← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 145

Sashe 33

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsawa S.p Adnan Aliyu Matawalle ya ce.
"Heyyy!  What's going on here?"  Wani da ga cikin police ɗin wajan ya tsarawa S.p Adnan ya ce.
"He was arrested for raping a three-year-old girl"

S.p Adnan ya ware manyan idanunsa, idan akwai abinda ya tsana a cikin  main crime that people are found with shi ne ”fyaɗe” He hates the word and doesn't like it at all. Cikin ɗaga murya S.p ya ce "What? Reped  three-years old? Police officer ɗin ya ce "Yes sir, wlh abin is so boring The girl died too"

Nan take idanun S.p Adnan ya ƙara yin jaa fiye da baya jikinsa na ɗan rawa kasancewar sa Mutum mai zafin zuciya, yana zuwa wajan Mutumin da ya yi fyaɗen ya kama hannunsa yana faɗin.

"You're mad, How can you rape a little girl like that? Ehh? you killed her!"
S.p ya faɗa yana fesar da iska da ga cikin bakinsa, idan ransa ya ɓaci bai iya controlling kansa ba, gaba ɗaya Police Officers ɗin suka shiga hankalinsu.
Cikin ɓacin rai S.p Adnan Aliyu Matawalle ya damƙi Hannun mutumin ya ce.
"An old man like you is the one who will rape her?"
Ƙass!!! Sauti Hannun tsohon ya bada ƙara sakamakon ƙarya hannunsa da S.p ya yi, wanda shi kansa bai san ya aikata ba.
Rai ɓace ya koma Officer ɗin sa ya ɗauki key car ya nufi waje.
Police Officers ɗin suka faɗawa D.o.p, abinda ya ke faruwa shi kuma D.p.o ya faɗawa presquito, presquito ya miƙa tsohon zuwa Court.

Tun da ga bakin gate ya fara danna Horn babu saurarawa, da sauri gatekeeper ya buɗe masa gate ɗin, cikin zafin nawa ya tura kan Benz ɗin sa cikin entrance ɗin babban gidan na su. Murfin motar ya buɗe ya fito kansa a ƙasa hannunsa zu be cikin Aljihu ya nufi cikin gidan da ɗan sauri domin babu abinda ya ke bashi tsoro irin hadari. Gashi garin dab ake da fara ruwan sama.

Hajiya Mama dake zaune a Parlour tana kallon News ta ce. "Wlcm My son"  wajanta ya Ƙarasa yana ɗora kansa a cinyarta idanunsa ya rufe, kalmar fyaɗe na yi masa yawo a cikin kansa. Hajiya Mama ta ce "what happened? as if you are worried"
Mirginawa ya yi a saman cinyarta ta tare da yin shiru, a hankali ya ke saukewa numfashi a nan cinyarta barci ya É—auke sa tana shafa masa kai. Da idanu Hajiya Mama ta ke bin Adnan har tsoron zafin ransa ta ke, ga taurin kai. Tana jinjinawa matar da zata iya zama da shi matsayin miji. Burinta a yanzu bai shige ta ga aurensa ba.

Washegari ya kama weekend. Driving ya ke kamar zai tashi sama, Usman dake gefensa ya ce. "Wlh ka zubar damu Allah ya isa" S.p ya ja tsaki ransa a ɓace Usman ya ce "ka daɗe ba kayi tsaki ba, zance ne dole ka rakani kayi ta zama a haka mu soyayya yanzu muka fara" Adnan dai yaƙi cewa komai, kuma babu alamun zai ce Usman ya gyara zama ya ce.

"You don't understand, but love is love, it changes a person, ban taɓa tunanin zan so farar mace ba, burina na auri baƙar mace, When I saw Meenal for the first time, I couldn't help myself, yarinyar classic ce very educated ƙyakƙyawa ce sosai, A beauty I have never seen before" Usman ya wani lumshe idanunsa ya ce. "Kuma a photo kawai na kanta,  ina ta imagine yadda zan ganta reality, Uhm anya zan iya controlling kai na?

Ƙiiiiii!! S.p Adnan Aliyu Matawalle ya ja burki cikin zafin zuciya ya damƙo Usman ya ce.
"Banza, lion mayen mata zaka fice min da ga mota" Usman ya zare idanu ya ce "Goodness, zaka yiwa Meenal asarata let go of me pls my dear friend" hankaɗasa gefe S.p ya yi cikin ɓacin rai yaci gaba da driving har suka isa unguwar su Meenal wacce take da ɗan nisa da tasu sosai.

Kaf unguwar babu gida mai kyau da girma irin gidan Dr G.y Bulama, mai gadi ya buɗe musu ƙofa kasancewar Meenal ta sanar masa da zuwan guests ɗin ta. S.p ya gama parking Usman ya fara fita Adnan ƙin fita ya yi sai ma ƙira'ar Mishary Rashid Alafasy. A hankali ya ke bin ƙira'ar idanunsa rufe, cikin jin haushi Usman ya ce "Wannan dai wulaƙanci ne, ka ga idan zaka wulaƙantani a gaban Yarinyar nan ka koma kawai Nagode"

Adnan ya yiwa motar key, ganin da gaske tafiya zai Usman ya ce "Amma da ga ɗan iska sai kai S.p kaga ni wasa nake Please get down ga yarinyar nan" kashe motar ya yi tare da fitowa yana ƙare haɗe fuska nan na tasa, jikinsa sanye da maroon ɗin voyel mai kyau idanunsa maƙale da glasses mai kyau sai sumar kansa kwance da ita. Idanunsa ya ɗauke lokacin da Meenal ta ƙaraso wajan Usman ya shafa kai ya rasa me zance tayi musu Welcome ta ce "shall we...?" Ta faɗa ta nayin gaba. Usman ya kama Hannun S.p suka nufi guest Room ɗin da Meenal tayi.

Few minutes ta cika musu gabansu da kayan motsa baki, S.p ko amsa gaisuwarta bai ba, saboda rsai zufa data yanko masa, ganin yanayin S.p yasa Usman faɗin "Are You Okay Adnan?" A karo na farko Meenal ta ji Muryar Adnan mai tsananin daɗi ya ce "Headache.. i think I'm going now" ya faɗi hakan yana ɗauke idanunsa daga kan photon dake maƙale a jikin bango, Waje ya yi yana dafe kansa, yana fita Usman ya ɗan tattauna da Meenal ya na jin kamar ya ɗauke ta su tafi kawai tun yaushe, a nan tayi inviting na su zuwa birthday party ɗin ta, kana sukai sallama.

Kasa driving S.p ya yi, hakan yasa Usman ya amshi driving É—in suka nufi gida.

A nan garin Kano. Salman ne ke biye da Abra cikin Ado Bayero mall, bayan ya rakata Saloon suka biyo yin shopping tare da shan ice cream. Bill ɗin kuɗin kayan akai masu Salman ya bada a.t.m aka cira, shi kuma ya ɗauki kayan ya ce "Angel muje" Abra ta bi bayan Salman cikin sanyin jiki, musamman da wani mutum ya kafeta da idanu. "Yaya idan ki kai aure ba'a gidanki zan tare ba, sbd na dinga tayaki aiki,  wannan sanyin jikin naki ya yi wa, kalleki wata rana dai zan goyaki naji nauyinki, dan na tabbatar jariri sai ya fiki" Abra tai Murmushi ta ce "Allah ya shiryaka Faris" da sauri ya ce "Amin Yayata, ina buƙatar shirin Ubangiji kiyi min addu'a kwana nan bana gane kai na"

Da sauri ta ce
"Meke damunka Faris? Gaya min Pls" ya girgiza ma ta kai ya ce "Wlh ban sani ba Angel" suna ƙoƙarin fita daga cikin wajan mutumin dake kallon Abra ya yi saurin riƙe ma ta hannu. A razane Abra ta juya sukai idanu biyu da saurayin mai kyan gaske, fari tas ƙyakƙyawa ajin farko. Jiki na rawa ta fara ƙoƙarin  ƙwace hannunta.

Saurayin mai suna Abdullah ya ƙara riƙe hannun Abra gashi Salman ya yi mata nisa yana can yana surutu ya ɗauka suna tare, cikin razani Abdullah ya ja numfashi ya ce "Who are you?" Ya faɗa yana ƙoƙarin shafa fuskarta, kafin ya Ƙarasa ɗora hannunsa akan fuskarta ya ji an sauke masa wani irin mari, da sauri ya dubi Salman dake tsaye yana huci kamar zaki ya ce "How dare you slap me like that?"  Salman ya ce "An marake, kasan jikin waka taɓa? Wlh kamar an soka min  ma shi a zuciya,  mutum ɗaya keda mallakin jikin Angel wlh na ƙara ganin ka shiga harkata sai nayi maka illa"

A wannan lokacin Salman har Abra ya ji haushi,  ko inda take bai kalla ba ya juya tare da yin waje, yana ƙoƙarin ficewa Abra ta ƙwala masa kira
"Faris...!!!" Zubewa ta yi a waje jikinta na rawa numfashinta na ɗaukewa ƙirjinta na ɗagawa kamar mai Asthma, hannunta riƙe da cikinta, a kiɗeme Abdullah dake tsaye ya durƙusa zai kama Abra Salman daya ƙaraso wajan ya hankaɗe Abdullah yana zubewa gaban Abra yana faɗin "Yaya mene ya sameki? Yaya menene I'm here ga ƙaninki a wajanki, Angel open your eyes" ya ƙare maganar yana jijjigata amma tuni numfashinta ya yi sama yana ƙoƙarin ɗaukewa. Cikin tashin hankali Salman ya jawo Abra jikinsa yana ƙanƙameta kamar wani zai ƙwace masa ita.

Ganin numfashi na ƙoƙarin ɗaukewa, ga shi duk mutane sun zagaye su yasa Salman warware rolling ɗin kan Abra ya rufe mata fuska can kuma ya tuna da maganar wani malamin su daya faɗa musu a lap, cikin sauri jikinsa na rawa da ɓari ya ɗaga mayafin nata tare da zura ƙansa ciki, a hankali ya tallafo fuskarta a hannunsa tare da ɗora bakinsa akan nata...

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*

_Brigh pens✍️_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

                               P14

Domin samun complete litattafanmu, ku yi following É—in wannan accounts É—inkin a Arewabooks

https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949

https://arewabooks.com/u/nimcyluv
https://arewabooks.com/book?id=

Elegant online writers

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.

Kamar wanda aka tsikara ya yi saurin janye fuskarsa ya fasa yin abun da ya yi niyya, gyara mata mayafin jikinta ya yi ya ciccib'e ta ya miƙe tsaye da ita a jikinsa. Mutumin nan da Salman ya hankaɗe shi bai daddara ba ya ƙara matsowa da niyyar ya taimaka masa su riƙe Abra tare, a matuƙar kufule Salman ya kai masa duka da ƙafa, saurin ja baya ya yi cikin mamakin ƙarfin halin yaron da taurin zuciyarsa. Wata muguwar harara Salman ya cilla masa tare da yin ƙwafa sannan ya yi gaba da sauri ya nufi Motarsu.
Chapter 33 · 0% Book details