← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 145

Sashe 41

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ruÉ—e Mama ta ce. "Yanzu me ya faru, na gan ki a hargitse?" Labarin abun da ya faru ta sanar mata.

Cikin takaici Mama ta ce, "Wannan mata akwai bala'i, mata kawai ki É—orawa kanki jaraba a rayuwa?"

"Shegiya ga shi ta ƙi mutuwa."

Jinjina kai Mama ta yi ta ce. "To ta je dan kanta, aniyarta ta bi ta, zama gidan Khamal ne yanzu kika fara, sai dai ta mutu dan baƙin ciki. Ki kwantar da hankalinki, na san Khamal ɗin zai zo ya mayar da ke cikin ruwan sanyi."

"Hmm, Mama babban tashin hankalina kullum cikin cewa za ta yi masa Aure take, tsorona kar zancenta ya tabbata, dan sai abun da ta ce iyayensa suke bi, idan ta dage amincewa fa za su yi." Ta yi maganar cikin tsantsar damuwa.

"Ba zai yiyu ba, wannan tatsuniya ce, ki daina damun kanki akan wannan soki burutsun tsohuwar mara ma'ana, ki É—auki zancenta shirme kawai. Tashi ki wuce ciki ki huta, bari Suwaiba ta dawo ta dafa miki abin da zaki ci."

Zuciyar Nai'ma fal baƙin ciki ta miƙe ta shige ciki, wata irin tsanar Granny na cika mata zuciya, shegiyar mata ta yi sanadin da yau za ta kwana a cikin zafi ba a cikin AC ba, ita da ko taro ake a gidansu ba ta kwana, sai dai ta zo da sassafe saboda ba ta iya baccin cikin kwanciyar hankali. Babban takaicinta ba ta san abun da ta yi Granny ta yi mata haka ba, don ko kusa ba ta yi tunanin Salman ne ya sanar musu abun da ta yi wa Abra jiya ba.

Abra na ɗakinta tana zuba abubuwan school a cikin new bag ɗinta, sai a time ɗin ta farga da rashin ganin I.d card ɗinta. Ƙara checking tsohuwar jakarta ta yi ko za ta gan shi amma ba ta gani ba, parlour ta fito inda Salman yake zaune yana kallon Ball.

"Faris school i.d card É—ina yana gurinka?"

Ba tare da ya ɗago ba ya ce. "No." Cikin damuwa ta ce. "Na duba ban gani ba, Allah yasa ban yar da shi ba." Yana duban ta ya ce. "Ki ƙara dubawa dai sosai Yaya." Kamar za ta yi kuka ta ce. "Na fa duba ko'ina ban gani ba."

"To mene abun damuwa? Kar ki mun kuka ni akan É—an wannan abun."

"Dole in damu Salman, idan aka hana ni shiga school fa saboda babu shi."

"Babu mai hana ki, wasu ma ba a ba su ba, ki bari gobe idan muka je school sai mu yi report a sake miki wani, kafin a sake sai ki dinga nuna admission latter É—inki in za mu shiga."

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Amma na yi mamakin rasa abun nan, ko garin ya na yar oho?"

"Yarinya ce ke, shi ya sa komai naki sai addu'a, kuka, shagwaɓa, everything."

Dariya ta yi ta faki idonsa ta ja dogon hancinsa da ƙarfi ta ce. "Tazarar shekaru uku ba wasa ba ce yaro." Tana faɗin hakan sai Salman ya yunƙura kamar zai kamo ta, ƙara ta saki tare da yin baya da sauri tana dariya. Ƙwafa kawai ya yi bai ce komai ba.

Dawowa ta yi ta zauna a kusa da shi ta ce. "Please kar ka faÉ—a wa Abbi na yi loosing i.d card É—ina, ya ce daga fara zuwa har na fara yarda abubuwa."

"An gama My Angel, zo ki taya ni kallo."

"Maƙe kafaɗa ta yi ta ce. "Bacci zan yi, ka san gobe 8 muke da lecture, kai ma haka, saura kuma ka makarar da mu."

"Uhm, su Yaya Æ´an University, inyee." Ya yi maganar cikin dariya."

"Na ji, ka kira Mami kuwa?"

"Na kira ta ba ta É—auka ba."

Jinjina kai kawai Abra ta yi ta miƙe ta koma ɗakinta.

Washegari da sassafe Ammi tana kitchen tana haÉ—a breakfast Granny ta zo bakin kitchen É—in ta tsaya ta fara magana.

"Kai jama'a, mutane babu Allah a ransu, É—ana yana can gurin neman halak amma saboda rashin tsoron Allah an kira shi an haÉ—a mu, jiya har na fara bacci kiran wayarsa ya tashe ni, to ni dai ba ruwana kowa ya haifa, kuma duk abun da mutum ya mun sai an yi masa shi ma, ato."

Murmurshi Ammi ta yi tare da juyowa tana duban Granny, cikin girmamawa ta tsuguna ta ce. "Ina kwana Hajiya?"

"Lau." Granny ta ba ta amsa cikin ɓata fuska.

"Bari na kawo miki abincin Granny, yau na makara ban tashi da wuri ba ne.

"To ba yunwa ce ta taso ni ba, a ƙoshe nake, kin san ni ƴaƴana ba sa cewa in yi abu in ƙi yi, tunda ni ma suna mun biyayya daidai gwargwado, abun da Hamisu ya faɗa mun ne na kwana da shi a raina, yau kuwa ina tashi na ce ba zan yi sanya ba, gidansu waccan gantalalliyar matar kamalun zan je in dawo da ita."

"Hajiya da kanki kuma? Da kin bari Khamal É—in ya je ya É—auko ta."

"Bar ni in je da kaina É—in, ni yanzu ba dogon surutu na zo mu yi ba, kira direba ya zo ya kai ni."

Ammi ta ce. "Toh, amma dan Allah ki tsaya ki karya Hajiya." Granny ta ce. "To na tsaya, kuma fa da gaskiyarki A'isha, dan waɗancan ruɓaɓɓun idan na je babu abun da za su ba ni, sai dai su bar ni yunwa tai ta sakaɗa ta, Allah na tuba ma ko sun ba ni ba ci zan yi ba, yo me zan yi da kayansu?"

Takwas da mintuna a ƙofar gidansu Nai'ma ta yi wa su Granny, tana zaune a bayan Mota take bin gidan da wani irin kallo. Tsaki ta ja ta ce. "Tirrrr, ban da ƙaddara me zai haɗa Kamalu da ƴar wannan gidan? Gida ɗan tsurut haka kamar kabari, don ma Allah ya yi mu masu ilimi, mun san Talaka da mai kuɗi duk Allah ne ya yi su." Ta ƙarashe maganar tare da buɗe Motar ta fita, fuskar nan babu fara'a ko kaɗan, sai fama take da ƙatuwar jaka a hannu. Murmurshi kawai driver yake.

Aunty Suwaiba tana tsakar gida tana alwala Granny ta rafka sallama, cikin mamaki take kallon ta, lokaci É—aya ta haÉ—e rai ta cigaba da abun da take yi.

"Ba mutane a gidan ne ko gidan na arna ne? Ana ta sallama an ƙi amsawa."

Hararar ƙasan ido Suwaiba ta wurga wa Granny, cikin raini ta ce. "Me Idonki ya gane miki?" Tafa hannuwa Granny ta yi ta ce. "A'a fa, kar ki mun fitsara da farar safiyar nan, wallahi jibguwa zaki yi, kin san jikana soja ne, yanzu sai in kira shi ya turo sojoji mota-mota a tafi dake a ɗaure, don haka ki kiyaye ni. Kodayake ba laifinki ba ne, zafin zawarci ne, dan shi babu abun da ba ya sakawa." Ba ta jira cewar Suwaiba ta shige ciki tana baɓɓata fuska.

Mama ta tarɓe ta ba yabo ba fallasa, Granny ba ta damu ba ta zazzage musu abun da yake cikinta tass, sai da ta ƙare musu cin mutunci akan mugun halinsu sannan ta dubi Nai'ma dake ta banka mata harara a sace ta ce. "Kya iya kwaso jiki ki biyo ni mu tafi, ba kuma don halinki na zo bikon nan ba, don ɗanki Salman na zo, yaron kirki kar ya ƙullace ni akan abun da na yi miki." Nai'ma ba ta tanka mata ba ta miƙe ta shige ɗaki. Taɓe baki ta yi. "Ko ba komai yau an yi kwanan gidan gyatumi cikin sauro da zafi ba cikin raɓa gidan jikana da aka saba ba." Tsaki Aunty Suwaiba ta yi ta miƙe ta bi bayan Na'ima.

Around 12 na rana su Abra suka fito daga lecture, lecture biyu gare su kawai yau. Za ma ta yi a ɗaya daga cikin rumfunan department ɗinsu dan jiran Salman, shi sai 1 za su tashi. Khairat ce ta ƙaraso ta kama hannun Abra ta ce. "Zo mu je ki kira ni in duba wani abu kafin twin brother ɗin naki ya fito." Ƙin tashi Abra ta yi ta ce. "Kai khairy kin fiya yawo."

"Please ki taso mu je."

Yamutsa fuska Abra ta yi ta ce. "Ina za mu?" Khairy ta ce. "Can ne fa ba wani da nisa ba, daɗina dake ragwanta, yanzu ɗan zaman lecture ɗin nan sai ki ce kin gaji, ana ganin ki an ga fresh student." Murmurshi Abra ta yi ta miƙe suka tafi.

Office ɗin Fayyad suka je, Khairy ta duba ko za ta ƙara ganin Adnan yau ma, sai dai ta yi rashin sa'a, yana tafiya suka zo." Cikin rashin jin daɗi ta ce. "Oh My God, kar dai yau ban zo school a sa'a ba?" Abra da ba ta san akan me take magana ba ta ce. "What happened?"

"Guy ɗin da nake ba ki labari jiya na zo gani, daƙyar na iya bacci daren jiya saboda tunaninsa, na ci burin sake ganin shi yau, kuma kin san muna zuwa nan na ji ƙamshinsa." Khairy ta ba ta amsa cikin rawar jiki.

Jinjina kai Abra ta yi ta ce. "Kin gamu da wahala amma, daga ganin mutum duk kin wani burkice, har kin gane wani ƙamshinsa?"

"Ba za ki gane ba ne Abra Khamal Khamis, guy ɗin ya haɗu ƙarshe, kin san bana son baƙin Namiji, amma ganin guy ɗin nan jiya gaba-d'aya ya canza mini ra'ayi, ban yi tunani cikin baƙaƙen maza akwai masu kyau haka ba."

Taɓe baki Abra ta yi dan totally shirme ta ɗauki batun, a ganinta wannan wahala ce da ɗora wa kai jidali. Komawa gurin zamanta ta yi ta bar Khairy da dube_dube, dan ƙin haƙura ta yi ta ce ita ba za ta tafi ba sai ta gan shi.

Bayan sun koma gida suka tarar Nai'ma ta dawo, ba ta nuna musu komai ba da za su gane akwai dalilin da ya sa ta tafi gida jiya ba. Kasancewar Abbi yana nan ba ta nuna wa Abra komai na kyara ba, har girki ta yi kafin su dawo, a cewarta Æ´arta ta kwaso gajiyar school ba za ta dawo ta yi girki ba. Abra tana cin abinci ta yi Sallah ta watsa ruwa ta kwanta, tunda babu abun da za ta yi.
Chapter 41 · 0% Book details