Sashe 86
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
LITTAFIN DARE DA DUHU, na kuÉ—i ne biya 300 ta wannan acct É—in 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne zaka biya 500 kai Mgn ta wannan number. 09047871750/08081012143
[10/20, 7:45 PM] Abk: Da sauri Salman ya shiga girgiza mata kai, alamar kada ta ƙaraso wajansa domin ya san abin da zai faru idan ta zo. Ita ta haramta a garesa kamar yadda ya haramta a gareta. Da sauri ya yi baya ganin yadda ta yo kansa gadan-gadan, hawaye na bin fuskarta ga wani irin kuka da take tamkar wacce akai wa mutuwa.
Juyawa ya yi da sauri ba tare daya shirya ba da nufin barin parlourn yama fita daga cikin gidan baki ɗaya. Ƙyakkyawar rungomar da Abra tayi masa ta baya ita tayi sanadiyar ɗaukewar wutar kan Salman, cak ya tsaya zuciyarsa na bugawa da ƙarfin gaske, shi kansa ya san ya azabtu da rashin Yayar tasa, amma ba shi da iko da ita a yanzu mummunar ƙaddara tai musu shamaki da juna.
Gaba ɗaya ya kasa motsawa sbd yadda Abra ta ƙankamesa ta baya hannunta ɗaya a ƙirjinsa ɗaya kuma ta riƙe ƙugunsa dashi, wani irin kuka take wanda yake ratsa zuciyar Salman, saurare ɗaya yayiwa kukan yasan cewa bawai Iya na farin cikin ganinsa bane, akwai abin da yake faruwa a ƙasa.
Idanunsa da sukai jaa ya buɗe a hankali cikin nutsuwa ya saka hannunsa tare da zame hannayenta dake rungome da jikinsa da ƙyar. Juyawa yai ya fuskance ta ƙanta a ƙasa yana kallon yadda take kuka kamar zata haɗiyi zuciya. Tun daga sama har ƙasa yabi jikinta da kallo babu abin da ya bashi tsoro sai ramar da yaga tayi ba haka ya tafi yabar Angel ɗinsa ba.
Inda take ya matsa tare da sanya hannunsa duk biyun ya tallafo haɓarta fuskarta ta samu gurbi a cikin hannunsa, kasa magana ya yi sai binta da idanu kawai da yake, Eyeballs to Eyeballs suke kallo juna, Abra na shassheƙa ta ce.
"Faris"
Kasa amsata ya yi yana son tantance muryar data kirasa da ita, hannunsa ya zame kaÉ—an yana mai dashi cikin Aljihu a nutse ya É—aga kansa sama ya fara bin parlourn da kallo kamar daga sama taji ya ce.
"Kin rame, kamar ba Angel tawa mai son girman nan ba" kwaɓe fuska tayi tare da matsawa kusa dashi ta shiga dukan ƙirjinsa tana sakin kuka tare da faɗin.
"Why did you go and leave me? Kai ne wanda nake gani naji daɗi, kai ne walwalata, farin cikina, me ne yasa zaka barni a lokacin da nake buƙatar ka? Why Why Why Faris" ta faɗa tana sakin raunataccen kuka while tana ƙara dukan ƙirjinsa da dukkan ƙarfin ta. Jajayen idanunsa ya lumshe yana jin yadda take dukansa kamar wanda yayi mata babban laifin nan, baya ita ce wacce ta bashi lasisi da damar tafiya ya barta,ita ta zaɓi waninsa ta kasa fahimtar feelings ɗinsa a gareta, ta gagara gane cewa so da ƙaunar da yake mata ba iya na ƴan uwa bane, so ne irin na masoya wanda zai kai matakin Mata da Miji.
Jin kukanta yake har ƙasan zuciyarsa, zafin da zuciyarsa ke masa a yanzu ya tabbatar yafi wanda zuciyar take mata, ji yake kamar ana ɗiga masa ruwan dalma a zuciyarsa. Ganin yadda take kukan har numfashinta ya fara sama alamar zata sume masa, cikin rashin abin yi da mafita yabi umarni da kuma ragamar zuciyarsa ya jawota jikinsa tare da yi mata masauƙi a jikinsa ya rufe ta ruf da hannayensa. Kamar tana jira tai holding nasa back sai kuka take tana ƙankamesa tare da faɗin.
"Stay with me, don't leave me again. I am happy when you are near me. Idan zaka tafi ka tafi dani kaji"
Shiru Salman ya yi mata, har lokacin yana riƙe da ita a jikinsa zuciyarsa kamar zata fito waje haka nan ya keji.
"Faris.." ta faɗa tana ɗaga kanta tare da kallon fuskarsa wacce tayi jaa sosai. "Kayi magana mana ɗan ƙanina" ta ƙare maganar tana Murmushi while hawaye na zubu mata ta rasa yadda zatai she can't believe wai Faris ne tsaye a gabanta. Hannunta ta miƙa taja dogun hancinsa tana faɗin "Say sometimes yaushe ka zo? Waya faɗa maka gidana" zameta yayi daga jikinsa ya tsaya kamar an dasa shi ya ce.
"Banji daɗin ganinki haka ba, Abra." Kanta ta sunkuyar ƙasa a karo na farko taji kamar ta faɗawa wani halin da take ciki musamman yanzu da take ganin Salman a gabanta. Amma idan ta tuna gargaɗin Adnan a gareta, sai ta ji tsoro da fargaba ya kamata, kuma tayi tuni ga Sirrin Aure tsakanin ma'aurata, sai taji duk jikinta yayi sanyi. Shiru ta yiwa Salman ba tare da ta ce komai ba.
"Is something bad happened to you? Look Angel kasa jurewa da ganinki a cikin mafarkina da nayi ne ya sanya na biyo jirgi na tawo ba tare da sanin makarantar da nake ba,kina so zuciyar Faris É—inki ta buga ne?"
Girgiza masa kai tayi muryarta na rawa tace "Ka zauna na kawo maka ruwa, me zaka ci?" "Banzo dan naci abincin gidan mijinki ba, I'm here sbd sanin halin da kike ciki, da kuma dalilin da yasa kike addabata a cikin barcina" shiru tayi masa hawaye wani yana bin wani wata tsawa ya buga ya ce "Talk Abra, Talk" dugun numfashi taja tana ɗaga kai da sauri ya ƙaraso inda take tsaye ya kama hannunta zuwa kan kujera ya zaunar da ita.
Juyawa yayi da sauri kuma ya nufi wajan deep freezer yaje ya buɗe, ruwa mai sanyi ya ɗauka ya dawo inda take zaune, a lokacin har idanunta ya fara lumshe a gefenta ya zauna ya kama Fuskarta tare da bata ruwan, tana sha yana ɗan bubbuga bayanta tare da shafa kanta. Ajjiyar zuciya mai ƙarfi ta saki kanta ta ɗora saman cinyarsa ta ce.
"Zuciyata babu daɗi Faris, komai ya lalace duniya ta juya min baya nasan da kana kusa dani da hakan bai faru ba, bana da mafita bana da mataimaki, bana da ikon faɗin abin da yake raina, Ubangiji ne zai min maganin komai ka tayani da addu'a...," Kukan da yaci ƙarfinta ne yasa ta kasa ƙarasa abin da tai niyya. Shiru yayi mata har lokacin yana shafa kanta ganin ta fara dawowa hayyacinta ya sa ya ce.
"Kinci Abinci?" Kai ta girgiza masa ya ce "to É—agani, kin wani haye min cinya" murmushi tayi tana faÉ—in.
"Wallahi bacci ma nake shirin yi, naji cinyar ta ƙara laushi"
"Ko?" Ta miƙe tsaye tana faɗin "Sure" sai a lokacin ta shiga kallonsa maroon ɗin voyel ne jikinsa mai manyan zane amma shara shara haka Voyel ɗin yake, hatta farar singlet ɗinsa ana gani ya ƙara fari tas dashi, ga ƙirjinsa daya buɗe fuskarsa ta fara cika da gemu da saje, sai jajayen laɓɓansa da suke haske. Zaka iya tunanin yayi shekaru ashirin da biyar ko da bakwai haka.
Marairaice mata fuska ya yi ya ce "Yaya" dry tai tana watsa hannunta ta ce "You have changed totally wallahi mai kake ci acan China?"
"Tunanin ki ke ƙara min lafiya" idanunta a kansa ta kasa magana yana ɗago kai suka haɗa idanu ya zaro mata idanunsa ya ce "Ki je ki kawo Abinci Angel stop looking at me haka nan, kada ki fara ganin munina tun ina kyau a idanunki"
"Zoka ta yani" Waro idanu ya yi waje ya ce "Wa? Ni Salman Khamal Khamis? Jeki kawai Yaya ina jiran ki" "haba mana Faris yaushe rabon da muyi girki tare" girgiza kai kawai yayi ya ce. "Yaya gsky ba zan iya ba"
Turo baki tayi ta juya zuwa kitchen ɗin ajjiyar zuciya ya sauke sai a lokacin hawayen da suke maƙale a idanunsa suka silalo a hankali, da sauri ya sa hannunsa ya goge tare da Miƙewa yabi bayanta.
Duk abin da take da Idanu kawai yake binta, yana nan tsaye da ƙyar ta samu ya yanka mata albasa da carrot. Babu jimawa ta kammala haɗa fried rice with chicken kabab. A plate ɗaya ta zuba ta saka 2 spoons, ya rigata tafiya a zaune ta samesa kan kujera ta ce.
"Baka gaya min ya Mamina take ba da Abbi, Ammi, Granny i so much missing them wallahi" shi dai bai ce komai ba ta ce.
"Ga abinci" "kefa?" Girgiza kai tayi ta ce "bana ci" ƙuri yayi mata da ido kafin ya ɗauki spoon yana sakkowa ƙasa, A nutse yake bata abincin tana ci harta ƙoshi . Zamewa tayi ta ɗora kanta a cinyarsa idanunta a sama shi dai bai motsa sai girgiza ƙafarsa da yake, hakan yai wa Abra daɗi domin sai ya zamana kamar rarrashinta yake bai aune ba yaji saukar numfashinta bacci ya ɗauke ta.
Tunani Salman ya fara, game da sauyin Abra amma ya kasa gane gaskiyar al'amarin, sai ya alaƙanta hakan da sabuwar rayuwar data samu kanta ciki, da kuma tafiyar da ya yi barta wannan dalilin sune suka sauyata, ya san tana son mijinta tana kuma farin ciki da aurensa. Babu wanda ya san da batun zuwansa Nigeria, domin shi kansa bai yi tunanin cewa zai iya zuwa cikin gaggawa haka ba, Khairy ce ta bashi Information na gidan Abra, kuma yaci sa'a yana da aboki a Kaduna, yana zuwa kuma bai sha Wahala wajan maigadin gidan ba, har lokacin da ya nufi ƙofar parlourn bai yi tunanin zai sanya Abra acikin ƙwayar idanunsa ba, sai gashi yana buɗe ƙofar ta sadashi yayar tasa. Numfashi ya sauke yana kallon yadda take bacci ta ƙanƙame hannunsa a ƙirjinta, zuciyarta na ɗan bugawa a hankali. "Zaki dawo gareni, zaki zama mallakina Insha Allah yaya" kwanciya ya fara tunanin gyara mata.
Yana ƙoƙarin ɗaukanta zuwa saman kejera yaji ance "Well-done Salman Khamal Khamis Well-done masoyi na ƙwarai" ko ba a faɗawa Salman ba ya san Sp Adnan Aliyu Matawalle ne. Murmushi ya yi a hankali ya ɗauki Abra ya kwantar saman Kujera yana duba yadda baccin nata ya yi nisa, hannunsa ya zuba cikin Aljihu idanunsa akan Adnan ba tare da ya ce komai ba.