← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 145

Sashe 89

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace Adnan ya riƙo gashin kanta cikin mugunta tare da faɗin. "Weldone TSINTACCIYA, mara asali da 'yanci, ke har kin isa ina magana kina musa mini, wato kin waye wuyanki ya isa yanka? Who are you? Kin yi kaɗan wallahi!" Fizge kanta ta yi saboda wata irin azaba da ta ji tun daga kanta har tafin ƙafarta, cikin kuka ta ce. "Wanne irin azzalumi ne kai mara imani da tausayi?" Dariyar rainin hankali ya yi ya ce. "Is your father, duk waɗannan abubuwan da kika lissafa halinsa ne ɗabi'arsa ce. Abra Khamal Khamis! Ko kashe ki na yi ban yi kwatankwatan zaluncin da mahaifinki yake aikatawa ba." Za ta kuma magana ya katse ta cikin tsawa da faɗin. "Za ki tashi ki yi abin da na saka ki ko ya?" Cikin kuka ta miƙe jiri na ɗibanta ta fice, har faɗuwa ta yi, amma ko a jikinsa. Bayan ta zuba masa abincin ta ajiye masa ya ce sai ta dafa masa coffee, ba ta yi musu ba ta dafa ta kawo masa cikin matuƙar dauriya da ƙarfin hali. Bayan ta koma ɗaki ta kwanta ta samu bacci ya ɗauke ta da ƙyar, amma Adnan ya zo ya katse mata baccin da buƙatar gangar jikinsa, cikin rashin imani da tausayi kamar yadda ya saba zuwar mata kodayaushe.

Na'ima ce kwance a kan katifa idanunta a lumshe amma ba barci take ba, tunanin yadda za ta shawo kan Khamal ya haƙura ya mayar da ita ɗakinta kawai take. Idan ta tuno yanayinsa a lokacin da suka rabu sai ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, saboda sanin da ta yi indai yay irin wannan fushin saukowar shi sai an ci ƙwaƙwa. Ba ta taɓa da na sanin tura Salman China da dagewa akan Auren Abra ba sai yanzu, don da suna nan ta san da yanzu tana gidanta, ko da Khamal ya sake ta ba zai kore ta daga gidansa ba, saboda gudun kar su Abra su shiga cikin damuwa, don idan akwai abin da Khamal ba ya so a duniyar nan bayan fushin iyayensa sai ganin ƴaƴansa a cikin damuwa. Cikin haka Nepa suka yi tsiyar su suka ɗauke wuta, hakan ya sa sauro ya fara shawagi. Tsaki Na'ima ta ja tare da yin juyi tana kore sauron dake yi mata kuka a cikin kunne. Ba ta kai ga sauke hannu ba wani ya millira mata cizo a gefen kunne, hakan ya sa ta tashi zaune ba shiri ta janyo wayarta ta kunna torchlight. Cikin mamakin take kallon Aunty Suwaiba dake baccinta hankali kwance, jinjina kai ta yi don ta san ita kam baccinta a haka ba zai yiyu ba in dai ba Nepa aka dawo da ita ba, ga wani irin zafi da ya rufe ta lokaci ɗaya. Gabaɗaya ta rasa sukuni, ta rasa inda za ta saka ranta. Baƙin ciki kamar ya kashe ta, ga sauraye sai watanda suke yi a jikinta. Ita kuma ba ta son maganin sauro balle ta kunna, mura yake saka ta. Wannan daren dai cikin wahala ta yi shi, sai washegari bayan Sallar Asuba ta samu bacci ya ɗauke ta.

After 2 days

Hajiya Na'ima ce tsugunne a gaban mahaifiyarta tana kuka tare da faɗin. "Kullum sai na kira shi sau ba adadi Mama amma ba ya shiga, na san kuma blocking ɗina ya yi, ko na yi masa text ma ba zai gani ba." Cikin damuwa ta ce. "Lallai ma yaron nan, wato shi ba ya uzuri a rayuwa ko? Bai san kuskure ba, ai ko Ubangijin da ya halicce mu muna saɓa masa kuma ya yafe mana. Amma ba komai, ba ni numbern Mahaifiyarsa mu tafi plan ɗinmu na biyu, in ya san wata ai bai san wata ba. Cikin rawar jiki Na'ima ta lalubo numbern Ammi ta yi dialling ta miƙa wa Mama wayar bayan ta shiga. Don ba ƙaramin gajiya ta yi da zaman gidan nasu ba, kullum cikin faɗa suke da Aunty Suwaiba, ga Faisal dake yi mata rashin kunya son ransa, saboda yana cike da haushin hana shi auren Abra da aka yi. Ga tattalin arziƙinta na neman ƙarewa a ɗan zaman da ta yi na kwana huɗu, ita ce sayan abincin gidan da kuɗin cefene, don Faisal daina bayarwa ya yi, ya ce tunda ta dawo gidan sai ta cigaba ita ma. Har ƙaton Gen. ta siya saboda ba za ta iya rayuwa cikin sauro da zafi ba, ga shi Mama kullum cikin cewa ta yi mata kaza ta saya mata kaza take. Gabaɗaya ta rame ta yi baƙi saboda damuwa da rashin kwanciyar hankali.

Ammi tana ɗakin Baffa tana yi masa tausa a lokacin, kiran Na'ima ya shigo wayarta. Miƙewa ta yi ta ɗauko wayar, ganin Na'ima ce ya sa ta faɗin. "Alhaji ka ga ƴar halak, yanzun nan na gama zancen su ita ƴarta, na ce kwana biyu shiru ba mu gaisa ba, duk da ita Abran Babanta ya ce wayarta ce ta samu matsala." Ta ƙarashe maganar tare da daga wayar ta kara a kunnenta tare da yin sallama. Daga can Mama ta amsa mata, cikin mamaki Ammi ta ce. "Au Hajiya ke ce? Ina Na'iman?"

"Tana nan ƙalau, daga yanda na ji maganarki da alama ba ku san abin yake faruwa ba."

"Me ya faru kuma? Allah ya sa dai lafiya?" Ammi ta tambaya a ruÉ—e.

Sanar da Ammi sakin Na'iman ta yi. Cikin jimantawa Ammi ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Subhanallahi! Baban nawa ne ya aikata haka? Da k'uruciya ma bai yi haka ba sai yanzu da girma ya fara kama su har an kai 'ya É—akin miji? Wallahi ba mu sani ba bai sanar mana ba."

"To dai yau kwananta huÉ—u a gida, abin dai ba daÉ—in ji."

"Ku yi haƙuri Hajiya, insha Allahu za a daidaita tunda saki ɗaya ne, bari in kira shi yanzu."

"Tom shikenan Hajiya mun gode, sai na ji ki."

Bayan sun gama wayar Ammi ta kira layin Abbi, ta yi masa har 2 missed call amma bai É—aga ba. Baffa dake sauraren duk abin da suka tattauna ya ce. "May be yana wani uzurin ne, idan ya gama na san zai kira, sai mu ji gaskiyar abin da yake faruwa." Ammi ta ce. "Haka ne, amma wannan abu bai daÉ—i ba ko kaÉ—an."

"Allah ya kyauta kawai." Cewar Baffa cikin jimantawa.

Kwance take a kan gado ta lulluɓe jikinta da bargo, fuskarta ce kawai a waje ta ƙura wa wuri ɗaya ido, ga dukkan alamu sana'ar tata take yi wato tunani. A haka Adnan ya shigo ɗakin ya same ta ba tare da ya yi sallama ba, uniform ɗinsa na police guda biyu ya watsa mata a jikinta, cikin ba da umarni ya ce. "Gashi nan ki wanke mini su yanzu-yanzu." Kallon kayan ta yi ta kalle shi ba ta ce komai ba, don ko magana ba ta son yi, saboda tarin damuwar dake cikin ranta, ga shi yau ta tashi ba ta jin daɗin jikinta, gaɓoɓin jikinta duka ciwo suke mata, ga ciwon kai da idan ana sabo da shi ta saba da shi, ga wata irin kasala da take ji.

"I'm talking to you Madam!" Adnan ya faÉ—a cikin tsawa tare yin kanta.

Cikin ɗaga murya gami da kuka ta ce. "Ba zan yi ba, idan ka tashi ka kashe ni, haba! Na gaji da wannan azabtarwar taka Adnan, ka yi mini duk abin da ka ga dama!" Ta ƙarashe maganar tare da tashi zaune ta ɗauki uniform ɗin nasa da niyyar ta cillar da shi, hakan ya sa ƙamshinsa dake manne a kayan bugar hancinta, da sauri ta saki kayan tare da toshe hancinta, don wani irin hautsinawa ta ji jikinta ya yi mata lokaci ɗaya. Dama tunda ya shigo ta shaƙi ƙamshin ta ji kamar za ta yi amai. Cikin masifa ya buɗe baki da nufin zazzage mata kwandon bala'i, miƙewar da ta yi cikin sauri kamar wadda aka tsikara ya hana shi abin da ya yi niyya, sakamakon ganin ta nufi toilet a guje ta fara kelaya amai kamar za ta amayar da kayan cikinta.

It's not for free, contact us for more information. 09047871750
[10/24, 12:28 PM] Abk: Ta daɗe tana aman, sannan ta fito gaba ɗaya gaɓoɓinta sun saki, saboda yunƙurin amai. Ko da yake ba sabon abu bane a gurinta, dan haka kan faru da ita lokacin period ɗin ta.
Ba ta ko kalli Adnan ba, ta wuce ta fara ƙoƙarin hayewa kan gado.
  "Wai me kika mayar da ni ne? Na umarce ki ki mini abu, amma kin koma gado me kike nufi?".
"Abin da idanunka suka gane maka, shi nake nufi" a sukwane ya yo kan gadon yana cigaba da bala'i "Ke kin isa babanki ya wulaƙantani, kema kice zaki mini rashin mutunci? Wato kin gado halin dabbanci irin na babanki".
"Adnan! Kar ka sake zagin ubana,uba fa bai fi uba ba".
"Kina nufin nima zagina za kiyi kenan?" Yayi Maganar yana nuna kansa da yatsa.
"Allah ya tsare ni in zageka, ni mahaifinka uba na É—auke shi, uba na gari makuwa, abin tausayi Allah ya bashi azzalumin É—a mai fuska biyu".

Taku ɗaya yayi, ya fizgota daga kan gadon, zai wanka mata mari, amma yaji jikinta zafi rauu, kamar an kunna wuta, hankaɗata yayi ta faɗa ƙasa ya nuna ta da yatsansa ya ce "Ko ki ɗau ubana uba, koma me kike ɗauke shi, abin da na sani shi ne, ubana yafi ubanki imani da mutunci, kuma na dawo na tarar da kayan nan baki wanke ba, sai na tattaka ki".
Binsa ta yi da ido har ya fice.
Girgiza kai kawai tayi, dan Yanzu zuciyarta ta fara bushewa da lamarin Adnan, dan haka a nan kan tiles ta gyara kwanciyarta, ta yi shiru abubuwa daban-daban na kai komo a kwanyarta.
Chapter 89 · 0% Book details