← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 145

Sashe 134

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya ce "Ku kuka tsaya biye ta tasa, Salmanj kawo takarda ya saketa ta huta" aikuwa Salman ya zaro jotter da biro ya miƙo, tabbas da Adnan na kusa da Salman ba abin da zai hana ya fasawa Salman baki.
Abba ya wurgo masa takardar ya ce "Saketa maza, daga nan ta wuce Dubai  wurin mamanta, ta huta itama"
"Dan Allah Abba kayi haƙuri, ba zan iya ba"

  Wayar Bulama tayi ringing babu adadi, ya ɗauko wayar a hasale ya ɗaga wayar.
"Gwamnati ta rufe maka Asibitinka, kuma an turo maka sammaci daga kotu, an kai ƙararka da Asibitinka"
[11/28, 8:05 PM] Abk: Muryar wani mutum ta doki dodon kunnansa a kausashe da faÉ—in haka. Rarraba ido ya fara yi cikin rawar murya ya ce. "Ban gane ba, wa..wake magana?"

"Ba ka da buƙatar sanin hakan, kai dai kawai ka amsa kiran kotu, an je gidanka har sau uku ba ka nan, shi ya sa muka nemi lambar wayarka don mu sanar maka, takardar sammacin tana hannun mai gadinka."
Daga haka aka katse kiran. Gumi ne ya shiga tsatstsafowa a jikinsa duk da ac dake parlour'n, gabaɗaya mutanen gurin kallon shi suke cikin neman ƙarin bayani. Taɓe baki Ummi ta yi cikin harshen turanci ta ce. "In dai bala'i ne yanzu ka fara ganin shi a cikin rayuwarka Yusuf, tunda ka fifita kuɗi fiye da komai a duniya, ciki har da tsoron Allan ka. Ka zaɓi rayuwar cin zali da rashin tausayi ga wanda ba shi da shi, a garin hakan har mutumin da ya riƙe maka ƴarka ya mutu, wallahi ka yi asarar rayuwarka." Ta yi maganar cikin tsantsar ɓacin rai da tsanar shi. Girgiza kai Abba ya yi cikin Dattaku ya ce. "Yanzu me ya faru? Me aka ce maka a wayar?" Cikin raunin murya ya ce. "Daga court aka kira ni, an kama asibitina tare da turo mini takardar sammaci."

"Subhanallahi, Ubangiji ya kawo maka mafita."
Abbi ya faÉ—a cikin tausayawa

Hawaye Bulama ya fara tare da faɗin. "Ko me ya faru da ni, ni na janyo wa kaina, na biye wa son zuciyata na yi ta aikata kuskure, duk da na san hakan ba daidai ba ne, Ubangiji kuma ya yi ta ba ni nasara, fiye da shekara ashirin ban taɓa fuskantar wani ƙalubale akan abin da nake aikatawa ba sai yanzu komai ya rincaɓe mini." Ya nisa sannan ya cigaba da magana. "Na rasa matata mai ƙaunata da ta ba ni dukkan yardarta, sannan na rasa soyayyar Ƴaƴana waɗanda duk duniya babu abin da na ji ina so sama da su a yanzu. Tabbas bahaushe ya yi gaskiya da ya ce. "Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya tak ta mai kaya."

Wani mugun kallo Adnan ya wurga masa cikin tsana, ko kaɗan bai ji tausayin shi ba, sai ma takaicin shi da ya ƙara cika zuciyarsa, saboda shi ne Ummul aba'isin duk abubuwan da suka faru. Kasa magana kowa ya yi, Abra Sarkin kuka sai hawaye take yi, zuciyarta ta karye, wani irin tausayin mahaifinta ya cika mata zuciya. Miƙewa Bulama ya yi ya kalli Ummi da su Afra ya ce. "Zan tafi cikin baƙin cikin tsana na da nake gani kwance akan fuskokinku, amma don Allah ina roƙon ku alfarma guda ɗaya, ku yafe mini, ku kuma kasance masu yi mini addu'a, domin na san da ƙyar mu ƙara haɗuwa, saboda abubuwan da na aikata na cancanci zaman gidan kaso na har abada, kotu za ta iya yanke mini hukuncin ɗaurin rai da rai." Kawar da kai Ummi ta yi cikin ƙoƙarin danne tausayin shi da ya taso mata, duk da cikin harshen Hausa ya yi maganar amma yanayin da yake ya karyar mata da zuciya. Tashi Abra da ta fi su raguwar zuciya ta yi ta rungume shi tare da fashewa da kuka. Duk lalacewar Uba, Uba ne, kuma hannunka ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar. A hankali Afra ta tashi ta ƙarasa ta janye Abra, cikin ɗacin zuciya ta ce. "Wannan mutumin ba abun tausayi ba ne, kar ki bari wannan kalaman yaudarar tasa da marairaicewar da ya yi su yi tasiri a zuciyarki, domin shi bai san hakan ba ga al'umma, wallahi ba zan taɓa yafe masa mutuwar da Babana mai ƙaunata ya yi ba saboda shi, taho mu bar kusa da shi kar baƙin....."

Da sauri Abra ta toshe mata baki da hannunta tare da girgiza mata kai ta ce. "Ki daina faɗar haka ƴar'uwata, duk lalacewar shi mahaifinmu ne, shi ya yi sanadin kawo mu duniya, ko da kowa ya ƙi shi bai kamata mu ƙi shi ba, kar ki manta da Uba ake ado, a lokacin da ba mu san shi ba muke cikin ƙishirwar ganin shi addu'a muke ko yaya yake Allah ya nuna mana shi, yau ga shi Ubangiji ya amsa addu'armu, bai kamata kuma mu butulce masa ba. Wannan halayyar tasa ƙaddararsa ce a haka da mu baki ɗaya, Ubangiji ya riga ya rubuta duk abin da ya faru sai ya faru, babu yadda za mu yi." Ta ƙarashe maganar cikin kuka mai taɓa zuciya. Rungume ta Afra ta yi cikin hawaye, kalaman ƴar'uwar tata sun tsinka mata zuciya. Babu wanda tausayin su Abra bai ratsa wa zuciya ba a gurin, musamman Ummi da take ganin kamar ita ce ba ta zaɓa musu Uba na gari ba. Kan Bulama a ƙasa cikin tsananin jin kunya da nadama ya fice daga parlour'n cikin harɗewar ƙafa tamkar mai koyon tafiya, Abra da Afra suka raka shi da ido cikin wani irin yanayi. Tasowa Ummi ta yi ta rungume ƴaƴanta suka cigaba da kukan a tare.

Bayan sun nutse sun yi shiru Baffa da tun ɗazu bai ce komai ba sai nazartar kowa da yake ya gyara zama ya ce. "Alhamdulillah komai ya yi farko zai yi ƙarshe, kuma komai na rayuwa nan mai wucewa ne. Tashin hankali da rashin nutsuwar zuci da Yusuf Bulama ya tsinci kansa a ciki ya ishe mu ishara da sauran masu irin halayyar shi. Allah ya sa mu dace, ya sa mu fi ƙarfin zuƙatanmu." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Abba da bai manta da batun sakin Abra ba ya dubi Adnan ya ce. "Yanzu kai kaɗai muke jira, ka ba mu takardar sakin Abra." Kuka Adnan ya fashe da shi zai yi magana Abba ya ɗaga masa hannu tare da faɗin. "Idan har ba ka yi abin da na umarce ka ba a yanzu to ka sani babu ni babu ka..."

"Ashsha! Me ya yi zafi haka Alhaji? Duk abin bai kai haka ba, abi komai a sannu. Saki ai ba shi ne mafita ba, Ubangiji ma da ya halatta a yi shi ba ya son a yi shi, yanzu a bar wannan maganar don Allah, na roƙi wannan alfarmar, a taimaka a yi mini ita."
Baffa ya katse Abba da faÉ—in haka.

"Amma Baffa da ka bari ya sake tan, tunda yarinyar ita ma ba ta son shi a yanzu."

"Idan ba ta so babu mai yi mata dolen sai ta koma, amma abun da nake so a ba ta lokaci ta huta ta yi tunani, idan har lokacin da aka ba tan ta ce ba ta son shi ni da kaina zan karɓar mata takardar saki a hannun Adnan. Don mu sulhu muke so ba ɓatawa ba."

Cikin gamsuwa Abbi ya ce. "Haka ne, na gamsu da bayaninka sosai Baffa, a ba ta lokacin, ko dan darajar yarinyar dake tsakaninsu." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Adnan ya sauke ya cillar da jorter da pen ɗin hannunsa ya rarrafa gaban Baffa ya dinga kwarara masa godiya.

Murmushi Baffa ya yi ya shafa kan Adnan ya ce. "Ba komai yaron kirki, kai dai ka dage da addu'a da kyautata mata, hakan zai taimaka gurin kankare mikin da ka yi mata a cikin zuciyarta." GyaÉ—a masa kai ya yi idonsa a kan Abra, wadda ke wurga masa muguwar harara.

"Yanzu tsawon wanne lokaci za a ba ta kafin a ƙara jin ta bakinta?"
Abba ya tambaya.

"A ba ta wata guda."

"Shikenan Allah ya kai mu lafiya, amma kafin lokacin ina son a yi bikin Salman da Afra."

Dam zuciyar Abra ta buga, Faris ɗinta ne zai auri ƴar'uwarta? 'Ya Allah.' ta faɗa a cikin zuciyarta tare da yin ƙasa da kanta cikin wani irin yanayi na karayar zuci. Salman dake lura da ita ya sauke numfashi, so yake su haɗa ido amma ta ƙi ɗago kanta.

"Please ku bar maganar auren nan? Ku ba ni na tafi da ƴaƴana can ƙasata." Ummi ta faɗa cikin hawaye.

"Babu mai hana ki Ƴaƴanki duk duniyar nan, amma tunda suna son junansu ita da Salman ki bari a ɗaura auren sai ku tafi dukanku har shi, mun san kin yi haƙuri na zaman da kika yi a nan tsawon lokaci, ga ƴan'uwanki suna ta son ki koma don su gan ki dake Ƴaƴanki, amma ki ƙara wani haƙurin, ana ɗaura auren da sati biyu insha Allahu za ku tafi."

Tana ganin mutuncin Baffa sosai kuma ba za ta iya jayayya da shi ba, kallon Uba take masa tunda ya haife ta, hakan ya sa ta ce masa ta amince. Tashi suka yi suka bar iya su Abbi a parlour'n suka ƙara tattaunawa, sun tsayar da lokacin bikin sati uku masu zuwa. Su Abra sun fito suna yi wa Abba da su tafi sallama Adnan ya kafe ta da ido, duk da tana jin kaifin idonsa a jikinta amma ta ƙi kallon inda yake. Ganin hankalin su Abba ba ya kansu Salman ya ƙaraso ya kama hannunta.

"I'm sorry my angel."

Ya faÉ—a kamar zai yi kuka.

Ƙasa ta yi da kanta ba ta ce komai ba, damƙe hannunta ya yi a cikin nasa cikin raunin murya ya ce. "Ban yi zaton zan ƙara ganin ki ba a rayuwata, na sha wahala sosai dalilin rashin ki, daga baya Ubangiji ya sako mini dangana na haƙura, duk da soyayyar ki tana nan a cikin zuciyata ko ɗigo ba ta ragu ba. Shigowar Afra cikin rayuwata ya warkar da duk mikin rashin ki a cikin rayuwata, saboda ganin na samu madadin ki." Murmushi Abra ta yi cikin ƙarfin hali ta ce. "Wannan bayanin duk na mene ne bro?"
Chapter 134 · 0% Book details