← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 145

Sashe 37

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya kawai take kanta a ƙasa, gaba ɗaya hankalinta baya jikinta, jinta take wata uncomfortable ta saba duk inda zata suna tafiya tare da Salman, a yanzu kuma ita kaɗai ce gani take kamar mutumin ɗazo ne zai biyota, tana tafe kuma tana cin karo da Old Students na University ɗin, sai faɗin Sir S.p Adnan Aliyu Matawalle suke suna nufar hanyar data baro.
Ita dai ba wanda ta kula balle ta san meke faruwa, ji tayi yunwar ma ya tsaya mata.

Caraf taji an riƙe mata hannu, a gigice ta ɗaga idanunta wanda ta gani kuma yasa ta saki ajjiyar zuciya tana kwaɓe fuska tare da ƙanƙame hannunsa daya riƙe ta da shi. Salman ya ware idanunsa akan Abra yace. "Ya na ganki a hargitse?" Ta girgiza masa kai, nan da nan mood ɗinsa ya sauya a tunaninsa wani ya biyota, bai ce mata komai ba sai manyan idanunsa daya kafesa da ita.

"Let's go Faris"
Ta faɗa kamar zatai kuka tana mai sake damƙe hannunsa, Salman ya haɗe fuska a kaushashe ya ce "Ban gane mu tafi ba, you told me you are hungry" "yanzu kuma na ƙoshi, mu tafi gida tunda mun gama abinda ya kawo mu" ta faɗa tun kafin Salman ya sauke numfashi da ga maganar da ya yi.

Kasa ce mata komai ya yi, ya daɗe da sanin halin ya yar tasa, a hankali ya kama hannunta tare da nufar ƙasan wata Bishiya da ita, zaunar da ita ya yi saman Kujera a hankali Shima ya zauna cikin rarrashi ya ce.
"Kina jin yunwa sosai Yaya, ki fara cin abincin sai mu yafi ba zan barinki da yunwa har muje gida ba, kuma ba lallai Mami tayi abinci ba"
Abra ta haɗe rai, tama ƙi yarda ta kallesa baki ɗaya, ta lura akan buƙatar ta Salman baya jin mgnarta sam.

"Angel" tai masa banza, tare da ɗauke kanta gefe guda a hankali ta shiga wasa da yatsun hannunta. Salman ya zame ƙasan qwiwoyinsa hannunsa ya ɗora a cinyar Abra, yana leƙa fuskarta dake ƙasa, haɗa idanu sukai tai saurin rufe nata tare da ɗauke kai zuwa gefe.
Tashi zaune ya yi tare da zama gefen ta, takeaway ɗin daya kawo mata ya buɗe, wainar shinkafa ce mai zafi, da miyar agoshi ta sha nama sai ƙamshi take, bayan ya buɗe takeaway ɗin ya ɗauki ruwa faro tare da wanke hannunsa.

Muryarsa bata fita sosai yace "Yaya" tai masa banza ya ƙara cewa "Angel" still taƙi kulasa, gyara zama ya yi yana tura hular kansa baya saboda damunsa da tayi, kamar da ga sama taji yace "Abra...!!!" Da sauri ta juya baki buɗe saboda Mmkin jin sunanta a bakin Salman wanda bata taɓa ji ba, suna haɗa idanu ya ɗauke nasa idon, shima fuska a haɗe.

Ganin sauyin nasa yasa ta marairaice fuska tace "Faris muje gida" bai bari ta sake magana ya kama Fuskarta da tafukan hannunsa ya tallafo haɓatar sosai, baki ta buɗe Zatai magana ya yi saurin ɗora yatsarsa a bakinta ya ce "Shhhhhh" shiru ta yi wanda ba tai niyya ba, a karo na farko wani kwarjinin Salman ya ziyarci ƙwayar idanunta, ƙasa tayi da ganinta.

"Hahhhh" Salman ya faɗa a sanyaye, ba tare da ta yi musu ba, ta buɗe cute small mouth ɗin nata wanda yake ɗauke da red ɗin laɓɓan masu taushi a hankali ya saka mata naman daya ɗakko har lokacin yana riƙe da Fuskarta yana ƙare mata kallo, ita kuma idanunta a ƙasa. Tana cinye naman ya fara bata wainar shinkafar bata wani ci da yawa ba, ta girgiza masa kai ya ce "Sai kin cinye fa"

Kamar zatai kuka tace "wallahi na ƙoshi, ka cinye sauran" shima ya ce "Ni ai bance ina jin yunwa ba, karatu zaki fara dole kici abinci ƴar nan" yana faɗin hakan ya ƙara tura mata wainar a baki. Da ƙyar ta haɗiye tana zare Idanunta tace "Zanyi amai fa" yana haɗe fuska ya ce "ba wani amai yaya, na fahimci sai nayi maki da gaske ba ruwana da girmata da kikai"

Ba zato yaji ta fashe masa da kuka sosai, da gudu kuma ta miƙe tsaye tana kakarin amai amma sam yaƙi zuba, kakari take sosai jikinta na rawa, da sauri Salman ya kama hannunta ganin zata faɗi yayi saurin yi mata side hug ruwa ya bata tasha yana bubbuga bayanta "Sorry Angel, I'm so sorry" ƙin kulasa tayi sai shassheƙar kuka take, ganin da taƙi kulasa duk ya rikice daidai nan ƙawarta Khairy ta ƙaraso itama an bata admission a B.u.k.

Cikin rashin damuwa da yadda ta gansu tace "Wow yau nayi Sa'ar zuwa B.u.k Wlh" Shiru Abra ta yi Salman ya ware idanunsa yana faÉ—in "Sbd kin samu course É—in da kikeso?" Ta girgiza masa kai tace "Is not like that Salman, I have never seen a man so beautiful as him" daga Abra har Salman ba wanda yace mata komai, Salman hankalinsa na kan Abra ita kuma ta haÉ—e fuska tana kallon Wani wajan.
Khairy baki na ƙaiƙayi ta kalli Abra tace "Wai ashe a nan shcl ɗin ya yi karatu, ya riƙe muƙamin shugaban ɗalibai, ba kiga yadda aka rufesa ba kowa na son ganinsa, kai Ubangiji ya yi halitta a nan"

Abra ta taɓe baki tace "who asked you? We have nothing to worry about... let's go Faris" dry khairy ta saka tana tafa hannayenta cikin farin ciki tace.
"Ba lallai ki yarda da kyansa ba, tunda baki gansa ba, ni da har kallon sexy eyes ɗinsa na yi, gashi wani babba mai kyan sura, irin namijin da nake so mai baƙar fata" Haka kurum Salman yaji baya son jin maganar, duk da bai san Who is she talking about ba, amma yaji ransa ya ɓaci.

Abra ta kalli Khairy tace "kuma sai ya zama dole na sani Ummulkhairy?" Khairy na ƙoƙarin magana Idanunta ya sauka akan Sp Adnan shi da Fayyad suna tahowa, jikinta na rawa tace "Look Abra, wlh shine wanda nake maki magana" daga Abra har Salman babu wanda ya juya balle suga wanda Khairy ke magana akansa.

Fayyad ya yi Murmushi yana dokan kafaɗar Adnan yace "You're kidding, it's just your pride that prevents you from finding a wife" Ya ƙare maganar yana ƙara kaiwa Adnan doka, kafin ya ɗora da faɗin.
"Aure duniya ne, ma'aurata sune kaɗai zasu fahimci abinda nake cewa, Let's keep the joke aside, you have education, money, health, you are handsome Adnan, babu macan da za tace bata sonka I'm still wondering akan abinda ya hanaka aure, Shawara nake baka tun kafin lokaci ya ƙure maka wallahi rayuwa bata da tabbas gwara ka Ajjiye masu yi maka addu'a kafin lokaci tsofa ya riske ka"

A karo na farko Sp Adnan yai wani irin Murmushi daya sanya fararen haƙoransa bayyana, wanda shi kansa Fayyad ya yi mamakin Murmushin nasa. A hankali yace. "Thank you Alhaji Aliyu Matawalle"
Fayyad ya ware idanu ya ce "it's just a suggestion. Ba lallai ka amince ba"

Su Adnan na zuwa daidai inda su Abra suke ya lumshe idanunsa kana ya buÉ—e ya ce
"I don't believe in true love, mata sai a hankali there is no Promise in their hearts"

Da sauri Abra ta matsa kusa da Khairy ganin Adnan na ƙoƙarin take mata ƙafa, amma yana zuwa inda take ya janye ƙafarsa zuwa wani gefe ko inda suke bai kalla ba, yana ji Khairy na cewa "Bye sir" amma ko amsawa bai ba. Salman ya nufi motarsu ganin Drivern gidansu, Abra tabi bayansa. Kusan lokacin ɗaya dasu da Adnan suka bar cikin B.u.k.

Washegari ya kama Weekend. Abra na tsaye a kicthen sanye cikin wata fitted gown ɗin green ɗin lace sai Stones masu ƙyalli, tayi simple ɗauri gashinta har baya, tattara carrot ɗin data yanka tayi, tare da green, yellow, and red pepper ta Ajjiye gefe guda. Green beans ta ɗauka wanda ta ɗan dafa, bayan ta kammala komai ta ɗauki shinkafar da tayi pi bowling ta juye ta zuwa cikin wata pot ɗin, another pot tai using wajan zuba mai mara yawa, ta zuba kayan miya, kana ta zuba su magi da spices in few minutes ta haɗa fried rice with chicken kabab. Tana gamawa ta haɗa salad wanda tai using lemon kaɗan a ciki sai pineapple juice.

Salman dake shigowa kitchen ɗin yai saurin tsayawa a bakin ƙofa yana jan numfashi tare da rufe idanunsa, na ƙamshin daya daki hancinsa. Idanunsa ya ware a kanta tun daga kan fararen yatsun ƙafarta ya fara Kallonta, zuwa hips ɗinta da gadon bayanta, a hankali ya maida idanunsa kan baƙin dogon gashinta. Cikin rashin sani ya furta.

"Rest of my life.... Angel na" Abra ta juya da sauri suka haÉ—a idanu ya kashe mata ido É—aya tare da É—aga mata gira. "like you said something?" Ta tambayesa bayan ta gama wanke hannunta a jikin sink. shiru ya yi mata sai idanu da yake binta dashi, ganin ta É—auke kanta zuwa É—aukan warmers É—in data zuba abinci ciki a nutse ya ce.
"Sweetheart"
Juyawa ta kuma yi suka haɗa idanu, ta wani haɗe fuska tace "Wai me kake cewa ne,It's like calling someone's name?" Hannunsa da yake saƙale a ƙirjinsa ya zame tare da zuba su cikin Aljihu, a hankali ya ce "wane suna zan kira wanda ya shige Angel" tana miƙa masa warmers ɗaya tace "ba haka naji ba, kadai ce wani abu nada ban" Murmushi kawai ya yi mata yana girgiza kansa, shi kansa bai san lokacin da yace hakan ba.
"Kada ki manta kina using Hearing aid ne Angel" ta kallesa tace "And then?" Ya ware shoulder irin Nothing É—in nan.

A tare suka jera kayan abincin akan dining room suna kammalawa Salman ya zauna yana faɗin "zuba min abincin" hannu tasa ta dungure masa kai tana faɗin "Food, food, food. stop eating too much" Salmanun-faris girgiza kai ya yi yana tsiyaya Juice a cup a hankali yake sipping Juice ɗin kafin ya ce "gwara na zama ƙatoto yadda za kifi yadda da abinda zan zo maki da shi" Abra tai shiru can kuma tace "like how?" Yana ɗaukan spoon ya ce "With time"
Kafin wani ya ƙara magana a cikinsu Mami ta ƙaraso wajan hannunta riƙe da waya cikin wani dakakken lace idanunta akan Abra tace.
Chapter 37 · 0% Book details