← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 145

Sashe 69

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami 'yan biki sun watse, sai wanda ba'a rasa ba.
Tayi wanka tana ƙoƙarin shiryawa, ta ga wata takarda ta faɗo daga cikin wardrobe ɗin ta.
Ta sunkuya ta É—au takardar ta buÉ—e, rubutun Salman ta gani a jiki, hakan ya sanya ta sake gyara tsayuwarta ta fara karantawa.
*Assalamu alaikum warahmtullah. Ina fatan lokacin da saƙon nan zai riskeki kina cikin ƙoshin lafiya Mamina. Na san zakiyi mamakin ajiye miki wannan takarda da nayi, amma ba abun mamaki bane, duk da ba zan kira hukuncin da kika yanke a kaina kuskure ba, amma zan iya kiransa da shamaki da farinciki na, ta hanyar nisata ni da abu mai daraja da nake matuƙar ƙauna. Domin sake nesanta kaina da Abra kasancewar na san mallakin wani zata zama, ina mai sanar miki da cewa daga ranar da na bar Nigeria ba zan sake dawowa ba har Abad, dan muddin ina Nigeria, ruhina yana tare da Soyayar Abra, dan tabbatar da samun farincikinki da nutsuwar ki, ba zan sake dawowa Nigeria ba. Idan kuma kika yi ƙoƙarin tursasa sai na dawo, zan bar China in koma ba im da ba wanda ya sani. Ki huta lafiya Mamina, ki gaishe mini da Abra tare da yi mata fatan Alkhairi a rayuwar Aurenta. Salman Khamal Khamis*.

Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143
[10/11, 7:20 PM] Abk: Take jikin Hajiya Na'ima ya ɗau rawa, hannunta ya fara karkarwa, ta nemi guri ta zauna a gefen gado, wani irin gumi yana tsatstsafowa a goshinta, a hankali ta furta "Na shiga uku, mai yaron nan yake nufi dani ne?" Cikin azama ta miƙe, ta ɓoue takardar ba tare da ta nunawa kowa ba.

Sai ƙarfe takwas na safe sannan Adnan ya shigo gidan, shi ma bai shigo inda take ba, maganarsa ta jiyo a parlour suna gaisawa da waɗanda da suka kawo ta, hakan ya sa ta fita parlour'n da sauri, zuciyarta cike da ɗokin ganin shi.

Gaishe shi ta yi, sarari ya ji ta amma ya É—auke kai kamar bai ji ba, hakan ya faÉ—ar mata da gaba. Amma dai ta daure suka yi sallama da waÉ—anda suka kawo ta, har da kukanta lokacin da suka fice daga parlour'n.

A tunaninta bayan fitar su Aunty Suwaiba Adnan zai taho gare ta cikin zumuɗi ya rarrashe ta, amma sai ta ga saɓanin haka. Ƙafa ya ɗora ɗaya akan ɗaya yana latsa wayarsa, tamkar bai san da halittar ta a parlour'n ba. Cikin tsananin shock Abra ta ce. "Baby! Me yake faruwa ne? Jiya ba ka dawo ba ka bar ni na kwana ni kaɗai cikin jin tsoro, yanzu kuma ka dawo amma ka yi kamar ba ka ganni ba." Tamkar da dutse take magana, ko motsi bai yi ba da sunan ba ta amsa. Ƙura masa ido ta yi tana kallon shi cikin mamaki, Adnan ɗinta ne kuwa wannan ko an canza mata wani? Adnan ɗin da ya ci burin ganin wannan ranar da za ta kasance a gidansa, amma me ya yasa ya yi mata haka? Me yasa tana yi masa magana ya share ta? Ko dai something bad happened to him? Tunanin hakan ya sa ta matsawa kusa da shi da niyyar ta ji abun da yake damun shi. Wata uwar harara da ya ɗago kai ya banka mata yasa ta tsayawa cak a inda take cikin bugawar zuciya. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un." Abun da ta ambata a fili kenan. Rasa abun yi ta yi hakan ya sa ta koma ɗakinta cikin sauri, faɗawa kan gado ta yi tare da sauke wani wahalallen numfashi. So take ta tuno ko ta yi wa Adnan wani lefin amma ta kasa, hakan ya sa ta fashewa da kuka. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskarta. Bayan ta fito ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta, cikin ƙoƙarin son gano ko wani abun Adnan ya gani a jikinta da bai masa ba, amma ba ta ga komai ba. Duk da ita ba ma'abociyar son kwalliya ba ce amma haka ta zage ta tsantsara ta tare da kafa ɗaurin ɗankwali mai kyau, ita kanta ta san ta yi kyau, duk da yanda take jin wata irin fargaba a cikin zuciyarta amma sai ta murmusa, ta san dole kwalliyar tata ta burge Adnan. Daddaɗar humra mai daɗin ƙamshi ta shafe jikinta da ita, sannan ta fita zuwa ɗakin Adnan. Sai da ta fara shiga kitchen ta haɗa masa breakfast wanda aka ajiye dan shi sannan ta nufi ɗakin nasa. A zaune ta tarar da shi a kan gado yana operating system. Cikin sanyin jikinta ta yi masa sallama, ko d'agowa bai yi ba balle ya amsa mata. Hakan ya ƙara tsinkar mata da gaba, zuwa yanzu kam ta gane da akwai matsala. Kanta a ƙasa ta ce. "Ga abinci." Nan ma bai kula ta ba, kawai sai ta fashe da kuka cikin rashin sanin abun yi. Ta daɗe a duƙurshe tana kuka mai tsuma zuciya, yana jin ta amma ko tari bai yi ba, ƙarshe ma tashi ya yi ya ɗauki car key ya fice ya bar mata gidan. Hasbunallahu..... kawai Abra take maimaitawa, a ranta tana tambayar kanta me yake shirin faruwa da ita ne? Me Adnan yake nufi da ita? Jiki a saɓule ta miƙe ta koma ɗakinta ta kwanta akan gado ta cigaba da kukanta, kewar Faris da Abbi da Mami na nuƙurƙusar zuciyarta, wani azababben ciwon kai ne ya far mata lokaci ɗaya, cikin dauriya ta janyo bargo ta lulluɓe jikinta, saboda yanda take jin wani sanyi na ratsa gaɓoɓin jikinta, tamkar wadda za ta yi zazzaɓi, a haka wani wahalallen bacci ya ɗauke ta.

Sai Azhar ta farka, shi ma ƙarar doorbell ya tashe ta, cikin sauri ta miƙe ta shiga toilet ta wanke fuskarta da ruwa sannan ta fito ta saka hijabi ta fita. Mata ne kusan su takwas ta gani, cikin fara'a ta tarɓe su tare da yi musu iso. Bayan sun zauna sun gaisa ta kawo musu drinks da kayan garar ta, anan suke gabatar mata da kansu. Dukkansu cousins ɗin Adnan, Ƴanmata shida sai matan aure biyu. Ta ji daɗin zuwansu ba kaɗan ba, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa suka yi ba. Sai dai duk bayan sakanni idan ta tuna Adnan da yanayin da ya nuna mata ɗazu sai gabanta ya faɗi. Da abinci suka zo, hakan ya sa ba ta yi girki ba shi suka ci, ita ɗan caccakalar abincin ta yi kaɗan ta ci ba don daɗi ba. Sai kusan Magriba suka tafi suna ta tsokanar ta wai kar Ango ya dawo ya same su ya yi musu korar kare, ita dai murmurshin yaƙe kawai take, sai ta ji dama kar su tafi.

Ba ta zauna ba sai da ta tsaftace gidan ta saka turaren wuta a burner, hakan ya sa gidan gabaɗaya ya karaɗe da ƙamshi. Bayan ta yi Sallah ta yi wanka ta shirya cikin wani tsadadden yadi mai kyau maroon color, ya yi mata sosai ya haska farar fatarta. Parlour ta fita ta jera abinci akan dinning sannan ta koma ta yi Sallar Isha'i da aka fara kira. Tana idarwa ta janyo wayarta dan ta kira Abbi amma ta tarar wayar a kashe, ta manta tun jiya wayar babu chaji ta mutu. Chajin ta jona ta zauna jiran ya ɗan yi, Salman ne ya faɗo mata a rai. A fili ta ce. "Kana ina My Faris? Me kake yi yanzu? Me ya sa ba ka kira ni ba tunda ka tafi? Yaushe zaka dawo ka zo gidana in gan ka ɗan ƙanina? Na yi tsananin kewar ka." Daga haka ta fashe da kuka.

Khamal na zaune a parlour'nsa shi da Na'ima wadda zuciyarta ke cike da tsananin farinciki, jin ta take kamar a mafarki yau Allah ya yi Abra ta bar mata gida, shikenan fargabarta ta ƙare. Sai dai tuno letter Salman da ta gani ya sa gabanta fad'uwa da ƙarfi, ta rasa me ya sa abun ya dame ta? Dan da farko shirme ta ɗauki abun, saboda sanin komai daren daɗewa dole Salman ya neme su, ba kuma zai taɓa iya yin zuciya da su ba, letter da ya yi mata dan yana cikin ɓacin rai ne, abun yana cin shi a lokacin shi ya sa, amma ta san idan tafiya ta yi tafiya komai zai wuce. Khamal yana duban ta ya ce. "Komai lokaci ne, kamar ba yau ake zancen bikin Daughter ba, ga shi har an yi an gama, ta tafi ta bar mu da kewar ta. Cikin kissa Na'ima ta ce. "Ta bar mu da kewa kam, don gidan babu daɗi yanzu ko kaɗan, ga ba Salman." Khamal ya nisa ya ce. "Har kin tuna mini kuwa, na kai sati ina trying his number ba ta shiga, amma na kira mutumin da ya kira ni da numbern shi lokacin da ya sauka a garin, ya ce mini neighbours suke, idan sun haɗu zai kira ni ya haɗa mu." Murmushi Na'ima ta yi ta ce. "Allah Sarki yaron kirki, Allah ya tsare mana shi." Khamal ya amsa da Amin tare da zaro wayarsa daga aljihu ya kira layin Abra amma sai aka ce masa a kashe, tun rana yake kira ta ba ta shiga. Numbern Adnan ya kira, dan ya san duk sabon ango i yanzu yana gida. Bayan ya ɗaga suka gaisa cikin mutuntawa, Khamal ya tambayi Abra, Adnan ya tabbatar masa tana nan ƙalau, wayarta kuma babu caji ne shi ya sa bai same ta. Khamal ya buƙaci Adnan ya ba wa Abra wayar, sai ya ce ya ɗan fita, idan ya koma gidan zai haɗa su, daga haka suka yi sallama.
Chapter 69 · 0% Book details