← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 145

Sashe 128

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya ce "Wannan yaron ba abin tausayi bane, gara a bari ya ɗanɗana kuɗarsa, kuma sati mai zuwa zan karɓawa Salman Auren Afra a wurinka, idan har zaka mini kara, Salman ɗana ne"
Cikin hanzari Abbi ya janyo hannun Abba, zuwa waje ya ce "Duk laifin da yayi bai cancanci wannan horon ba, magana fa ake ta rayuwarsa".
Abba ya ce "Amma dai ka san Aurensa da Afra ba abu ne mai yiwuwa ba ko? Alhalin ga Salman".
"Na sani, amma sai a tausayawa halin da ya tsinci kansa a ciki, koma wani irin laifi ya aikata maka, bai kamata ace ka ɗau wannan zafin ba, har ka nesanta shi da tausayawarka ba, haba Alhaji Aliyu, ka zafafa da yawa, akwai buƙatar ka sassauta masa haka"

Abba ya girgiza kai ya ce "Ba zaka gane bane Major, halin da Adnan yake ciki, dai-dai da shi ne, shiya janyowa kansa".

Abbi ya ce "Ba ina son jin laifin da ya aikata maka bane, ina nema masa alfarma ne, dan Allah dan Annabi, a sassauta masa a duba halin da yake ciki, ka rage wannan fushin da ka ke da shi".

Abba ya ce "Na ji, amma ni yanzu babbar damuwata shi ne, ba zan bar garin ba, sai Mutumin nan ya dawo, mun cinma matsaya, na tabattar da abin da Adnan yake faɗa, gaske ne ko kuma ƙarya yake yi".

"Haba Alhaji Matawalle, ga gidana mai zai sa kaje ka kama hotel ka zauna, idan ma ba zaka zauna a gida na ba, akwai guest house É—ina, sai kaje can ku zauna, mu jira zuwan mutumin, Allah dai ya sanya mu ji alkhairi".

Afra sai koke koke take yi, gaba ta ma rasa kukan me take yi ne? Damuwa da halin da Adnan yake ciki? Ko kuma farincikin an san waye mahaifinta? Bana wannan ba, ai haryanzu lalube ake a cikin duhu, ba tare da an tabattar da sahihancin cewar wanda Adnan ɗin ya ambata shi ne mahaifinta ba, wataƙila ma ƙarya yake mata, kamar yadda ya yi mata ƙarya a ƙauye.

Kwanakin Adnan uku a Asibiti, ya ɗan farfaɗo jikinsa da sauƙi, Afra taje duba shi sau ɗaya yana bacci, ya yin da Salman kuwa, sai da Mami ta haɗa masa da zagi, sannan ya yadda yaje duba Adnan, duk da a ƙule yake da Adnan, amma ya tausaywa yadda ya ga Adnan ɗin ya koma.
Akwa abubuwa da yawa da Salman ba zai taɓa mantawa da su ba a rayuwarsa, daga shigowar Adnan rayuwarsu, ya rusa musu farinciki, zuwa ga mutuwar Abra, ba zai taɓa manta lokacin da a gaban idonsa, Adnan ya mari Abra ba dan kawai ta ce tana son sa, da ya tuna ire-iren wannan abubuwan da suka faru, sai tsanar Adnan ta ninku a zuciyarsa, ban da zuciyar musulunci, da kuma yadda Mami ta dage da babu abin da zai sanya ya zo duba Adnan. Kuma a wannan karon ya ƙudirce a zuciyarsa ko mai za ayi, ba zai barwa Adnan Afra ba, a wannan karon Afra tasa ce.

Wasa-wasa, sai da Bulama ya kwana biyar a Dubai, sannan passport ɗin Rumaisa ya zama ready, gaba ɗaya a kwanakin nan, banda aikin rarrashinta babu abin da yake yi, kullum cikin kuka take, ga gefe guda Saudat ta uzzura masa da kira, ƙarshe sai kashe wayarsa ya yi gaba ɗaya.
Ranar Asabar, Bulama da Rumaisa tare Abdallah suka sauka a Nijeriya, a garin Kaduna, sai dai a guest house É—in sa na Kaduna suka sauka, saboda baya son wani dalili ya sanya wani ya san da cewar, sun sauka da Rumaisa a Nigeria.
    Lambar Adnan Bulama ya duba, ya kira shi, sai dai sam Adnan ya ƙi bawa kiran mahimmanci balle ya ɗauka, kasancewar yana tare da su Abba a guest house ɗin Abbi, Yana kwance a falo, Hajiya Mama na gefensa tana jan carbi, ta ji wayar Adnan ta cika mata kunne, amma ba shi da niyyar ɗaukar wayar.
"Adnan ba wayarka ce take ringing ba"
Cikin numfarfashi na marasa lafiya, Adnan ya ce "Mama I can't pick it".
Mama ta miƙa hannu ta ɗaga wayar, cikin nutsuwa Bulama ya yi sallama, Mama ta amsa suka gaisa, Bulama ya ce me wayar yake nema.
Mama ta ce "Bashi da lafiya, yana kwance"
Bulama ya ce "Subhanallah, Allah ya bashi lafiya, dama nine Yusif Garba Bulama, wanda aka ce yarana na wurinku".
Mama ta ce "Ahh, Allah sarki, ka dawo garin ne?"

"Eh mun dawo, naje na taho da mahaifiyarsu ne, dan mu samu a tabattar idan yaran namu ne"

Mama ta ce "Alhamdilillah, muna nan Kano dama ku muke jira, da ka ce tun a washegari zaka zo".

"Eh, an tsaya gyara passport É—in mahaifiyarsu ne, insha Allah gobe in Allah ya kaimu, da wuri zamu taho, sai a bani Address É—in in da zamu zo".

Mama ta tashi, taje ta kaiwa Baba waya, suka sake yin magana da Bulama, ya yi masa bayanin Adress É—in.

Washegari, wajen ƙarfe goma sha ɗaya na rana, Abba ya shigo ɗakin da Adnan yake ya ce "Ka tashi ka shirya, muje mu tari Mutanen nan, sai ka tabbatar mana da dalilin da yasa kace shi ne mahaifinsu, kuma ka gaya musu da ka auri 'yar su me kayi mata, da kuma dalili da ya sanya ka san in da mahaifin na su yake, amma ka ƙi faɗa da wuri". Marairaice fuska Adnan ya yi zai yi magana, amma Abba ya dakatar da shi ya ce "Kar ka gaya mini komai, ka tashi mu tafi, mutumin banza kawai, ai kai ba abin tausayi bane"
Jiki ba ƙwari haka Adnan ya kammala shiryawa, suka tafi gidan su Salman.
Suna zazzaune a falo, suna jiran zuwan su Bulama, Little da tuni ta fara rarrafe, ta na jikin Adnan tana wasa, ta ja masa gemu, ta ja masa gemu, yana kallonta yana murmushi, lokaci lokaci yana share ƙwalla.

Ko da Afra ta fito falo ta yi tozali da Adnan sai da gabanta ya faɗi, yayi rama tamkar ba shi ba duk yayi wani iri, gashi yadda numfashinsa ke fita ma zai ƙara tabattar maka yana cikin mawuyacin hali.

Kallo ɗaya yayi mata ya kauda kansa, ya cigaba da yiwa Little wasa, yana share hawaye, gaba ɗaya sai jikin Afra yayi sanyi, ko ba komai mijin 'yar uwatta ne, abin da tayi na nuna masa ƙiyayya, bai kamata ba, amma ba yadda zata yi, dan ita tafi son Salman a kansa.

Abbi ne ya shigo tare da Abba ya kalli Mami sannan ya kalli Afra ya ce "Afra tashi ki koma ɗaki, make sure baku bari ta fito ba, sai mun gama tattauanawa, gasu can sun ƙaraso" Afra tana ji tana gani, aka kaita ɗaki aka rufe.

Abbi ne ya yiwa su Bulama jagora, zuwa cikin katafaren falon gidan Major.

Rumaisa sai rarraba ido take yi, Mami ta tsurawa Rumaisa ido, a ranta ta ce "Tsarki ya tabbata ga Allah, su Abra dai 'ya'yan balarabiya ne".

Abdullah ya kalli hoton falon, cikin harshen larabci ya ce wa Rumaisa "Ai wannan ita ce yarinyar da nake baku labari, na haÉ—u da ita karo biyu".

A gigice Rumaisa ta nufi hoton, tana ta larabci, ba komai suke ganewa a maganar ta ta ba, saboda kukan da take yi, da ƙyar Bulama ya rarrashi Rumaisa, su Abbi suna ta rarrashinta cikin harshen turanci.
Tabbas babu wanda zai kalli matar nan ya ce ba ita ta haifi su Abra ba.
Har ta zauna ta miƙe a gigice ta nufi in da Adnan ke zaune yana binta da ido, dan hatta yanayin rikicewarta tana kuka tamkar Abransa.

Little ta ɗauka ta ƙanƙame, tana cewa Bulama wannan ma 'yar ta ce.

Cikin harshen turanci Bulama ya ce "Ta yaya wannan zata zama 'yar ki, bayan 'ya'yanki sun kai aƙalla shekaru ashirin da huɗu".

"To ina yaran nawa suke?" Ta tambaya tana zubar da hawaye, tare da sumbatar Little, duk ƙyuyar yarinyar amma ba ta yiwa Ummi ba, saima kallonta da take tayi.

"Bayani za ai miki ai, amma ki zauna"

Da ƙyar Rumaisa ta zauna, aka gaggaisa aka kawo musu ruwa, aka samu Rumaisa ta ɗan nutsu, sannan Abba ya kalli Adnan ya ce "To ka san dai kai ne silar taruwarmu a nan, dan haka saika warware mana abin da ka ƙulle a ranka, kayi da turanci yadda zata fahimta".

Adnan ya ɗan yi jimmm, sannan yai ajiyar zuciya, jiki a sanyaye idonsa fal ƙwalla ya fara bada labarin abin da ya faru.
Ya fara da irin soyayya da shaƙuwar da ke tsakanin sa da mahaifiyarsa, har zuwa lokacin da ta rasa ranta a sanadin Sakaci da son abin duniya na Bulama.

Ya cigaba da bada labari, yadda ya rayu, da kewar rashin mahaifiyarsa har zuwa ranar da ya raka Usman gidan Bulama wurin Meenal, da hoton Bulama da ya gani, da fari a kan Meenal ya so ya aura, kuma ga Usman, katsam da yaje Kano, ya haÉ—u da Abra. Nan ya basu labarin yadda ya je har Yola, garin su Bulama samun bayanai a kansa, a nan ya tabattar da Abra 'yar sa ce.

Rumaisa ta ce "Ita ba ta fahimta ba, wacece Meenal da ake magana a kanta, kuma wane Asibitin ake magana ba ta gane zancen ba?!

FARKON LABARI

YUSUF GARBA BULAMA É—an asalin garin Adamawa ne cikin Yola

NA KUÆŠI NE, A BIYAMU HAKKINMU KAN A KARANTA
08081012143
[11/23, 12:57 PM] Abk: Su biyu kacal iyayensu suka haifa, daga shi sai ƙanwarsa Murja. Sun taso cikin kulawa da soyayyar iyayensu, duk da ba masu ƙarfi ba ne sosai amma suna da rufin asiri daidai gwargwado, kuma babu abin da suka nema suka rasa a rayuwa. Yusuf ya kasance mutum ɗan gayu, mai son rayuwar ƙarya da sabgar masu kuɗi. Tun yana karami Mahaifinsa Garba Yusuf Bulama ya fahimci wannan halin nasa, hakan ya sa kodayaushe cikin masa nasiha da nusar da shi ya tsaya a duk inda Ubangiji ya ajiye shi a rayuwa yake. Yusuf ya kan nuna kamar ya ɗauki maganar mahaifinsa, amma cikin ransa ƙara burika ma yake yi, addu'ar shi da burinsa a kullum Allah ya sa ya zama shahararren mai kuɗi, wanda za a dinga kwatance da shi saboda kuɗinsa.
Chapter 128 · 0% Book details