← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 145

Sashe 125

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya ƙalau." Ta amsa tare da ɗaukar little, kamar wadda aka faɗawa yarinyar sai ba ta yi mata ƙiwa ba, sai ma dariya da ta shiga bangala mata. Socks Mami ta ɗauko ta fara saka mata tare da faɗin. "Lallai yarinyar nan, wato ke ba kya yi wa iyayenki ƙiwa ko? Da wani ne ya ɗauke ta da tuni kin cika ɗakin nan da kuka da ciccilla ƙafafuwa." Murmushi Afra ta yi tare da shafa sumar kan little, tana jin duk duniya babu abin da take so sama da yarinyar. Tare da suka koma parlour da Mami, lokacin har Salima da Abbi sun fara karyawa. Cikin son gwaninta Salima ta miƙe ta yi serving ɗinsu, don a gaban Abbi biyayya da girmamawa take yi wa Nai'ma. Ciki-ciki Mami ta ce. "Thanks." Abbi bai ji daɗin hakan ba, amma ya danne saboda Afra dake gurin bai nuna ba, fahimtar hakan ya sa Salima sakin murmushi cikin jin daɗi, dama abin da take so kenan a kodayaushe, Abbi ya dinga ganin lefin Mami a zamantakewar su.

Tsurawa kayan breakfast ɗin ido Afra ta yi, a kallon farko da ta yi masa ta ji yawunta ya tsinke, ga ƙamshinsa da ya cika mata hanci, tun kafin ta ci ta san ba ƙaramin daɗi zai yi ba. Inna da Yaya Musa ne suka faɗo mata a rai, ji ta yi dama a ce tare da su za su kwashi wannan daɗin, ga masoyin nata bread ƙatoto a gurin. A hankali ta ɗauki cup ɗin da Salima ta haɗa mata tea ta yi Bismillah ta fara sha, daidai lokacin Salman ya shigo parlour'n. Gabansa ne ya yanke ya faɗi ganin Afra, don gani ya yi tamkar Abra ce zaune a gurin, hakan ya tuno masa lokuta da dama da suke yin breakfast exactly like this da Abra. Addu'a ya yi mata sannan ya ƙarasa dinning area ɗin cikin sanyin jiki. Bayan ya gaishe da su Abbi ya ɗauki little dake bacci sannan ya zauna. Kamar yadda Salima ta yiwa kowa haka ta tashi ta yi serving ɗin shi. Ba yabo ba fallasa ya yi mata godiya. A hankali Afra ta ɗaga kyawawan idanunta ta kalle shi tare da sakar masa murmushi, mayar da mata murmushin ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce mata. "Morning Angel, da fatan kin tashi lafiya?"

"Lafiya ƙalau"

Mami dake lura da su ta yi gyaran murya, hakan ya sa Salman haɗiye abin da yake son faɗa, sanin da ya yi ƙa'idar Abbi ne idan ana cin abinci ba a magana idan ba dole ba, gyaran muryar da Mami ta yi kuma ya san tuna masa hakan take. Bayan kowa ya gama cin abincin Abbi ya dubi Afra ya ce. "Yata a ina kika tsaya da karatu ne?"

"Na yi Candy."

GyaÉ—a ya yi ya ce. "Da kyau, islamiyya fa?"

"Muna izifi Ashirin."

"Masha Allah, yanzu kina da takardun WAEC da NECO?"

"Eh, na taho da ita ma, Inna ta haÉ—o mini a cikin kayana, amma NECO kawai na yi."

"Okay." Abbi ya faÉ—a tare da mayar da duban shi ga Salman ya ce. "Idan Allah ya kai mu gobe Monday ka je ka yi mata registration a school É—in English Academy, saboda ta samu bakinta ya faÉ—a a Turanci kafin ta shiga University, idan an fara registration na JAMB sai a yi mata, Islamiyya ma ka kai ta wadda kuka yi ta cigaba da karatun a can."

"Insha Allahu Abbi."

Cikin matuƙar farinciki Afra ta ce. "Na gode sosai Abbi, Allah ya ƙara girma da arziƙi."

"Amin Daughter, babu komai. Yanzu sai ka kai ta, ta gaishe da su Ammi, idan kun dawo sai ku je tare da Auntinku ku yi mata shopping na kayan sawa da sauran abubuwan amfani." Ya ƙarashe maganar idanunsa a kan Salman.

Godiya sosai Afra ta yi masa har da hawayenta, ta so a ce Baba yana raye ya ga wannan ranar, don ba shi da buri da ya wuce na ganin ta yi karatu mai zurfi na addini da na boko, karamcin da Abbi ya nuna mata a yanzu ya ƙara tabbatar mata da an yi wa ƴar'uwarta riƙon mutunci a gidan, hakan ya ƙara kwantar mata da hankali akan zamanta a gidan.

Daren jiya Adnan bai samu ishashshen bacci ba saboda damuwar dake cunkushe a cikin ransa gami da fargabar rasa Afra. Raba dare ya yi yana kallon hotunan Abra cikin zubar hawaye tare da surutai, ta tafi ta bar shi cikin tsananin kewa da ƙaunar ta, ya samu wacce yake ganin za ta ɗebe masa kewar ta amma ita ma yana ƙoƙarin rasa ta. Sai bayan Sallar Asuba wani wahalallen bacci ya ɗauke shi, bai farka ba sai da goma ta wuce, ko sakkowa bai yi daga kan gadon ba ya lalubi wayarsa ya kira Mami, bayan sun gaisa ya ɓukaci ta ba wa Afra saboda muryar ta kawai yake son ji ko zai samu nutsuwa a cikin zuciyarsa, lokacin su kuma sun tafi gidan Ammi, cikin rashin jin daɗi ya yiwa Mami sallama, a ransa yana ƙudirce dole gobe ya yi wa Kano dirar mikiya.

Littafin kuɗi ne, don neman ƙarin bayani: 09047871750
[11/20, 7:09 AM] Abk: Washegari kamar yadda Adnan ya sanya a ransa haka ne ya kasance. Tun asuba ya shirya cikin wata shadda shampoo maroon colour ya murza hula duk da bata dame shi sosai ba, amma ganin weather ya sanya ya yi shiga mai kyau. Sai ƙamshin Pur oud yake lokacin daya fito gari ya yi duhu sbd hadarin dake kwance a garin Kadunan.

Ba tare da sanin Hajiya Mama da Abba ba ya nufi Kano cikin duhun asuba sai gudu yake shararawa burinsa kafin 11 na safe ya yiwa Kano tsinke idanunsu ya sauka akan Afra ko ya samu sauƙin ciwon da zuciyarsa ke masa akoda yaushe. Cikin wannan tunanin ya ƙarawa motar giya.

Afra na zaune cikin wata white-collared t-shirts tare da wani red cropped trousers ta ɗora wata red ɗin kinomo a saman kayan, tayi kyau sosai domin duk a cikin kayan da Abbi ya bada akai mata shopping ne. Hannunta riƙe da Aishatul-humaira wacce a kullum ƙara wayo take. Mami data fito ta ce.
"My dear kinji daÉ—i Little bata miki halin nata, ko dai ta gane ke Mother É—in ta ce?"

"Wallahi Mami ina sonta sosai, bana son rabuwa da ita kamar muna kama ko?" Kafin Mami tayi magana Salman dake gyara zaman babbar rigarsa ya ce.
"Dake da ita ban san wanda nafi so, ina tunanin burina ya kusa cika"

"What are you saying Salman?" Ya shafa sajan fuskarsa yana basarwa ya ce "No Mami,ina breakfast É—ina?" Mami ta Harare shi ta ce.

"Liar, It's like I heard you say something?" Ya girgiza yana zama kusa da Afra idanun shi akanta ya ce.

"It seems that Mami's ear is starting to have problems. Amma breakfast na ce ta, yunwa zata hallaka miki É—an yaro Mami"

"Allah ya shiryaka Salman, yunwar ka kewa haka?" Ya marairaice fuska sosai wanda ya bawa Afra mamaki ya sanya ta buɗe baki tana kallon ƙato da shagwaɓa. Da ƙyar ya ce

"Da gaske Mami yunwa na keji sosai, Yaya Please abinci" ya faɗa tare da juyawa ya kalli Afra wacce ke riƙe da Aishatul-humaira tana mata tsalle tsalle da ƙafa a cinya.
Barin wajan Mami tayi cike da fatan samawa Salman nasara domin ta riga da taji abin da ya ce.

"Why are shy yaya my angel?" Ya faɗa yana saka hannunsa zuwa haɓarta tare da juyo da fuskarta suka fuskanci juna. Fararen idanunsa masu kaifi wanda suke ƙara sawa Afra kwarjinin Salman a idanunta ya zuba mata ya ce.
"Ba haka yaya Abra ke mini ba, na sama hira da yayata sosai wani lokacin daja hancina kamar like this" ya ƙare maganar yana jan hancinta cike da ƙaunar ta wacce lokaci guda ta mamaye dukkan zuciyar shi.
Cikin siririyar muryar ta ta ce "Uhm to aini ban girmeka ba" ya lumshe idanunsa yana mai girgiza kansa kaÉ—an tare da tura hular kansa zuwa gaba ya ce.

"Injiwa? Tsakanina da Abra good 3yrs ne, ke da Abra twins shekara É—aya aka haife ku Kinga kin zama yayata"

"Kuma na ganka ƙatoto ni kuma ƙarama" zuba mata gajiyayyun idanun shi ya yi yana karantar yanayin ta sosai kafin speaking calmly ya ce.

"Sbd ni ne mijin ai" ta ware ido ta ce "me kace?" Ya girgiza yana miƙewa tsaye tare da ɗaukan Little ya ce "I'll explain later" kafin tai magana ya miƙar da ita tsaye ba zato taji ya jawota ɓarin jikinsa ya yi musu photo yana murmushi ya ce "My family my happiness, zuri'ar Salmanun-faris" ita dai bata fahimta ba, sai saurin zame jikinta da tayi zuciyarta na bugawa da ɗan ƙarfi.

Dining room suka nufa a can suka samu Salima Abbi daman tun 7 yabar gida yin binciken asalin iyayen Afra da Abra. Jikin Salima na É—an rawa ta ce "Salman my son bari na serving naka abinci" idanun shi akan Afra ya ce. "No thanks, Afra please serve me" ya faÉ—a fuska a kame.
Salima bata so hakan ba domin gaba É—aya Salman birgeta yake tana neman duk yadda da zata samu connection da shi amma ya toshe ba lallai idan yana mata kallon matar Mahaifin nasa ba.
Afra tai serving nasa a nutse take har kar nan gudun kada ta kwafsa, ta nuna ƙauyancin nata shi ya sa ta kame kanta da kyau domin siyawa kanta martaba da ƙima a idanun jama'ar gidan.
Ganin daga Afra har Salman abinci suke ci babu wanda yako kalli inda Salima take, ya sanya jiki a sanyaye ta miƙe kamar zata ɗauki Little wacce take barci a jikin Salman ta wani ƙanƙame shi da duk hannunta biyu sai kawai ta fasa da ɗan sauri tabar wajan.

Suna cin Abinci Mami ta fito cikin kwalliya sai ƙamshi take, ganin Afra da Salman ya bata sha'awa. Ta ɗauki Little tare da bar musu wajan. Lokaci zuwa lokaci Salman ke satar kallon Afra yana jin kamar ya faɗa mata abin da ke zuciyarsa kada ya ƙara rasa damar shi a wannan karon.
Chapter 125 · 0% Book details