← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 145

Sashe 52

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abra tun tana kewar rashin wayarta, har ta saba ta haƙura da rashin wayar, gefe guda haka kurum take jin ta yi missing ɗin me turo mata messages ɗin nan a wayarta, ko ba komai wani mutum na musamman ne da ya shigo rayuwarta, ta wata siga da babu wanda ya taɓa shigowa ta haka.
Guntun tsaki ta ja, bayan tuna Adnan ya tafar mata da wayarta.
Sosai ta maida hankalinta kan karatunta, tun daga ranar da Adnan ya tafi da wayarta, ba ta sake ganinsa ba, tun tana tunanin zata kuma ganinsa ya bata wayarta har ta dena, ta cigaba da al'amuranta, sai cewa ma take wa ya sani koma ɓarawon wayane, wayar yake son ya sace shiyasa yake ta binta.

Yau ba lokaci É—aya Abra za su tashi da Salman ba, dan haka akwai snacks a jakarta, ta tafi department É—in su Salman, domin suci sai ta jira har ya gama lectures, Sannan su tafi gida, dan ta san idan taje gidan ma, ba daÉ—insa za taji ba.

Ajin Su Salman ta nufa, ta ɗan leƙa ta window, taga ana yi musu lectures, Malmin ya raba ajin gida biyu, yana yi musu kacici_kacici, yace duk rukunin da suka ci, suna da maki goma-goma dukaninsu, amma sai ya kammala lectures ɗinsa na yau za'ayi.

Ajinsu Faris Maza sunfi yawa akan mata, dukkansu suna sanye da fararen lapcoat akan kayansu, sun tattara nutsuwarsu akan malamin.

Ba wanda ya ganta, tana nan tsaye aka gama lectures É—in, aka fara Quiz.

Anayi tana ta murmushi, abun yana burgeta sosai da sosai.

Can aka yiwa rukunin su Faris wata tambaya, abunka da manyan professors, sai da ya rikita tambayar, yadda ba za su fahimta ba.
Sai ya basu option yace su zaɓa, ganin sunyi shiru suna mazari ya sa Abra tai farat tace "Faris Ba ne amsar fa" gaba ɗaya ta manta a jikin window take, tana leƙe.

Aikuwa gaba É—aya suka waigo suna kallonta, sai kuma tayi shiru tana rarraba ido.
Prof É—in nan yace "Zo nan" jiki a sanyaye ta zagaya ta shiga ajin, tana sunkuyar da kai, saboda ba ta son kallo.

Ya kalleta yace "Me kike yi a jikin window?".

"Brother na nake jira mu ci Abinci" ta faÉ—a kai tsaye.

Yai murmushi yace "Sai kace a Nursery? Waye brother É—in naki?"

Tace "Faris ne"

"Waye Faris?".

Ta kalli Salman da ido, Salman wata kunya ta kama shi, Sam Abra bata da wayo wasu lokutan.

Prof É—in yace "iyee, cire facemask É—in nan".

A hankali ta sauke face mask É—in, tana sunkuyar da kai, harda masu cewa wow, tubarkallah abunda ya sa Salman sake tsuke fuska.

Prof Jibiya yana da barkwanci sosai, dan haka yace "Salman, is she your sister?".

Salman yace "Eh ƙanwata ce".

Zaro ido ta yi, za tai magana, amma Salman ya harareta, hakan ya sata yin shiri.

Jibiya yace "Masha Allah, to yanzu yi mana bayanin, meyasa kika zaɓi B a matsayin Amsa?".

A nutse Abra tayi masa bayani, wanda in ba me kaifin hankali ba, babu wanda zai iya gano amsar.

Ya jinjina kai yace "Kai Masha Allah, Madalla da basira irin taki, me kike karanta ne?"

Ta gaya masa, ya jinjina nai, gaba É—aya ba science tayi ba, amma ta iya bada wannan amsar.

Prof yace "Yanzu kiyi tafiyarki, kije ki ci Abincin ki, dan wannan ba yanzu zai fito ba".

Tace "To, amma zan iya ba shi nasa kan su fito?" Ya jinjina mata kai, 'yan ajin sai dariya sukewa halin ƙuruciya na Abra.

Taje gaban seat É—in Faris, ta É—akko wata leda ta ajiye masa tace "zanje inyi karatu in kun gama sai mu tafi".

Faris ya kalleta, a hankali yace "Dan Allah Angel yaushe zaki girma ne? Yarinya ba wayo gaba É—aya".

Tace "Ni ba zan kulaka a nan ba, sai munje gida".

Daga haka ta yiwa lecturer godiya, ta fice, prof ya cigba da koɗa Abra da baiwarta, har da tambayar Salman anya uwa ɗaya uba ɗaya suke? Ko dai su larabawa ne, sai da Salman ransa ya ɓaci, ya tsuke fuska.

Tana tafe tana ƙoƙarin samun gurin da zata zauna, ta ci Abincinta tayi karatu.
Wani irin mahaukacin parkig aka yi a gabanta, wanda sai da ta razana, ta runtse idanunta.
Jin shiru ba'a bugeta da motar bane ya sa ta buÉ—e idanunta a hankali.

Ido huÉ—u suka yi da shi, wanda sai da ya fuskanci halin firgici da ta shiga.

Juyawa tayi za ta canza hanya, amma cikin zafin nama ya fito daga motar, ya danƙo hannunta, ya jefata a cikin motar ta sa, ya rufe motar ya zagaya ya shiga, ya fizgi motar da gudu, ya bar makarantar.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina zaka kai ni, na shiga ukuna, wayyo Abbina, Faris dan Allah a temake ni"

"Shut up, ki dena yi mini ihu" yai mata wata razananniyar tsawa.

Abra cikin kuka tace "dan Allah kayi haƙuri, ka ƙyaleni dan Allah" shiru yayi Mata ya cigaba da tafiya.

Wani gurin cin Abinci yaje, yayi parking ya kalleta ransaa a haÉ—e ya ce "Fito" Cikin tsoro da fargaba ta fito tana zare ido, gurin ba mutane sosai suka shiga cikin gurin cin Abincin.

Yayi mata umarnin ta zauna, haka ta zauna tana cigaba da waige-waige, tsoronta Allah tsoronta kar wani wanda ya santa ya ganta yaje ya gayawa Abbi.

"Me za'a kawo miki?" Yayi Maganar yana kallonta.

Ta girgiza masa kai alamar babu.

"Ba sace ki nayi ba, Cin Abinci kika rako mijinki, dan haka You Are safe, ki saki jikinki, bana sace mutane" Kallonsa take, kamar ba shi ne ya gama yi mata tsawa ba.

Yayi musu order Abinci, amma taƙi ci.

"Nifa Mutum ne ba dodo ba, stop looking at me, like this"

"Dan Allah ka mai da ni, dan Allah kayi haƙuri"
Wani irin kallo yake mata, wanda sai da ta ji tsigar jikinta na tashi.

Sauke idanunsa yayi, ya cigaba da cin abincinsa.

"Ki dena kallona kar in ƙware".

"Ai ba kallonka nake ba" ta faÉ—a a raunane.

"Ya maganarmu ne?".

"Wace Maganar?"

Ya É—ago ya kalleta yace "ina tambayar ki, ki na tambayata?"

Ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Abra talk" yayi Maganar in a cool voice, kamar ba shi ba.

Shiru tayi bata amsa ba.

Adnan yasa hannu ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna.

Ya ɗan kashe mata ido yace "Yaushe zan zo gidanku in ga Major? Kinga ni ba ƙaramin yaro bane, ki dena mini wasa da hankali, ina ta binki amma kina mini wasa da hankali?"

Tace "bakomai"

A hankali ya saki haɓarta yace "muje mota, in baki wayarki, sai muje in ga gidan naku".

"Za'ai mini faÉ—a a gida"

"Ba za'ai miki faÉ—a ba, tashi muje".

Gaba É—aya Abra tsoron sa take ji, duk da tayi mamakin yadda yake Magana yanzu kamar ba shi ba.
Haka ya sata gaba, zuwa cikin mota, a motar ya bata wayarta.

Har bakin layinsu ya kaita, ya kalleta yace "Ranar Saturday zan zo insha Allah, ki shirya karɓa ta"

Ba tace Komai ba, ta fara ƙoƙarin buɗe motar ta fita.

"Wai ke ba ki iya godiya bane? Ko nace na sallameki ne?"

"Nagode" ta faÉ—a tana tsoron kar wani ya ganta, dan ma motar tint ce.

Yace "Well, a sauka lafiya Angel" da sauri ta waiwayo tana kallonsa.

"In baki gama kallon nawa ba, sai in juyo" ba shiri ta buÉ—e motar ta fice, tana waige-waige kar taje wani ya ganta.

Ihsan ce tai wani É—an ihu tace "Janna, Baby kunga Mutumin nan ya rikice, wai Zai zo ya sameni, ko nawane zai sai videon in goge shi".

Baby tayi dariya tace "A siyar masa a farashi mai tsada, sannan ki goge amma muna nan da shi ai, zai gane kuskuren sa, duk da ya saki kuÉ—i, da ba'ai haka ba, yanzu mu dai zamu fita, ki janyo shi nan, ya zo ki tatse mana shi.

Haka suka cigaba da shewa, suna shawarwarin nawa zasu tatse shi.

Suka shirya tsaf suka tafi nasu guri, suka bar Ihsan kawai tana jiran zuwan Yallaɓai.

Su Janna basu koma ba sai bayan la'asar daga nasu gantali, Sai dai abunda suka gani ne ya girgiza su, cikin tashin hankali Janna ta ƙwala ihu, gawar Ihsan ce kwance a cikin jini!

Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/1, 3:01 PM] Abk: A gigice Baby ta cillar da jakar hannunta, cikin waro ido ta kurma wani uban ihu tare da ficewa daga ɗakin hotel ɗin a ruɗe. Ƙarasawa Janna ta yi ta shiga girgiza ƙafar Ihsan cikin kuka da tsananin tashin hankali.

ÆŠaya daga cikin ma'aikatan hotel É—in ne ya hawo sama da sauri jin kururuwar Baby.

"Hey, Lafiya kike mana wannan kwakwazon?"

Kasa magana Baby ta yi, nuna masa ɗakin kawai take yi da hannu tare da toshe bakinta. Shiga ɗakin ya yi cikin sauri, cak ya tsaya tare da dafe ƙirjinsa cikin firgici.

"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un!" Abun da ya furta kenan a fili idanunsa akan gawar Ihsan dake kwance cikin jini malel-male. Da sauri ya juya ya fita ya je ya sanar da Manager na hotel É—in abun da yake faruwa.

After some minutes
Su Janna ne zaune a police station mafi kusa da hotel É—in, idanuwansu sun yi luhu-luhu alamun sun ci kuka sun gode Allah, sai zazzare idanuwa suke yi cikin firgici.

D.p.o dake bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya ya dubi wani jami'i ya ba shi  umarnin ya shigar da Janna cikin cell, kuka ta fara tare da yi masa magiya tana ba shi haƙuri, tsawa ya daka mata wanda ta sa su duka suka razana, ba shiri ta yi shiru ta shiga jujjuya kai. Tasa ƙeyarta jami'in ya yi har cikin cell.

"Ki nutsu, tambayoyi zan miki, kuma ki faɗa mini gaskiyar abin da kika sani, domin idan ma kin mini ƙarya zan gano daga baya, kuma hakan ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba." Cewar D.p.o yana kallon Baby da jikinta ke tsuma.

"In...insha Allahu zan faɗa maka gaskiya yallaɓai."

"Good." Ya faÉ—a cikin gyaÉ—a kai.

"Mene ne alaƙarki da wacce aka kashe?"

"Ƙawata ce."
Chapter 52 · 0% Book details