

Ko gama rufe baki ba ta yi ba Asabe ta miƙe jiki a saɓule ta bar parlour'n.

Ajiye wayar ta yi ta miƙe ta ɗauki plate ɗin ta haye upstairs. Meenal tana kwance akan gadonta na alfarma suna chatting da Usman Mahaifiyarta ta shigo ɗakin. Ɓata fuska Meenal ta yi ta ce. "Mommy sai yanzu?"

"Sorry Daughter, tashi ki ci, ke ma da tsifa kike wallahi, duk abubuwan da ke gidan nan amma ki ce sai wata wainar fulawa za ki ci?"

A shagwaɓe ta ce. "Ita kawai nake sha'awa ne Momy."

"Ai gata nan." Hajiya ta faɗi haka tana ajiye plate ɗin akan bedside drawer, sannan ta juya ta fita ta koma ƙasa.

Zamanta babu jimawa wani mai aiki a gidan ya shigo parlour'n, cikin respect ya gaishe ta, a wulaƙance ta amsa masa cikin yatsina fuska, sanar mata ya yi tana da baƙi.

"Maza ne ko Mata?" Ta tambaya kamar ba ta san magana.

"Mata ne." Ya amsa mata.

Da hannu ta yi masa alamar ya shigo da su.

Idanunta akan ƙofa bayan fitar Ilya ta ga waɗanda ba ta yi tsammani ba sun shigo, miƙewa tsaye ta yi da sauri cikin shouting ta ce. "What! Su waye waɗannan a cikin parlour na?" Iliya da ya yi musu jagora ya ce. "Su ne baƙin Hajiy...." Bai ƙarasa ba ta dakatar da shi cikin tsawa da faɗin. "Shut up! Wannan abubuwan za ka shigo mini da su har cikin parlour? Ubanwa ma ya ba su damar shigowa gidan nan har suka ƙetare main Parlor su shigo mini nan?"

Kansa a ƙasa yana sosa kai ya ce. "Am Haji..."

"Hajiya me? ashe ba ka da hankali Ilya ban sani ba? Tunda kake a gidan nan ka taɓa ganin mutane irin waɗannan sun zo gurina? Ko a bakin gate ɗin gidana ka taɓa ganin talaka yana shawagi?"

Shiru Ilya ya yi bai ce komai ba, ƙwafa ta yi tana ƙara bin tsoffin matan da kallo cikin yatsina fuska kamar ta ga kashi. Ɗaya daga cikin Matan ne ta tsuguna akan gwiwoyinta cikin kuka ta ce. "Hajiya dan Allah ki yi haƙuri, neman taimako muka zo, ki taimaka mana kamar yadda Ubangiji ya taimake ki." Kallon sama da ƙasa ta yi mata cikin raini ta ce. "Nan ba gidauniyar taimako ba ne Malama, don haka ku tattara tsummokaran ƙafafuwanku ku bar mini parlour, kafin ku gama cika shi da wari da tsami. Mutane sai mutuwar zuciya, ba za ku fita ku nema ba sai yawon maula." Mtss ta ja tsaki tare da ɗaukar wayoyinta. Cikin gargaɗi ta kalli Ilya ta ce. "Ka fitar mini da su daga parlour kamar yadda ka shigo da su, ka jirayi hukunci kuma na shigo mini da matsiyata cikin gida da ka yi." Ba ta jira amsar shi ba ta shiga ƙwala kiran sunan Asabe da sauran abokan aikinta, jiki na rawa suka fito daga wani ɗaki dake cikin parlour'n, umarnin sake tsaftace parlour'n gami da saka masa turare ta ba su sannan ta haye sama, cikin izza da ɗagawa tamkar wata matar Shugaban ƙasa.

Baby ce ta kalli Ihsan, da har zuwa wannan lokacin, tana kwance akan gado.
A É—an hasale Baby tace "waike Ihsan meye haka ne? Ki tashi ki shirya Abuja zamu tafi yanzun nan, cin uban wancan É—an iskan".

Ihsan ta yamutsa fuska tace "Wallahi Baby, haryanzu jikina na yi mini ciwo sosai, kin san na zubar da jini sosai".

"To ai shiyasa dan ki fanshe wahalar ki, ya sa nace ku shirya mu tafi Abuja, bana jin Alhajin Janna Sosai, yana da sakin hannu, Amma shi wannan sojan nake son ki wankar mana, tunda mutumin banza ne shi, ga rowar tsiya, Wallahi ko mu É—au tsiraicinsa muyi blackmailing É—insa".

Ihsan tace "Wallahi tsoro nake ji Baby"

"Au tsoro, kwanta zaki ga tsoro, dalla ki tashi ki shirya ba zaki sha wannan wahalar a banza ba, kuma idan muka je kar ki gaya masa an cire cikin nan kice kuÉ—i zai baki kije ki cire"

Haka Baby ta sata a gaba, ta tashi tai wanka ta shirya, su uku suka hau motar Baby, suka nufi garin Abuja.

Major ya kasa ya tsare, akan Lallai a tsananta bincike a gano, dalilin mutuwar sojojin nan da ake tuhumar yadda hatsaniya ta ɓarke, har sukai faɗa a tsakaninsu, amma abubuwa gaba ɗaya sun cakuɗe, an hargitsa abubuwan, yadda Binciken zai bada wahala, wanda duk plan ɗin General Ibrahim ne.

Ba tare da an samo bakin zaren ba, a dole Abbi ya shirya komawa gida.

Washegari ya kama Saturday, around 3pm bayan Abra ta gama ayyukan gida tana kwance akan kujera 3 seater tana browsing wani assignment da aka ba su a wayarta, Na'ima da Khamal suka shigo cikin parlour'n. Idanun Abra akan wayarta ta amsa musu sallamar da suka yi tare da gaishe su, saboda hankalinta gaba-d'aya yana kan assignment É—in, so take ta yi ta gama dan yana da wahala, gashi kuma da yawa.

Dinning area su Na'ima suka ƙarasa, Khamal ya zauna ta fara zuba masa lafiyayyen abincin da Abra ta girka. Bayan ta gama ta saka masa spoon ta saci kallon Abra ta ce. "Man, ban san me yake damun Daughter ba, yanzu ta koma always busy with her phone." Cikin rashin damuwa Khamal ya ce. "Kin manta yanzu yar jami'a ce ita? Ai dole sai tana fama da browsing da karatu kodayaushe."

"To me yasa Salman shi ba ya haka?" Ta tambaye shi tare da zama a kusa da shi."

"Ta fi shi serious ne."

Cikin takaicin abun da Khamal ya faÉ—a ta ce. "Gaskiya ban yarda ba, yarona ma babu lefi, abun da na fi tunani kawai ita da akwai abun da take yi a wayar bayan karatun."

Khamal ya dakata da cin abincin da yake ya ce. "Ban fahimce ki ba, me kike nufi?" Duk da Na'ima ta tsorata da yanda ya tsare gida amma ta dake zuciyarta ta ce. "Ni nake zaune da yaran nan kodayaushe a gida, kuma duk wani motsin su a kan idona yake, ta haka na gane yawan amfani da waya da Abra take yi, koda yaushe waya tana hannunta, har cikin dare idan na je duba ta ina hango hasken screen ta cikin blanket É—inta, alamun ba bacci take ba waya take latsawa. Yanzu ma ka lura fa da muka shigo, ko É—auke idonta daga kan wayar ba ta yi ba."

"Shi ne me? Ba ki ga papers ɗin dake gabanta ba, may be tana discussing something important related to her study ne, wanda yake buƙatar full attention ɗinta akai."

Cikin baƙin cikin rashin sanin haɗin kai Na'ima ta ce. "Haka ne, ni ma ba wani abun nake nufi ba, kawai ina so a bincika ne in ma wanin abun ne a yiwa tufkar hanci tun wuri."

"Babu ma komai, na san tarbiyyar da na bawa yarana, na kuma yarda da su, dan haka ki daina irin wannan tunanikan, just pray for them, Allah ya kare mana su daga aikata dukkan wani abu mara kyau."

Cikin yaƙe ta ce. "Ameen Mijina." Khamal ya cigaba da cin abincinsa, yayin da Na'ima ta shiga saƙe_saƙen yanda za ta ƙara ɓullo masa, akan makircin da take son ƙulla wa Abra. Ba ƙaramin baƙin ciki ta ji ba a yanzu da ya ƙi bawa maganarta muhimmanci, ta so ya karɓi wayar ya ga abubuwan da ta tura a ciki, ba tare da ita kanta Abran ta san da su ba, ta san idan ya gani kashe Abra ne kawai ba zai yi ba, saboda yanda ta san shi da takatsantsan da tarbiyya akan Ƴaƴansa.

Cikin kwanikan nan da suka wuce mai turawa Abra text na love messages bai fasa ba, duk da ba kowanne take reply ba, saboda ta yi ta yi ya faɗa mata wane ne shi ko ya tura mata pics ɗinsa amma ya ƙi. Sai dai ta rasa me ya sa idan ta ga message ɗinsa take jin nishaɗi a cikin zuciyarta, ba ta gajiya da karanta messages ɗin nasa ko kaɗan, har ta haddace lokutan da yake tura mata, idan ya ƙara mintuna bai turo ba ta dinga duba wayarta kenan, tana jin vibrate za ta duba da sauri, idan shi ne ta buɗe ta karanta cikin sauri, idan kuma Company ne ta yi tsaki ta ajiye wayar.

Yau Monday, misalin ƙarfe bakwai da rabi Abra ce tsaye a gaban mudubin ɗakinta tana gyara rolling ɗin mayafin abayar dake yane a kanta. Wayarta dake kan mudubin ta yi vibrate alamar shigowar saƙo. Ɗauka ta yi ta duba, ganin Mr unknown ya sa ta buɗe da sauri ta fara karantawa.

"God Morning My Angel, da fatan kin tashi lafiya? Na san yanzu kina shirin tafiya school, Allah ya kiyaye hanya ya ba da sa'a, have a nice day Princess!"

Murmushi ta yi a saman leɓɓenta tare da lumshe ido ta buɗe, zuciyarta cike da son ganin Mr unknown ɗinta. "Yaushe zan gan ka? A ina zan gan ka? Mutum ne kai ko Aljan da kake sanin duk wani moment ɗina?" Ta tambayi kanta a hankali tana kallon fuskarta ta cikin mudubi, still tana murmurshi.

"Angel!"

Muryar Salman da ba ta san time É—in da ya shigo É—akin ba ta doki kunnenta.

"Na'am Faris." Ta amsa tare kallon shi.

Wani irin kallo yake bin ta da shi bai ce komai ba.
Chapter 47 · 0% Book details