Sashe 110
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
08081012143
[11/7, 6:36 PM] Abk: Ganin da tayi ya miƙo hannayensa gaba ɗaya zai ɗagota tsaye, ya sanya ta daddage ta ƙwala ihu "Wayyo Allah na shiga uku mahaukaci" tsayawa yayi sororo yana kallonta, ta tashi cikin hanzari ta suri farantin gyaɗar ba ta tsaya ta bia ta kan gyaɗar da ta watse ba, ta fyalla da gudu kamar ba zabgegiyar budurwa ba, binta Adnan ya yi yana kiran "Abra, dan Allah ki tsaya ki ji" sai dai kan kace Kobo, ta ɓace ɓat a cikin gonaki.
Dawowa yayi, wurin da gyaɗar ta ta watse a ƙasa, ta bar mayafinta a wurin, ya durƙusa ya ɗauka yana jujjuya mayafin, take hawaye ya cika idonsa "Angel, Allah ya sa ba gizo kike mini ba, ko dai haukacewa na yi ne ban sani ba? Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya daɗe a wurin a tsaye, sanan ya shiga motarsa ya ja ya cigaba da tafiya, ji yake tamkar an zare masa lakar jikinsa, ya rasa duk wani kuzarin sa.
Ya samu ƙasan wata bishiyar tsamiya, yayi parking ya kifa kansa a kan sitiyarin motar, ya shiga duniyar ta sa ta tunani, da hasaso lokutan da suka shuɗe wanda ya kasance tare da Abra.
Haka ya ɓata lokaci a wurin, yana ƙara rirriƙe mayafin yarinyar nan mai gyaɗa, yana son tabattar a zahiri Abra ya gani, ko mai kama da ita ce kawai, ko kuma dai duk gizo ne?
Ganin ba shi da mai ba shi wannan amsar ne, ya sanya ya fito daga motar ya tambayi wasu samari, gidan maigari, suka kwatanta masa yayi musu godiya ya koma motarsa.
 Tunani ya dinga yi ya aka yi bai tsaya ko sunanta ya sani ba, to ta yaya ma zai san sunanta yarinyar da ko tsayawa ba ta yi ba ta kwasa da gudu.
"No my Angel can't run like this, sje might be her ghost, or am just hallucinating" ya yi maganar a fili yana taune leɓensa na ƙasa.
Gaba ɗaya Hajiya Na'ima ta rasa me yake mata daɗi, duk ta birkice ta fita hayyacinta jin batun kishiyar nan, gashi Abbi ya sa ana ta gyaran gida, zai ƙara Aure, kuma duk wannan haukan da take, ko kallo ba ta ishe shi ba, balle ya bi ta kanta, sabgar Aurensa ce kawai a gabansa sai jikarsa Aishatul Humaira.
 Na'ima na zaune a ɗakinta, tana rungume da Little Abra, sai dai gaba ɗaya hankalinta ba ya jikinta, she can't imagine sharing her husband with a prostitute.
Sallamar Abbi a É—akin ce ta dawo da ita hayyacinta, ba ta amsa masa ba, kuma ba ta kalli in da yake ba.
Ya ƙaraso yana yiwa little murmushi, ya yin da ita kuma take ɗan murmusawa har dimples ɗinta suna lotsawa, haryanzu ba ta da wayo sosai, dan baka ba ta wani gane wasa, amma duk in da ta ga Abbi, tana yawan bin sa da idanunta, ko ma ta ɗan dinga yi masa murmushi.
Abin har mamaki yake bawa Na'ima, dan Aishatul Humaira ba ta yi wayon gane wasa ba, amma tana gane Major.
Ya miƙa hannu zai ɗau Little, amma Naima ta ƙanƙameta a jikinta tana watsa masa wani mugun kallo.
"Ya haka? Ki bani yarinyata in gani".
"Ba zan bayar ba, ka fita sabgata da ni da yarinyar nan, ka je ka yi rayuwarka mu yi ta mu".
"Hmm ikon Allah, madam kenan, har kin manta jikar karuwa ce Humaira?".
"Kar ka ƙara danganta mini 'ya da karuwa".
"Ohh sorry, ai ba ni na fara faÉ—a ba, ke ce ki ke faÉ—a, ko har kin manta Abra 'ya ta ce da karuwa ta haifa mini?"
Wata irin nadama da dana sani ne suka ziyarci Na'ima, ta tafka kuskuren da lokacin gyara ya ƙure mata.
"Kinga gara in kawo kakarta, ta kula mini da ita yadda yakamata, kar ƙiyayyar da ki ka nunawa uwatta ya shafeta ita ma".
"Ka ce mini ba zaka yi aure ne dan ka hukunta ni ba, amma wannan ƙananun maganganun da kake na menene?"
Bai amsa mata ba, sai murmushi da ya yi. Ya kuma miƙa hannu zai ɗau Little.
"Khamal ka ƙyaleni ka rabu da ni na gaya maka, idan duniya zata haɗu babu wanda ya isa ya rabani da jaririyar nan, kuma Wallahi ko ma wace tsinannaiyar zaka auro, babu ita ba Little, ka ƙyaleni ka rabu da ni".
Major ya ce "Allah ya baki haƙuri, zaki tsorata yarinyar ta ki, dama na zo ne in tambayeki, part ɗin ki kike so, ko wancan da ake gyarawa?"
"Ban sani ba, ida ka ga dama ka jani ka kai ni titi ka yar ka haÉ—a mini da saki, ka yi Aure ka sa a gidan".
"Hmm Na'ima mai rikicin gangan, ai duk wani abu da za ayi, muna tare forver, duk da ɓata mini rai da ki ke yi, kina da wata kima da daraja a idanuna, shiyasa na ke tambayar ki abin da ki ke so, amma tin da ba kya so, shikenan" ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya fice.
Yanzu da Abra tana nan, da wataƙila ita zata gayawa damuwar ta, ko ba komai ta tayata jin babu daɗi, amma Salman shi ba damuwa zai yi ba ko ta gaya masa, ga yadda suka ƙare da Anty Suwaiba, ta ƙanƙame Aisha ta fashe da kuka.
Da gudu ta shiga cikin gidan, tana ta uban haki kamar ta yi dambe da kura, Yaya Musa da yake jan ruwa a rijiya ya kalleta ya ce "ke meye haka? Gudun me ki ke yi ne?".
Da hanzari Inna ta fito daga wurin da suke girki, ta kalleta ta ce "meke faruwa haka? Ina gyaÉ—ar?".
Jifa ta yi da farantin gyaÉ—ar ta nemi wuri ta zauna tana ta haki.
Yaya Musa ya ce "Wai ma a haka ki ka fita aiken? Ina mayafinki?".
"Dan Allah ka bari in dawo hayyacina" ta yi maganar tana haki.
Sai da ta samu nutsuwa sannan ta fara ƙoƙarin tashi tsaye, Inna ta ce "Ina kuma zaki, ba ki mana bayanin mai ya faru ba? Ina aiken da na yi miki?".
"Wai Inna ke ta gyaɗar ki ma ki ke yi ba ta ratuwata ba ko? Wani mahaukaci ne fa ya buge ni da mota, kuma ya fara kirana da wani suna yana ƙoƙarin rungumeni".
Dafe ƙirji Inna ta yi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ban gane rungumeki ba, ya rungumekin ne ko kuwa?".
"A'a, kan ya rungumenin ne na É—au farantuna na gudo gida".
"Ki gaya min gaskiya dan ubanki, mai ya yi miki?".
"Be fa yi mini komai ba, ban bari ya taɓa ni ba".
Yaya Musa ya ce "Wannan yarinyar wataƙila ma ƙarya take, wata maganar ta je ta ɗauko".
MurguÉ—awa Yaya Musa ba ki ta yi, ta nufi É—akinsu.
"To ina gyaɗar? Ko baki karɓo ba?".
"Ni fa wannan gyaÉ—ar ta watse a hanya, kuma ban tsaye tsintowa ba, dan ban san me zai mini ba idan na tsaya".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shikenan yau asara ta hauni, gyaÉ—ar duk ki ka watsar mini, kin kyauta".
"Au Inna, in tsaya tsinto gyaÉ—a ya rungumeni ko? Kuma in dawo ki hau cajeni"
"A'a ni bance ba, Allah ya mayar mini da alkhairi, amma dai kin gama da ni".
"Allah sarki Baba, da yana nan da shi zai biyaki kuɗin gyaɗar nan, ki daina yi mini mita, amma yanzu ba mai biya mini sai mita ki ke yi, Allah ya jiƙan ka Baba"
Inna ta ce "Ameen, amma ai dole in yi mita, tun da asara ki ka janyo mini" Inna ta ƙarasa maganar tana ɗagowa, sai dai tuni hawaye ya wankewa 'yar Baba fuska.
"Wai ba zaki daina wannan koke koken haka ba? Kina tunanin kukan nan yana da amfani a gareki da kuma Baban ne? Ko shikenan idan kin yi laifi ba za ayi miki faÉ—a ba?" Cewar Yaya Musa da jikinsa ya yi san yi.
"Yaya Musa, ba ina kuka ne saboda fa₦an Inna ba, in dai wannan faɗan ne ai na saba da shi, ina kuka ne saboda rashin Baba, da kuma yadda aka yi Baba ya rasa ransa. Ka san wacece ni, kuma ka san waye Baba a wurina, na so ace ya yi tsawon rai a duniya, dan in nuna masa gata. Ina fatan Allah ya bani damar da zan yi ilimi mai zurfi, yadda wani talaka kamar Baba, ba zai ƙara rasa ransa ba, saboda shi talaka ne ba. Wallahi ba zan taɓa yafewa waɗanda suka yi sakaci a kan rayuwarsa ba, na san lokacinsa ne ya yi, amma ya mutu a wulaƙance ba kulawa, Allah ya tsinewa wa......
"A'a A'a, kar ki kuskura in ji irin wannan mummunan furicin a bakin ki, ai ko baki faɗa ba, Allah ishashe ne, kuma ya ga abin da ya faru, shi baban na ki tunda ki ke da shi, kin taɓa jin ya tsinewa wani? To kar in kuma ji, maza je ki yi alwala ki ɗau carbi, ki ta masa addu'a".
Abin duniya ya bi ya addabi zuciyar Bulama, ko wurin aiki ba ya iya zauwa, sai dai ya wuni a gida, kusan kullum cikin zarya yake tsakanin Asibitin da aka ce Adnan ya kwanta da kuma gidansa. Maƙwabcin Adnan ne ya nunawa Bulama gidan Adnan, da ya gaji da zaryar da yake masa, gidan Adnan ɗin ma idan yaje, sai mai gadi ya ce masa baya nan.
Babban abin da ya ƙara ɗagawa Bulama hankali, bai wuce yadda aka ce masa yarinyar nan ta mutu ba, saboda zuciyarsa ta azalzalu da son ya ganta, ya gano ya aka yi ta zama 'yar sa, sai dai har duniya ta gushe, ba zai fasa ɗorawa kansa da Asibitinsa laifin da sa hannunsu a kisan Abra ba.
"Yanzu kenan na bada gudunmawa wurin kashe 'yar da na haifa, idan ta tabatta 'ya ta ce?" Ya yi wa kansa wannan tambayar.
Wasu hawaye ne da bai shirya zubarsu ba, suka gangaro a kan kuncinsa, bai taɓa aikata abin da ya zo ya dame shi ba, ya hana shi sukuni ba irin wannan. Shiryawa ya yi ya kuma ɗaukar mota, ya tafi gidan Adnan.
Ya na zuwa ya tarar da maigadi suka gaisa, mai gadin ya ce "Wallahi ranka ya daÉ—e, yau ma baya nan, yama yi balaguro fa".