← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 145

Sashe 19

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dalla rufemin baki, da anyi magana yenyen ayi haƙuri, ba yau ba gobe kuna liƙe da juna, ba ku san kun girma bane, kusancinku da juna ba shi da wata fa'ida ba?"

Kai tsaye Salman ya gane in da maganganun mahaifiyarsa suka dosa saboda haka yace 'haba Mami, ya zaki dinga Wannan maganar? She's my biological sister, meyasa zaki dinga kawo wannan tunanin?"

Ji tai kamar ta fasa ƙwai a gurin kowama ya huta, Salman ya ji Abra ba yayarsa bace, dan ba zata manta lokacin da ta taɓa gaya masa ba, befi 3yrs ba, dan haka baze iya riƙewa ba, amma da ta tuna kashedin Major, wanda  se ta haɗiye ba ta faɗa ba, dan haryanzu ba ta ƙaunar Abra, ko kaɗan.

Abra kam tuni ta bar falon, hawaye fal idonta, ta rasa meyasa Mami ba ta sonta, kuma ba ta san ta dinga zama da ɗan uwanta, tana son Salman sosai, da shikaɗai take sakewa se Abbi, dan ita ko ƙawaye ba ta da su, saboda ba ta son hayaniya sam, hayaniyar Salman kawai take iya jurewa.
Ta koma É—aki tai shiru tana tunanin menene laifinta a gurin Mamainsu?.

Mami ta cigaba da zazzagawa Salman faÉ—a, kamar za ta dake shi.

Sallamar da akayi ne ta sata yin shiru tare da amsawa.

"Ke da waye ne kike ta wannan ɓaɓatu haka?" Cewar Anty suwaiba.

"Bari Anty suwaiba, ni da wannan sakarkarun mana, kullum yaron nan yana liƙe da wannan yarinyar sekace jaraba, na rasa irin wannan abu, nayi nayi amma yaƙi ji, abu kamar jaraba".

Anty suwaiba cike da duniyanci tace "ban da abunki idan be zauna da 'yar uwarsa ba, da wa ze zauna? Tsakanin É—a da mahaifi ai se Allah".

Salman dai ko Anty suwaiba be samu kulawa ba, ya tashi ya fita tare da jin tausayin Yayarsa.

Suwaiba ta kalleta tace "Ke Na'ima meyasa baki da wayo ne? A garin wannan zafin ran da masifar taki wataran zaki faɗa abunda ake ta ɓoyewa, idan kuwa kika kuskura kika gayawa yarinyar nan ba ke kika haifeta ba, kin san mijinki baya Magana biyu ko? Kuma muddin ya sakeki ba ke kaɗai ya saka ba, har mu ya saka, dan Allah ne gatanmu Khamal ne gatanmu, duk asirinmu a lulluɓe a ƙarƙashin inuwar arzikinsa".

Hajiya Na'ima ta zauna tace "ni Wannan lamarin ya isheni, yau shekaru nawa yarinyar nan tana gidan nan, amma babu abunda ya canza, shawarar ki ba wadda ban amfani da ita ba, amma babu alamar zata bar gidan nan, yanzu na dena jin tsoron Khamal yace ze Aureta, amma Wannan shishshigin da yaron nan yake mata ne bana so".

Anty suwaiba tace "to ke ika ruwanki? Shekara uku fa ta bashi, ta ina ze Aureta kuma Khmal dai baze taɓa cewa ze aurawa ɗansa Ita ba, in dai ba ya so gayamata ba shine mahaifinta ba"

Na'ima tace "kin san wani abu kuwa?"

"A'a sekin faÉ—a"

'yadda Kamal yake fifita ta akan Salman ne ya ƙona min rai, ga ɗan da ka haifa ta sunna, amma ka maida shegiya 'ya kana nuna naka bakomai bane"

"To ya zaki yi, taki ƙaddarar kenan"

Tsaki Na'ima tai dan ji take kamar ta kori Abra daga gidan daurewa kawai takeyi.

Abra na ta jin daÉ—i gobe Abbi ze dawo, idan ya dawo zata tambayeshi tana son zuwa hutu gidan Ammi, dan Ammi tafi sonta akan Mami, babban abunda yake sake bawa Abra mamaki be wuce yadda ake cewa dangin mahaifiya sun fi son É—a, akan dangin mahaifi ba, amma ita a nata dagin, dangin mahaifinta da mahaifinta sunfi sonta fiye da mahaifiyarta da dangin ta.
Domin ƙauracewa ire iren wannan tunanin, se Abra ta ɗaura alwala ta fara haddarta ta Alqur'ani me girma.

Saboda sanin halin Salman, na rashin jure yunwa yake sa Abra ta tashi da wuri ta ɗora breakfast, gashi kuma Abbi ze dawo gari, dan haka bisa al'adarta ita ke shiryawa Abbin nata Abincin da za'a karɓe shi, amma a wannan karon har gari ya waye ƙarfe tara Abra ba ta fito ba.
Hakan ya bawa Salman mamaki, dan haka ya wuce É—akinta, dan jin ba'asi.
Yana zuwa ya tarar da ita ta dunƙule a bargo, se kuka take kamar wata 'yar yaye. Cikin hanzari ya ƙarasa gaban gadonta yana faɗin "Yaya, menene? Kukan me kike?"

Abra ta riƙo hannunsa tace "Salman cikina ciwo"

"Subhanallah, sannu ciwo yake miki?" Ta jinjina masa kai tana kuka.

"To kiyi shiru, ko dai cikin ki ne ya ɓaci, ina da maganin gudawa"

Kasancewar ta shagwaɓaɓɓiya cikin shagwaɓa tace "Um, Um ni ba gudawa nake ba"

Salman yace "to bari in kira Mami"

"A'a ni karka tafi ka barni a nan"

Salman yace "to, bari in kirata a waya"

Abra ta riƙe hannun Salman gam, tana cigaba da rintse ido.

Falo yaje ya É—akko wayar gida, ya dawo É—akin Abra ya zauna Wayar Mami ya kira, ya sanar mata da halin da Abra ke ciki, se dai amsar da ta bashi sam be ji daÉ—in ta ba, na ya kira mata likita ita tana da abun yi.

Haka Salman ya nemo lambar doctor Habib, wanda yake Family doctor É—insu ne, kuma soja ne, doctor Habib yace gashi nan zuwa.

"Faris" ta kira sunansa.

Yace "Na'am Yaya"

"Har amai fa nake yi, da ciwon kai"

Yace "to kiyi haƙuri, doctor yana hanya"

Tace "Ina Mami?"

Salman ya ɗanyi jimm sannan yace "tana zuwa, kiyi haƙuri" yai maganar cike da kulawa.

Yana nan zaune tare da Abra, Doctor ya kira wayar gidan Salman ya É—aga, ya ce "gani nazo, tana wani É—akin ne?"

Salman ya kalli Abra, kayan bacci ne a jikinta, ya É—an tsuke fuska kamar yana gaban doctor yace "jiramu a falo"

Ya kalli Abra yace "tashi muje likitan ya zo"

Abra ta yunƙura ta tashi, se dai Salman ya zare ido yace "Yaya, meye wannan a jikinki?" Da sauri ta waiwaya, jini ne duk ya ɓata mata shimfiɗa da jikinta.

Aikuwa ta fashe da kuka tace "Na shiga uku, meya sameni Faris mutuwa zanyi?"

Salman yace "Innalillahi ba zaki mutu ba, ki canza wasu kayan, semu gayawa doctor, ai normal ne"

Salman yace "to shiga ki canza kaya, bari in jiraki a falo"

Haka ya koma falo shi da likita suka jira Abra, ta fito tana ta tsantsame jikinta, likitan yai mata tambayoyi, nan ya tabattar da period ta fara, se dai ya zo mata da wahala, dan haka ya sakamta drip, tare da bata magunguna da shawarwari.

Salman yaje ya samu mahaifiyarsu kwance a É—akinta, ta haÉ—a abinci ta karya, Salman yace "Mami Yaya ba lafiya fa"

"To ni na saka mata ciwon da zan cire mata?"

Salman ya girgiza kai yace "A'a, doctor yace wai idan da wannan Pad É—in da mata ke amfani da ita wai ki bayar".

"Me za'ai da ita?" Ta tambaye shi.

" ukhty ce za tai amfani da shi"

Hajiya Na'ima ta É—anyi jimmm, sannan tace "jeka toilet ka É—auka"

Salman yaje ya ɗakko ya fice, dan abun kunya, Hajiya Na'ima na gidan, amma se doctor ne ya nunawa Abra yadda ake amfani da pad ɗin, hakan ba ƙaramin ciwo yai wa Salman ba, duk da yana da ƙarancin shekaru amma yana matuƙar kishin yayar ta sa, he is always protective to her, ko a Makaranta ba ya son yaga wani ya raɓeta, wanda tun suna yara sosai baya son ko baƙi sukai yaga yara sun fiye zuwa in da take, se ya dinga ganin kamar zasu cutar da Ita kasancewarta ba me hayaniya ba.

Tana nan kwance, doctor yana jiran ruwan ya ƙare ya samata wani, Salman yaje ya ɗakko bargo ya rufe Abra, yaje kitchen ya dafo mata tea ya ɗakko bread ya zo ya haɗa mata.

Shi kansa doctor yanayin gidan Khamal yana burge shi, kan yaransa a haÉ—e yake, suna son juna sosai, sai dai yana mamakin yadda matarsa bata bawa lamarin 'yar ta ta mahimmanci.

Da drip ɗin farko ya ƙare, Salman da kansa ya din ga bawa Abra abinci, har ta ɗan ci sosai, sannan ta kwata aka kuma saka ɗayan, ya nunawa Salman yadda zata sha magungunan ta, da yadda ze cire mata ruwan idan ya ƙare, sannan ya fita saboda yana da in da za shi.

Salman se jera mata sannu yake, ya ga ta kai hannu tana shashshafa gashin kanta, cikin kulawa yace "Ukty ya dai?"

"Ni kitson nan ne ya dameni, ƙaramin ciwon kai yake" ta faɗa har da ƙwalla.

Salman ya kalli kitson, manya guda shida, ga gashin nan baƙiƙirin, kwance a farar fatar kanta, yace "ko a tsefe ne?"

Tace "eh" ya tashi ya tafi É—akinta, ya É—akko comb da kibiya, ya dawo ya zauna ta É—ora kanta akan cinyarsa, ba'a jima ba ya tsefe kan nan tas, dama Salman ya saba da tsifa, shi yake tsefewa Abra kai wasu lokutan.

Ya shiga taje mata a hankali dan kar taji zafi, gashin ya baje a jikinsa, ya rufe mata fuska.

Hajiya Na'ima ce ta buɗe ƙofar part ɗinta ta fito, turus ta tsaya tana kallon Salman, "meye haka kamar wani ɗan daudu?" Mami tai maganar tana nuna su.

Salman yace "Mami ba kiga ba ta da lafiya ba, tsefe mata nake"

"Au bayan kurumtakar kuma, kuturwa ce ita da ba zata iya tsefewa ba, kai yau nina ke ganin tsiya, tsifar ma se kayi mata namamajo"

Abra tace "Faris bar shi haka, nagode sosai".

Salman yace "tsaya in sa miki ribbon É—in, sai a mai da hular"

"Ina maka magana kana cewa seka sa mata hula, ina ga nan gaba kuma shagon kitso da lalle zaka buɗe, sai kuma suyar doya da ƙwai tunda ka zama ɗan daudu"

Shi Salman ma dariya Mamin ta bashi yace "haba Mami, in ba gashin ki kona Ukty ba, gashin wa zan iya taɓawa, Mami ki mata sannu mana ba kiga ta rame ba?"

"Ba zan mata sannun ba, a kanta aka fara haila da za ta wani langaɓe ta na numfarfashi?, dalla tashi ka bar gurin nan, in ban yi da gaske ba ina ga nan gaba maƙale hannu zaka fara irin na 'yan daudu"

Jiniya ce ta cika layin, zuwa cikin gidan, wanda hakan ke almta cewar megidan ya dawo.
Chapter 19 · 0% Book details