← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 145

Sashe 50

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ta sauke tare da zare wayar daga kunnenta. sai ta tsinci zuciyarta da blaming kanta, kamar ba ta kyauta masa ba da ta yi shiru, to amma me za ta ce masa? Ita fa jinta take duk a takure, ga wani kwarjinin da yake yi mata, ga kunyar shi da take ji duk ita kaÉ—ai.

_Adnan_

ta ambaci sunansa a cikin zuciyarta, sunan ya yi mata daɗi ba kaɗan ba. Lumshe idanunta ta yi tana hango yanda yake magana cikin nutsuwa yana motsa ƙananun lips ɗinsa kamar ba ya son maganar ko wanda aka yiwa dole. Murmushi ne ya kufce mata ba tare da shirya yin sa ba, saboda tuno kyawawan fararen idanuwansa da yake tsare ta da su.

"Angel!"

Salman ya faɗa da ɗan ƙarfi lokacin da ya shigo ɗakin yana ƙare mata kallo. Da sauri ta buɗe idonta cikin ƙoƙarin daidaita nutsuwarta.

"Me ya sa kika taho ba tare da kin sanar mini ba?"

Kalar tausayi ta yi ta ce. "I'm sorry bloody, bayan na baro class É—inku na ji ina son shiga toilet, kuma ka san i can't use toilet É—in school, that is why na taho gida." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Shikenan, amma kin É—aga mini hankali sosai, kin san irin neman da na yi miki kuwa?"

"Sorry sweet Bro, ka je ka huta bari na tashi na haÉ—a maka delicious yanzun nan." Murmushi ya yi ya ce. "Baby girl, shi ne kika zo kika ba ni kunya a class."

Cikin shagwaɓa ta ce. "Kunyar me kuma Faris?"

"Ba ta komai, ni abun da ya fi ba ni haushi yanda ake ta tanka ki, bayan mun fito harda masu cewa in ba su contact ɗinki wai kin burge su." Ya ƙarashe zancen tare da jan tsaki. Murmushi kawai ta yi, ta rasa me ya sa Salman yake mata haka? Ba ya so ya ga maza suna kallon ta ko su yi mata magana, yanzu zai shiga ɓaɓɓata rai da jan tsaki. Lallaɓa shi ta yi ya sauko daga kumburin da yake, ta nuna masa an ba ta wayarta yau, taya ta murna ya yi sannan suka fita tare, ta shiga kitchen shi kuma ya yi ɗakinsa.

Ba ƙaramin firgicewa General Ibrahim ya yi ba da ganin wannan videon, wani irin gumi ya shiga tsatstsafowa a jikinsa. D.P.O dake karantarsa ya ce. "Zaka ce ba kai ba ne wani ne ya yi amfani da fuskarka? Wannan ƙaryar da ka yi ta ƙara sanya mini zargi a kanka." General dai kasa magana ya yi, sai goge zufa yake yana zare ido. D.P.O ya janyo laptop ɗin dake gabansa ya yi yan danne-danne sannan ya juya ta yanda za ta fuskanci General Ibrahim, bai ce komai ba sai wani kallo da yake bin sa da shi. General Ibrahim ya ɗaga ido daƙyar ya dubi laptop ɗin, videon lokacin da ya shiga reception ɗin Aminci Hotel ne.

"Wannan ma ko za ka musa ne? Ka saka facemask a lokacin dan ka yi badda kama, ma'aikacin hotel ɗin ya buƙaci ka buɗe fuskarka ya gan ka, sai ka ba shi cin hanci na 20k dan ya ƙyale ka wuce ka je ka kashe ƴar mutane. A matsayinka na babban jami'in tsaron ƙasa, wanda ƙasa take alfahari da kai."

"Haba D.P.O ya zaka dinga alaƙanta ni da abun da ban sani ba? Ni fa ba ni ba ne wannan da kake magana akansa." General Ibrahim ya faɗi haka cikin borin kunya zuciyarsa na tsananta bugu.

Miƙewa D.P.O ya yi ya ce. "Idan mun je gaba ka yi musu duk wannan bayanin." Bai jira cewarsa ba ya ƙwallawa Inspector kira, bayan ya shigo ya ce masa. "Ku tafi da shi headquarter tare da ƴan'matan nan, I.G yana jira, ya ce a mayar da case ɗin can, i will fallow you back.

Kafin dare labarin kisan Ihsan da videon da ta ɗauka nasu ita da General Ibrahim ya gama zagaye ƙasa da kewaye, duk inda ka je zancen ake yi. Al'amarin ya girgiza manyan ƙasa da Sojoji waɗanda suka san General Ibrahim, saboda yadda yake nuna shi na Allah ne akan komai, da yawa ba su yi tunanin zai aikata hakan ba.

Kwance yake akan gadonsa ya mimmiƙe baƙaƙen ƙafafuwansa, wata mata wadda da alama Matarsa ce tana yi masa tausa. Taba ce a hannunsa yana ƙarawa sama hazo daga kwancen da yake. Wayarsa dake gefensa ce ta shiga ruri, tsaki ya yi cikin maganar riƙaƙƙun ƴan daba ya ce. "Ba za a taɓa barin mutum ya huta ba." Ɗaukar wayar ya yi ya ɗaga ya kara a kunne, sai da ya zuga ya fesar sannan ya ce. "Ina jin ka ya aka yi ne? Kira da sakaliyar yammar nan?"

"Ban gane in hau WhatsApp za ka tura mini abu ba, kawai ka faÉ—a mini, ka san ni yanar gizon nan ba wani gane mata nake ba."

"To na ji, tunda ka dage zan hau." Ya ƙara jan tsaki sannan ya katse wayar. Yana ƴan mintocinsa ya siyi data ya kunna ya shiga WhatsApp. Wani uban ihu ya kurma tare da yar da wayar a ƙasa, cikin zafin zuciya ya cillar da tabar hannunsa tare da narka wani uban ashar ya ce. "Yata Ihsan ɗin aka kashe? Sannan kuma wancan tsohon matsiyacin gajeren Sojan ake zargi? Bayan ya gama lalata da ita? Taɓdi jan, Ibrahim ya deɓo ruwan dafa kansa, wallahi, wallahi, wallahi sai na ɗauki fansar jinin ƴata."

Aruɗe mahaifiyar Ihsan ta miƙe cikin ƙaraji ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Mai gida me kake cewa ne? Ban fahimta ba, wacce Ihsai ɗin aka kashe? Ba dai yata ba?"

"Ita fa Rabi, wai tun rana abun ya faru, ana ta kiran wayarmu daga ni har ke ba a same mu ba. An taɓo tsuliyar dodo Rabi, za a yi yaƙin da ba a taɓa yin kamar shi ba a duniya wallahi."

Rabi da ba fahimtar abun da yake cewa take ba ta ɗauki wayar da ya cillar cikin rawar jiki ta latsa, videon gawar Ihsan da bayanin abun da ya faru ya bayyana, ƙara ta fasa tare da zubewa a ƙasa sumammiya.

Na'ima na zaune a parlour ita kaÉ—ai tana kallo wayarta ta fara ringing, murmurshi ta yi tare da É—agawa.

"Hello Hajiya Maryam ya ake ciki ne?"

Daga ɗaya ɓangaren Hajiya Maryam ta ce. "Komai ya kammala ƙawata, ba dai level 1 take ba department of Mass communication?" Da sauri Mami ta ce. "Nan ne."

"To ki kwantar da hankalinki tamkar tsumma a cikin randa, wanɗanda na bawa aikin nan ba ni da haufi a kansu, gwanaye ne, ba su taɓa aiki an samu matsala ba, ke dai kawai da zarar aiki ya cika ki cika musu aljihunsu da ƴaƴan banki."

"Ba su da matsala da wannan, kin san kuɗi ba damuwata ba ne, ni dai kawai buƙatata ta biya, tsinanniyar yarinyar nan ta bar mini gida ko na huta, haba na gaji, na yi makircin na yi amma har yanzu ban ci nasara ba?"

"To daga wannan karon kin gama cizan yatsa ƙawata."

Murmushi Na'ima ta yi ta ce. "Da kuwa na zuba ruwa a ƙasa na sha." Maryam na dariya ta ce. "Ko acikin kwata ne ma ki zuba ki sha, duk a cikin celebration ne." Dariya suka yi a tare cikin tsananin farinciki.

Washegari 8 Salman yake da lecture, Abra kuma sai 10 hakan ya sa ba su tafi tare ba. Ƙarfe 1 Salman ya fito daga lecture, bayan ya yi Sallah ya nufi department ɗin su Abra, ya jira har ƙarfe biyu suka fito daga lecture. Yana tsaye a bakin class dinsu yana zuba idon ganin ta, amma har kowa ya gama fitowa bai ga ko mai kama da Abra ba. Cikin mamaki ya shiga dudduba cikin department ɗin nasu amma bai gan ta ba, ya kira wayarta ya fi sau 20 ba a ɗauka ba. Hankali a tashe ya kira Na'ima ya tambaye ta ko Abra ta dawo gida? Sanar masa ta yi tana zaune a main parlour tun 12 amma ba ta ga shigowar Abra ba, direbansu ya kira ya tambaye shi ko Abra ta kira shi ya zo ya ɗauke ta? shi ma ya ce masa ba ta kira shi ba. Hankalin Salman idan ya yi dubu ya tashi, duk inda yake tunanin zai ga Abra ya duba amma bai gan ta ba, ya tattambayi classmates ɗinta amma duk amsar ɗaya ce ba su gan ta ba, majority ma ce masa suke yi ba su san ta ba, tunda kullum cikin facemaks take. University ba secondary school ba, balle ya yi report ya ce bai ga Abra ba, to wa ma zai yiwa report ɗin?

Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/1, 3:01 PM] Abk: Ƙara rikicewa Abra tayi, ganin yadda ya tayara da motarsa ya bar gurin. Gaba ɗaya ta rasa abunda yakamata tayi a gurin nan, ihu za tayi ko kuka za tayi? Bata koma gurin cin Abincin nan ba, ta nufi department ɗin su, tana zuwa ta tarar da Salman da waya a hannunsa yana lelleƙawa  yaga ta in da zai hango Abra.
Yana waiwayowa ya sukai ido huÉ—u da Abra da take ta tsuma.

Da sauri ya ƙaraso in da take yana faɗin "Wai ina kika shiga ne? Over 15 missed calls, amma baki ɗaga ko ɗaya ba.
Shiru tayi tana rarrraba ido, ta kasa ce masa uffan.

A É—an hasale yace "ki yi mini magana ma, kin tsaya kina kallona".

"Wani lecturer ne ya ƙwace mini waya"

"Me ki kayi masa da ze ƙwace miki waya?".

"Wayata ce tayi ringing a aji, shine ya ƙwace mini wayar" tai maganar tana tsilli-tsilli da ido, saboda ƙaryar da tayi.

Salman dai kallonta kawai yayi, yace "to yanzu daga ina kike?".

"Cafeteria naje inci Abinci".

"To Yanzu kinci Abincin?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Wai meke damunki ne, gaba É—aya kamar a tsorace kike fa" yai maganar yana kallonta.
Chapter 50 · 0% Book details