← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 145

Sashe 116

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƴar Baba har ta shige ta gabansa bata lura da shi ba, kamar daga sama taji ya ce "Mai gyaɗa a bani gyaɗa" da sauri ta juya tana faɗin "Auzubillahi wayyo Allah Inna na shiga uku" ta faɗa tana dafe ƙirjinta da hannu ɗaya. Adnan ya ware manyan idanunsa waje cike da mmki yake binta da kallo ya ce "Kamar kinga aljani?" Murguɗa baki ta yi "Malam ɗan baƙi ka fita daga sabgata, Wlh kuma aniyyarka ta bika, idan kaci gaba da bina sai na kai ƙarar ka wajan Mai Gari"

"Yanzu ko dai anjima, ko gobe?" Adnan ya tambaya "Kai baka jin tsoran Mai gari ne?" Ya watsa hannu ya ce "For what reason zan ji tsoron sa? Bayan ke ɗin matata ce ina nufin zaki zama matata kiyi ta haifa mini fitsararrun yara irinki" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un bata taɓa jin rashin kuka da batsa irin wannan ba, ita yake cewa zata haihu iskanci fa kenan? "Wallahi ni ba ƴar iska bace, Allah ya sauwaƙe na zama matar ɗan baƙi wallahi bari kaji ba zan taɓa son ka ba, daka ganinka mugu ne" Murmushi kawai ya yi yana faɗin "Kinga kuma ni ɗan iska ɗin ne, kuma dole na aureki" banza tai masa zata juya ya yi saurin kama hannunta ya ce "Wait don tsaya sbd darajar iyayenki" jin ya ce iyaye ya sa ta tsaya ta ce "Sake ni, shi ya sa kwana biyu Inna ke ta caje ni kamar wata ɓarauniya zama faɗi me kake son cewa" a hankali ya ce "Ya sunanki?" "Ƴar baba" ta bashi amsa a taƙaice ya Girgiza kai ya ce "Ƴar Baba isn't a real name, sunan gsky" fari ta yi ta ce "Ohhu maka ɗan anace natacce" juyawa ta yi zata tafi yai saurin riƙeta yana ƙwace farantin kanta tare da ajjiyewa gefe guda. "Babu inda zaki sai ki faɗa mini Wacece ke, su waye iyayenki ina gidanku yake.." a tsora ce tace "Na shiga uku Shikenan Inna ta samu abin mita ka cikani....," Jawota da Adnan ya yi zuwa jikinsa tare da rungometa sosai a ƙirjinsa shi ne yai saurin katse mata zan can da take yi....
[11/10, 8:23 PM] Abk: Ƙura mata ido ya yi, wanda ya saukar da wata irin kasala, taga Adnan ya yi mata wani irin kwarjini, bakinta ya mutu ɗif.

"Ni ne mummuna ko?"

Ta yi saurin girgiza masa kai, tare da sunkunyar da kanta ƙasa.

"Kalleni" ya faɗa yana ƙura mata idanu.

A hankali ta ɗago kai ta kalli Adnan, sam Adnan ba shi da muni, dan duk ƙauyen nan ba zata iya nuna wanda ya kai shi kyawu ba balle ya fishi, amma dakakkiyar muryarsa da yanayin jikinsa sai ta ke ganin kamar zai yi mugunta.

"'yar uwakki sam ba ta da tsiwa, saliha ce, mai biyayya mai yasa halayenku suka sha banban?"

"'Yar uwata kuma?" Ta yi maganar tana kallonsa.

"Eh, wadda ki ka ji ina gaya miki sunanta"

"Tana ina?"

Adnan ya yi ajiyar zuciya ya ce "Mu je can wurin mu zauna in nuna miki hotonta". Haka nan 'yar Baba ta ji tana son ganin wadda ya ce "yar uwatta ce, dan ya soso mata abin da yake mata ƙaiƙayi a rai.

Suka nufi kan wani dakali suka zauna.

"Kafin in nuna miki, sai kin gaya mini sunan ki, da gidanku".

" 'Yar Baba" ta bashi amsa"'.

" 'yar Baba ai ba suna ba ne"

"Afra"

"Afra ko Abra".

"Malam ni Afra nace maka" ta faÉ—a cikin tsiwa.

"Waye ya sa miki sunan 'yan gayu haka?"

"Wani É—an sanda ne" ta bashi amsa.

"ÆŠan sanda kuma? Ya aka yi É—an sanda ya sa miki suna? Shi ne mahaifinki?"

"A'a cewa aka yi wai Baba tsinto ni ya yi" ta faɗa cikin rauni, idanunta na tara hawaye. Ras gaban Adnan ya faɗi, idan kuwa haka ne ya tabatta Afra da Abra suna da alaƙa, duk yaran Bulama ne.

Ya zira hannunsa a aljihunsa, ya ciro wayarsa, ya lalubo hotunan Abra ya miƙa mata.

Da sauri ta sa hannu ta karɓa, jikinta na rawa ta ƙurawa wayar idanu, cikin rawar murya ta ce "Kai, wannan ai nice".

"Matsa can, matata ta fiki kyau, ke ba 'yar gayu ba ce ai".

"Dan Allah da gaske 'yar uwata ce? Tana ina? Dan girman Allah a ina take?".

Adnan ya karɓe wayarsa ya ce "Sai munje kin nuna mini gidanku tukuna"

Da sauri ta tashi, ta É—au farantin gyaÉ—ar ta, ta ce "Tashi muje to ka gani"

Adnan ya miƙe ya bita, suna tafe tana share hawaye.

"To kuma kukan me ki ke yi?" Kasa magana ta yi, sai sake fashewa da kuka, alamar akwai wani abu da yake damunta a zuciyarta.

"Bana son kuka, idan ba ki daina kukan nan ba, ba zan kai ki wurinta ba" ta saka hannu ta goge hawayen fuskarta ta ce "Na daina, dan Allah ka yi haƙuri"

"Kin san wani Sadi a garin nan?"

Zaro idanuwa ta yi ta ce "Kai wannan É—an daban, me zai haÉ—ani da shi?, na san shi".

"Ya akai kika san shine, sannan A ina yake?".

"ShikaÉ—ai ne Sadi, ana ce masa É—an kunama, Gidansa a garin nan, yana da mata da 'ya'ya, amma fa sai ya shekara biyar baya garin nan, bama a sanin ya zo balle a san ya tafi, 'yan sanda sun sha zuwa su kama shi, amma ba a samunsa".

A hankali Adnan ya furta "Sadi É—an kunama"

Ta kalli bakinsa ta ce "Me kace?"

"Ba komai, watarana zaki nuna mini gidansa".

"Na shiga uku ni kaza, Wallahi ba zani ba, gaba É—aya layin gidan nan mafarauta ne, karnuka ne sun fi Ashirin a layin nan, wallahi ba zani ba"

"Ashe ba ki shirya ganin 'yar uwar ta ki ba".

"A'a dan Allah kar ka yi mini haka, Wallahi ina son ganinta, kuma har babanmu da Babarmu duk zaka nuna mini? Dan Allah ba yaudarata ka ke ba 'yar uwata ce? Ya aka yi ka san 'yar uwata ce? An sha yi mini gori a garin nan wai ba'a san iyayena ba, Baba ne ya tsinto ni, shi yake mini komai, rashin lafiya ta kama shi, aka tura shi wani Asibiti a Kaduna, wasu azzalumai suka bar shi ya mutu" tuni hawaye ya gama wanke mata fuska.

Wani irin tausayin yarinyar ya kama shi, ya tuna lokacin da Abra ke masa magiya a kan ya haÉ—ata da mahaifinta, Allah sarki a wannan karon ba zai iya sanar da Afra wane irin uba ne da su ba. Abin da yake birge shi da ita shi ne, ba ta da rufi, yanzun nan zaka ji abubuwa da dama a bakinta, a yanzu haka ya samu abokiyar gabatar da aikin da ya zo yi garin.

"Matata ki daina kuka, bana son sake ganin hawayenki dan Allah, ina son in goge laifin da na aikata miki a baya".

"Matarka? Wane laifi ka yi mata? Ba 'yar uwar tawa ka ke aure ba amma ka ke kirana da matarka?"

Sai da ta yi Magana sannan Adnan ya dawo hayyacinsa ya ce "Ai Yanzu tun da muna tare a nan kece matar tawa".

"Allah ya kiyaye, ji mayaudari".

Adnan ya haÉ—e rai ya ce "Ni kike cewa mayaudari?"

"A'a yi haƙuri dan Allah, ga gidan namu munzo, bari in shiga in gaya wa Inna ita ma ka nuna mata hoton, sai ma ka gaya mata ka san iyayena".

Adnan ya yi murmushi ya ce "To shikenan, maza shiga ki gaya mata".

Da hanzari kamar zata kifa, ta dafe farantin gyaÉ—arta, ta shiga cikin gidan tun daga soro tana kiran Inna.

Adnan ya ƙarewa gidan da Afra take ido, gidan ƙasa ne, ginin ƙauye ya jinjina kai ya ce "Afra, Allah ne ya so ni da rahama domin in gyara laifukana, ya haɗani da 'yar uwar Abra".

"Inna! Inna fito fito" A gigice Inna ta fito daga banÉ—aki, ta yi jifa da butar hannunta, tana nema ta dungura, saboda yadda ta ji 'yar Baba na kwaÉ—a mata kira.

"Ke lafiya?".

Ta ƙaraso ta riƙe hannun Inna ta ce "Inna Allah ya karɓi Addu'a ta".

"Wace Addu'ar?".

"Inna na haÉ—u da wanda ya san iyayena, har ya nuna mini hotunan 'yar uwata, Wallahi Inna komai namu iri É—aya".

A fusace Inna ta ce "Matsa ki bani wuri mahaukaciya, kawai kin zo kina É—aga mini hankali".

"Wallahi Inna da gaske nake, ki zo muje yana ƙofar gida ki ganshi".

Ta dinga jan hannun Inna zuwa ƙofar gida, sai dai suna zuwa Adnan ya tafi.

Ai kuwa Inna ta mangarewa 'yar Baba ƙeya.

"Dan ubanki kawai kin É—aga mini hankali, kin zo kina mini hauka, ni anya ma ba da gaske aljanu ne suka shafeki ba, yarinya sam ba kya Hankali, tsugunno zan yi amma ki ka saka na fito a guje, na É—auka wani abu ne ya sameki, ja'ira mara hankali".

Jiki a sanyaye Afra ta ƙarasa shiga cikin gida, ita ma ta fara tunanin anya ba da gaske aljanu ne suke mata wasa da hankali ba?.

Yaya Musa ne ya shigo gidan, yana faÉ—in "Inna ke da wa ki ke ta wannan faÉ—an?".

"Ni da wannan yarinyar mana, ta shigo tana ƙwala mini kira, wai wani in zo wai ga wani mutum ya san 'yar uwatta. Ranar lahadi mai zuwa, dan ubanta gidan na rimi zan kai ta ya yi mata ruƙiyya".

'yar Baba ta zare ido ta ce "Kai, dukan mutane fa yake yi, ni wallahi bani da aljanu".

"Aikuwa sai na kai ki, idan ma iskanci ne abin naki, ya zane mini ke".

Mami ce zaune tana waya da Hajiya Mama, suna hirar yadda Little ta yi wayo, Mama ta ce "Ai insha Allah cikin satin nan muke sa ran zuwa, mu zo mu ganta".

"Allah sarki, ubangiji Allah ya kawo ku, Allah yasa kar ta yi muku ƙyuwa, dan ta fara gane mutane yanzu".

"Ai ni idan ta mini ƙyuya, ba ta yiwa maigidan na ta ba" suka yi dariya gaba ɗaya.

Mama ta ce "Ya Major, da É—ana Salman?"

"Salman kwana biyu bai leƙo mu ba, yana can makaranta, Major kuma ya yi Aure".

"Subhanallah Aure kuma Hajiya Na'ima?".

"Aure fa, yau kwana takwas".
Chapter 116 · 0% Book details