← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 145

Sashe 84

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zaune ya samu Adnan a gaban Likitan shi ma ya ja Kujera ya zauna. Shiru sukai tare da zaman jiran jin ta bakin Likitan.
Gyara zama Dr ya yi yana duban su, kafin ya zame farin Photochromic glasses É—in idanunsa. Cikin nutsuwa ya du bi Adnan ya ce.

"Before even bringing her to the hospital, what happened to her at home?"

Ganin yadda Adnan ya rikice kamar ma baya cikin hankalinsa ya sa Abbi faÉ—awa Dr cewa faÉ—uwa tayi.

"Haka kawai ta faÉ—i, or something was said to her that upset her. or something bad she heard or saw?"

"It's almost like that Doctor" Abbi ya faɗa a taƙaice, domin baya son maganar tai tsayi har ya kai ga an maimaita zancan da kunnuwansa a yanzu basa buƙatar sake jinsa. Yana son Abra ta kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Dr bai damu da sanin abin da ya sanya Abra cikin halin suma ba, ya gyara zama in a serious tone ya ce.
"She is having breathing problems, wanda duk sanda ta samu rikicewa ko wani abu ya sameta wanda zuciyarta ta kasa ɗauka zata iya suma a ko wanne hali take ciki. This is the reason why her lungs started having problems. Munyi ƙoƙarin Seeing that she regained consciousness, Allhamdulillah yanzu bacci take amma sai an dinga ki ya ye wa, domin wannan Matsalar babba ce banda Ubangiji ya taƙaita".

"Thank you Doctor"

"It's my responsibility. Allah ya bata lafiya" cewar Dr yana kallon Abbi da ya yi maganar.

"Doctor I can see her now" "why not?" Adnan ya jinjina kai yana Miƙewa tsaye tare da faɗin.

"Thank you"
Kai tsaye Room da aka kwantar da ita ya nufa, a hankali ya murɗa handle ɗin without making any sounds wanda zai iya damunta, duk tunaninsa Abbi na biye da shi. Tsaye yayi yana ƙare mata kallo tare da bin Oxcgyen ɗin dake maƙale da ita wacce take taimaka mata wajan yin numfashi.

Taɓe bakinsa ya yi, irin ko a ƙafarsa ɗin nan, kafin ya Ƙarasa gefenta ya zauna yana kallon yadda take sauke numfashi gaba ɗaya ta faɗa ta zama wata kala tamkar ba Abra Khamal Khamis. Sai ka ɗauka ta shekara tana jinya, lallai anyi gaskiya da akace damuwa itace hanya ta farko wajan latata mutum.

There is no compassion or compassion in Adnan's heart. Wutar ɗaukan fansa ce kawai ke ƙara ruruwa a cikin zuciyarsa, tare da tunanin duk wata hanya da zaibi ya datse ƙaddarar da zata sada Abra da Real father ɗinta. Baya so baya kuma ƙaunar ganin haka, Imma mahaifin Abra zai ganta sai dai cikin makara yayin jana'izar ta. Ko kuma ita ta gan shi yayin tasa jana'izar. Zuciyarsa ta kasa jure abin da aka aikata a garesa, da ace zai yafe da tuni ya yafe amma wannan ba ƙaddara bace zallar son zuciya ne bama za'a haɗasa da kuskure ba.

Ajjiyar zuciya ya sauke yana jan idanunsa tare da rufewa zuciyarsa nayi masa nauyi tamkar yanzu ne abin da akai masa yake faruwa. Baya jin koda Abra zata mutu ta dawo ƙarƙashin inuwar auren shi zai yafe wannan laifin dole sai ya ɗauki fansa. Domin da wutar ɗaukan fansa ya RAYU.

China.
Mirginawa ya yi daga kwancan da ya ke. Idanunsa dake a lumshe ya buɗe yana ƙara kallon A.c. dake ɗakin, gently kuma ya juyar da kansa idanunsa ya sauka akan makeken photon sanyin idaniyarsa, wanda ya kai aka buɗa masa shi ya zama babba. Tashi ya yi daga kwanciyar da yake ya nufi inda ya ajjiye photon daidai wajan ya tsuguna tare da miƙa hannunsa ya ɗauki photon, idan ba gizo idanunsa suke masa ba sai yaga photon kamar ya sauya idanunta sai sheƙi suke tamkar zasu zub da ƙwalla.

A nutse ya shafi fuskarta idanunsa akan ƙaramin bakinta cikin muryarsa mai nutsuwa da kamala wacce girma da samartaka suka ƙara kamata ya ce.

"Yaya"
Ya faɗa yana kallon Fuskarta sai kuma ya ce "Akwai matsala yaya, na kasa samun nutsuwa me ya sa kike zuwa cikin baccina kina kiran sunana tare da yi min kuka? Why Angel ko akwai abin da ya ke damunki? Bai kamata ki damu ba, kina tare da wanda kike so kika zaɓa matsayin abokin Rayuwar ki. Uba ga yaranki kin samu abin da ki ke so. Nima kuma zan maki tawa rantsuwar yanzu"

Miƙewa tsaye ya yi hannunsa zube cikin Aljihu gashin ƙirjinsa ya kwantar lub sai sheƙi yake a saman farar fatarsa abin ka da farin bafulatani. Da ɗan sauri-sauri yake duba cikin wata box har ya samu sabuwar reza jikinsa na rawa ya ɗauki reza ɗin tare da tsayawa akan photon Abra ya ce.

"I, Salman Khamal Khamis, promise you if I don't find you as my wife... Ni ba É—an halak bane Abra" yana faÉ—in hakan ya tsaga tafin hannunsa da rezar nan ta ke jini ya fara zuba, Murmushi ya yi yana zubawa photonta ido ganin jinin da ke zuba a jikinsa yana sauka a photon ya ce.

"Ban damu da shekara nawa za kuyi tare ba, ban damu da yaran da zaku haifa tare ba, ban damu da girma ko tsofan da zaki kafin na dawo gareki ba, ke nake buƙata a cikin rayuwata. IDAN BA KE babu ni Abra, I love You, I love, I love Abra Khamal Khamis" Yana faɗin haka ya sake tsaga hannunsa da rezar ga wani gumin azaba dake tsastsafo masa a tsakiyar goshinsa. Kamar yana magana da photon nata ya ce "Yaya, I promise to love you unconditionally.
Darling, you are the love of my life, I promise never to break your heart as it will also break mine. I love you so much. I promise to be with you forever.
Honey, I know life has many challenges, but I promise to be dedicated to you. For better or worse I will always stand by your side until death separates us"

A hankali wasu hawaye Masu zafi suka shiga fitowa daga cikin idanunsa, amma a hakan bai sare ba ya ƙara sakin Murmushi wanda ya fidda zallar kyansa cikin wata kalar Murya wacce babu tsoro ko rauni a cikinta ya ce.

"Every day when I wake up, the first thing that comes to my mind is you. You know, how only a few things in this world make you happy with the fact that they are there and make your life great. You are one of those very few things. Thank you for being my destiny.
You are my destiny. You are my dream come true. I can’t imagine myself with anyone else. I love you and just want to thank you for every single thing you do. You are the reason why I live, the air that I breathe and the love of my life!Wherever you go, whatever you do, I want you to know that you are my destiny"

Ƙirjinsa ya buɗe jikinsa na rawa na tsananin azaba amma a haka ya rubuta alphabet letter na A. Nan take jini ya fara zuba kamar daga sama wani abokinsa mai suna Sunday ya shigo ganin Salman cikin wannan hali ya sa Sunday faɗin.

"What happened to you Friend?" Shiru Salmanun-faris ya yi yana kifa kansa a jikin photon Abra. While jini na zuba daga ƙirjinsa zuwa hannunsa. Sunday ya matsa kusa da Salman ya ce.

"你怎么了?你的情况呢? Nǐ zěnmeliǎo? Nǐ de qíngkuàng ne?" Ma'ana "Mene ya sameka? Kalli halin da kake ciki fa?".

Salman was speechless, hannunsa ɗaya dafe da ƙirjinsa ɗayan kuma ya rungome photon Abra a jikinsa idanuna rufe. Ganin Salman yaƙi magana ya sanya Sunday matsawa tare da ƙoƙarin taɓa Salman a hargitse cikin zafin zuciya ya ce.

"Don't torch me, i Said get out of my room".

Abbi da Adnan na zaune a gefen gadon da aka kwantar da Abra, har lokacin bata ta shi ba. Abbi da hankalinsa ke kanta a hankali yaga tana motsa bakinta kamar mai yin magana, sai hannunta da yake ɗan fisga, ganin yadda bakin ke motsawa sosai ya sanya Abbi matsawa kusa da ita, tare da ranƙwafawa daidai saitin bakinta. Ga mmakinsa babu abin da take cewa Maybe zafin ciwo yasa take haka.

"Innalillahi Faris, Faris mene wannan, mu gani" da sauri wannan kalaman suke fita daga cikin bakinta a kuma bayyane, Adnan dake zaune ya gyara zama yana binta da masifaffun idanunsa, wanda kuma zallar kallo ne na taƙaici musamman ganin yadda Abbi yake da riƙeta shi ba muharraminta ba, ga wannan ban zan Salman da take kira ba dare ba rana ba kullum bakinta cikin ambaton sunansa yake.

Kama hannunta Abbi ya yi cikin kulawa ya ce "Sweetheart kin farka?" A hankali ta buÉ—e idanunta bakinta har lokacin yana motsawa. Kallon Abbi ta shiga yi wani Irin kallo mai kama dana tuhuma, Murmushi yayi yace "Sannu Sweetheart sannu Kinji" kafin tai magana Adnan ya tashi da sauri ya zo inda take gaba É—aya kan gadon ya hau ya ce.

"Naji tsoro Angel, i can't life without you ki daina suma irin haka please Angel zuciyata ba zata ɗauka ba" ya ƙare maganar yana ɗora kanta a kan cinyarsa, ya shiga shafa kanta. Da ace tana da ƙwarin barin jikinsa tabbas da tayi haka domin babu abin da zai sanya ga Abbinta wannan mugun azzalumin ya riƙe tare da nuna mata soyayyar ƙarya. Maganganun Abbi ta tuna wanda ya sanya ta fara zubar da hawaye ba tare data shirya ba. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wacce kalar rana yau ta zame mini? wacce rayuwa zan fuskanta a nan gaba, mene aikata a gare su da suka zaɓi haihuwata ta wannan sigar tare da yardani? Laifina ne, ni nace su aikata abin da suka aikata su waye iyayena mene yasa za suyi mini haka wayyo Allah" Wani irin raunataccen kuka Abra ta saki hadda shassheƙa kamar numfashinta zai bar jikinta,da Yadda take ji a cikin zuciyarta gwara ace bata zo duniya baki ɗaya ko kuma aci gaba da ɓoye mata Asalinta.
Chapter 84 · 0% Book details