← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 145

Sashe 39

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ran Salman a ɓace gaba ɗaya ta gagara fahimtarsa, idan har bai Ajjiye girmansa da tayi ba, to ba zai iya kulawa da ita ba kamar yadda ya yi zuciyarsa Al'ƙawari, durƙosawa yyi tare da ɗago ta tsaye muryarsa babu wasa ya ce.
"You will not cry for me. Amsa zaki bani Abra amsa nake buƙata" muryarta na rawa tace "Bayan naje gidan Hajja Amina muka gaisa tai shigewarta ɗaki a nan naita zama, sai dab da magrib ta saka ɗan ta ya ɗauke ni wai shine zai ban saƙon, ganin Aiken Mami ne ban damu ba, shine ya kaini Sadaraki store yai shopping tare da bani wai shine aiken...," Kukan da yaci ƙarfinta ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana wani irin kuka take wanda ta daɗe ba tayi kamarsa ba.

Ganin yadda take kuka har tana shiɗewa kamar numfashinta zai fita ya sanya a fusace Salman ya jawota jikinsa tare da rungometa Tsam-tsam a jikinsa, zuciyarsa na wani irin bugawa kamar zata faso ƙirjinsa ta fito idanunsa ya yi wani masifar jaa kamar gauta jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa saman goshinsa numfashi kawai yake fitarwa.

"You shouted at me,after I am innocent" ta ƙare maganar tana sakin wani irin kuka tana ƙara ƙankame jikin Salman, domin a wajansa kawai take samun sauƙi. Faɗa masa ne kawai ba tayi amma tuntuni ta yarda cewa shine ragamar rayuwarta da babu shi ta tuni Zuciyarta ta buga.
Muryarsa bata fita sosai ya ce "I'm sorry Yaya" yana faɗin hakan ya zareta daga jikinsa kamar walƙiya haka ya ɓace daga ɗakin yana zuwa bedroom ɗin sa, Wayarsa ya ɗauka tare da kiran number Ammi bayan sun gaisa ya faɗa mata dake faruwa. Granny dake gefe hankali tashe tace. "Huhuhu idan ban kaɗa Na'ima gidansu ba yau to wlh kuce ƴar banza ce ni, Ubangiji ya yi gutsi gutsi da Zuciyar Na'ima. Zan aurawa Kamalu Babura sai naga ƙaryar iskanci" tana faɗin hakan ta miƙe tsaye yana ɗaukan mayafi tace "A'isha kike kowa masa kira salamamman drivern can ya kaini gidan Kamalu a yau shima shi ya gane cewa ni ba tsohuwar banza bace duk yadda ka ke da kiyaye harshenka sai an saka kayi saɓon Ubangiji" sai kuma ta fashe da kuka tace "Da ƙyar Na'ima taga Ubangiji da ƙyar ne ta kansa".

Tahir guest palace.
Room 36.
Yana kwance sanye da red ɗin Armless wacce ta bayyanar da faffaɗan ƙirjinsa. A hankali ya mirgina tare da yin rufda ciki yana ɗan lumshe idanunsa.
Ta cikin system ɗin dake gabansa Muryar Abba ta fito yace "Na faɗa cewa zani England,Follow the flight today and come back to Kaduna" Sp Adnan ya ware idanunsa dake cike da bacci a hankali ya Kalli fuskarsa mahaifin nasa ta cikin vedio call ɗin da suke "Abba ba yau zan dawo ba, kuma akwai mota tare dani" cike da damuwa Abba ya ce "How many times do I have to tell you that I don't like long car journeys" Murmushi Adnan ya yi cike da so da ƙaunar mahaifin nasa ya ce "Abinda Ubangiji ya ƙaddara zai samu bawa dole ya samesa ko a jirgi ne, just pray for me"

"Ok I'll, When will you come back?" Adnan na hargitsa sumar kansa idanunsa rufe ya ce "Ni ọsẹ kan tabi meji" Murmushi Abba ya saki yana kallon Hajiya Mama dake gefensa ya ce "Yau ɗanki ya tuna da yaran mahaifiyarsa" Hajiya Mama tayi dry tace "kyan ɗana daman ya gado mahaifiyarsa" Abba yana kallon Adnan ya ce "Idan ɗan ya kasance mace ko? Ɗa namiji kam Ubansa yake kwaikwayo" Murmushi kawai Adnan yake wa iyayen nasa

"Me zaka zauna yi a Kano har bako guda?"

Miƙewa zaune Sp ya yi cikin kwaɓe fuska ya ce "

"An investigation brought me to Kano, who I suspect is in the University" Abba ya ce "Ikon Allah. To Allah ya taimaka ya yi maka jagora please My son is rage zafin zuciya" da idanu kawai Sp yabi Abba "yanzu yaya za'ai ka kama criminal ɗin?" Adnan ya ɗan yatsuna fuska ya ce "I have a plan Abba.. bye take care of yourself" yana faɗin hakan ya kashe system ɗin tare da Miƙewa ya nufi bathroom, wanka ya yi ya shirya cikin wasu ƙana nan kaya Sleeveless tank top da tracksuit trousers ya ɗora white p.cap a saman sumar kansa, sai Ƙamshin Pur oud yake.

Wayarsa ce ta fara ringing ganin sunan Fayyad ya Sanya bai ɗaga ba, hannunsa ya miƙa ya ɗauki I.d card ɗin dake gefen gado, ƙyakkyawar Fuskarta yabi da kallo kafin a hankali yaja idanunsa ya rufe yana sauke numfashi. I.d card ɗin ya saka cikin Aljihu kana ya fita daga Room ɗin cikin sassarfa ya fara sauka daga kan strains ɗin 3 floor. Ganin zai ɓatawa kansa lokacin ya tsaya ya shiga elevator tare da danna 1floor. Yana sauka reception Wayarsa ya fara ƙara ganin sunan Abba yasa ya tsaya tare da ɗaga kiran.

"Son ka kula da kanka, ka rage zafin zuciya. Shine Abinda zaka faɗa ko Abba na riga na haddace fa" ta cikin wayar Abba ya yi Murmushi ya ce "ba zaka gane ba, Allah ya yi maka albarka" Adnan ya ce "Amin, Bye." Motar gabansa ya buɗe tare da shiga yana ji Fayyad ya daki kafaɗarsa ya ce. "Ban taɓa sanin baƙar fata duniya bace sai a kanka Adnan, kaga yadda kayi kyau"

Adnan dai bai ce komai ba.

"Jiya ka kirani kana son magana dani"

Adnan ya jinjina kansa yana rufe idanu, Fayyad ya ce "Ok bari muje gidana muyi magana, da ga nan sai ku gaisa da Madam"
Adnan dai bai ce komai ba, Fayyad ya ƙarawa motarsa wuta babu jimawa suka kawo cikin estate ɗin Motar Fayyad na shigowa ciki Motar Granny da driver ya kawota na danno kai cikin estate da sauri Fayyad ya daka burki ganin motar dake bayansu ta tawo da sauri ta nufi gidan dake kusa da nasa. Adnan ya buɗe idanu da sauri yana jan tsaki. Fayyad ya ce "Wannan driven mahaukaci ne" Adnan ya ƙara jan tsaki ya ce "Ƴan Nigeria ke nan" kafin Fayyad ya yi Magana sunga wata tsohuwa ta tsaya gaban motarsa ta fara Masifa.
"Wani gantallan ne wanda bai san darajar rai ba ke neman salwantar da tawa rayuwar? Kasan nawa ɗana ya sai motar nan kowa? Mutane suyi ta abu daka kamar marasa wadataccen ilimi. Nifa daidai nake da ko wanne ɗan kwalta Alkur'an sai na kwaɓe mu daku kawai kowa ya yi ta kansa" Salman da ya fito daga cikin gidansu ya yi saurin kama hannun Granny sukai cikin gidan. Adnan dai idanunsa a ƙasa Fayyad babu abinda yake banda dry yana buga cinya. Adnan ya ɗaga idanunsa ya ce "Old version ce fa motar masifaffiyar Tsohuwa" kamar ya faɗa a kunan Granny sai gani sukai ta fito daga cikin gidan a guje ta ce "Kaga masifa akanka wallahi li'ilafi qurash" tana faɗin hakan tai cikin gidan tana Masifa son ranta. Shi kansa Sp sai da abin bashi Murmushi kasancewar ba ɗabi'arsa bane sai kawai ya Girgiza kai. Fayyad ya Ƙarasa shigar da motarsa cikin gidan nasa gaba ɗaya suka nufi ciki.

Tunda daga bakin ƙofa Granny ta gyara zaman ɗan kwalinta. Kai tsaye Granny ɗakin Na'ima ta nufa babu jimawa ta dawo hannunta riƙe da mayafi, cillawa Na'ima tayi ta koma ta ƙara ɗakko hand bag itama ta cillawa Na'ima.

"Maza maza kama gabanki wlh Wlh yau koni ko ke, ke babu ruwana ni ba Æ´ar banza bace dole ki yi yaji yau"

Abbi ya ce "Mene ya faru Granny?" Granny ta runste idanunta ta ce "Ni da Ubangiji na kawai muka san abinda ya faru, kuma a satin nan zanwa Kamalu aure. Idan ki kaga banwa Kamalu aure ba cikin satin nan kice ni ba haifaffiya bace cikin uwata"....

LITTAFIN DARE DA DUHU NA KUƊI NE, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[10/1, 2:40 PM] Abk: LITTAFIN DARE DA DUHU NA KUƊI NE, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.

Cikin mamaki Khamal ya ce. "Subhanallahi! Granny wai me ya faru ne?"

"Mene ma bai faru ba Kamalu? Wannan matar taka mai kama da bayi ba matar arziƙi ba ce, mugunta ce fal cikinta da kake ganin ta haka, munafuka mai fuska biyu." Granny ta a faɗi haka tana hararar Nai'ma.

Salman dake tsaye ya juya tare da ficewa daga parlour'n, dan bai É—auki maganganun Granny da mahimmanci ba, a soki burutsunta ya É—au abun, dama fitar da ya yi gidan Aunty Iman zai je ya É—auko Abra, tana can tun safe ta kai mata ziyara.

Nai'ma da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi ta dubi Granny tare da faɗin. "Haba Granny, wai me na yi miki kika tsane ni haka?"

Kama baki ta yi ta ce. "Au ba ki san me kika yi ba? To ba za ki taɓa sani ba kuwa, tashi maza ki ƙara mai ki bar mini gidan jika, takardarki kuma na nan tafe zan kawo miki da kaina, as'as'as."

"Wai dan Allah Granny mene haka? Ya zaki zo ki É—aga mana hankali."

"Abun da ya fi hankali ma zan daga muku, kai da ba ka gane mai ƙaunar ka saboda Allah, wannan matar da ka ji abun da ta aikata wallahi da tuni ka sallame ta kafin ma wani ya ji."

"Me ta yi toh?" Khamal ya tambaya cikin ƙosawa da hargagin Granny.

"Ban sani ba Ubana! Wato ƙarya nake yi kenan, tsofai-tsofai da ni amma kake ƙaryata ni Kamalu? akan wannan makirar matar taka?" Sai ta fashe da kuka tare da faɗin. "Da A'isha ce ai ba za ka ƙaryata ta ba, to wallahi yau sai matar nan ta bar gidan nan, idan kuma ka ƙi in saka direba ya kira mun Hamisu da A'isha in sanar musu na saka abu ka ƙi yi."
Chapter 39 · 0% Book details