← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 145

Sashe 108

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Allah ka sa idona ne yake mini gizo abin da na gani ba daidai ba ne, no ba zai yiyu ba ma, babu ta yadda za a yi kwana uku da yin arba'in ɗin Abra hakan ta kasance, na san ma ba gaskiya ba ne." Ta ƙarashe maganar tana girgiza kai cikin tsananin firgici, ban da bugawa da ƙarfi babu abin da ƙirjinta yake.

It's paid book. 09047871750
[11/4, 7:56 PM] Abk: A ruɗe Mami ta sake duba wayarta domin gani take kamar idanunta bai nuna mata daidai ba. Babu yadda za'ai ace hakan ta kasance domin ba abune mai sauƙi ba,
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku ni Na'ima" ta furta a fili lokacin data ƙara tabbatar da abin gsky bawai gizau ba amma zuciyarta ta kasa gasgata hakan.

Jikinta na rawa ta ƙara duba status ɗin Uncle Shureim a karo na babu adadi, ƙurawa Invitation ɗin idanu tai zuciyarta na bugawa da ƙarfi ganin sunan Major Khamal Khamis and Salima Ibrahim Haroon.
Zaman ƴan bori tai ta jima ba taga abin daya ɗaga mata hankali irin wannan ba, kafin ta dawo daga tunani ta ƙara ganin matar Uncle Shureim tai status da Invitation na ɗaurin aure ta saka

_Wish You all the best babban yaya, Ubangiji ya baku zama lafiya yasa matarka ce har Abada. I'm so happy mun samu abokiyar hira_

Da ƙyar Mami ta Ƙarasa karanta rubutun dake ƙasan Invitation ɗin sbd yadda jikinta ke rawa da ɓari tashin hankali ya bayyana saman fuskarta shin da gaske ne? ko ƙarya ne? ko dai wani ne mai irin sunan mijinta,
But how can that be possible ta ya ya ne Major zai aure ba tare data sani ba?
Ganin kanta na neman kullewa na rashin gane gskyar abun yasa Mami da sauri taiwa Matar Uncle Shureim reply da.

"Amin. But waye zai aure?" Matar Uncle Shureim ta jima tana dariya ganin rainin hankalin Na'ima sai kuma tai mata reply da.

"Abbin Salman da Marigayiya Abra kakan Aishatul-humaira" tai mata reply da hakan tana tun tsira dariya.

Da sauri Mami ta kashe datar idanunta na cika da hawaye baƙin ciki da kuma yadda Major yaci amanarta tare da ci mata zarafi da can bai mata kishiya ba sai yanzu?
Me kishiya zata zo yi a cikinsu? Kishiyar ma wannan tsinanniyyar karuwar Salima. Number Anuty Suwaiba ta kira tana É—auka ta fashe da kuka sosai tama kasa magana baki É—aya.

Daga cikin wayar Anuty Suwaiba taja tsaki cikin faÉ—a ta ce "Mtwss Malam kin kira kuma zaki cika mini kunne da ihun banza wani abin ne ya faru? domin nasan wannan gidan naki baya rabo da issues kamar gidan haya ko yari" cikin kuka Mami ta ce.

"Na shiga uku Anuty Suwaiba Major Aure zai, kishiya zai yi mini dame zanji da rashin Abra ko da kula da Aishatul-humaira ko da masifar kishiya ba zan iya ba" kuka take sosai kamar ranta zai fita batun auren Major ya Girgizata ya zo mata hanyar da sam ba tai tunani ba.

"Aure? Shi ne yace miki aure zai ƙara?" "Ai ya shige wai, domin Shureim da matarsa sun ɗora Invitation na ɗaurin a status ɗinsu, kuma matar Shureim ta tabbatar mini da hakan,
Yanzu Abbin Salman ya kyauta mini kenan? Dame na ragesa tun ina amarya bai yi mini kishiya ba sai yanzu samu jika?"

Tsaki Anuty Suwaiba taja kafin ta ce "Matsalata dake rashin tunani wani lokacin Na'ima, wace jikar waye kuma ya haifa miki, ai da baki gangancin riƙe Abra tun farko ba da Khamal bai isa ya rainaki har haka ba,
Kin riƙe uwa yanzu zaki riƙe abin data haifa kamar baki san ciwon kanki ba wlh....," da sauri Mami ta ce "Look Anuty Suwaiba shawara na kira ki bani akan wannan mugun abin dake shirin faruwa dani, a baya nayi Kuskuren riƙe Abra da zuciya ɗaya, yanzu kuma nayi ladama riƙon da naiwa Abra ba shi zanwa Aishatul-humaira ba, da zuciya ɗaya zan riƙe ta,
Ki bani shawara kawai idan zaki bani idan kuma ba zaki iya ba shikenan but please ki daina sako mini zancan Abra kina fama mini mikin dake zuciyata ne"

"Ok haka kika ce? To kada ki sake kirana akan issues ɗinki tunda kina gani ba zan iya miki komai ba ki zauna kici miji tare da yaran riƙo" tana faɗin hakan ta kashe wayar.

Abin duniya yaiwa Mami yawa sai kawai ta fashe da me tai maka mene yasa zai mata kishiya bayan yanzu basa samun saɓani.
Sai da tayi kukanta ya isheta kafin ta tashi sbd kukan Aishatul-humaira da yaji.

Yana kwance saman Royal bed ya rufe idanunsa tare da rungome pillow. A yanzu ko sarari tunani bashi da shi, ya daina surutai da kiran Abra. Amma ya tattara komai ya ajiye a cikin zuciyarsa.
Ba zai taɓa yafewa kansa ba akan cutar da Abra dai ya yi, abubuwa da yai mata sai dawowa cikin ƙwaƙwalwarsa suke. Runste idanunsa yai sosai sbd tuna mganarta da yai.
"Ka barni a jikinka ɗomin jikinka nake buƙata" ƙankame pillown yai yana jin kamar ya kurma ihu amma ba hali Allah sarki a lokacin ita kaɗai ta san me take ji a jikinta.

A hankali aka turo ƙofar bedroom ɗin nasa, Hajiya Mama ce ta shigo riƙe da mug wanda ta haɗa masa coffee a ciki zama tai gefen gadon cikin sanyin murya ta ce.

"Haba jarumin maza tun safe yau baka fito ba, are you okay?" Juyowa yai tare da mirginawa ya É—ora kansa a saman cinyar Hajiya Mama.

"Mama ba zama Mutumin ƙwarai ba bani da imani Mama" rufe masa baki tai tana faɗin "Subuhanallahi kul ka sake jin irin haka a bakinka Adnan,
Babu musulmin da babu imani a zuciyarsa, kai ta astagafirullah tare da neman yafiyar Ubangiji, akan laifukan daka aika ga Abra,
Ubangiji mai jini kuma mai gani ne zai dubi zuciyarka ya sassauta maka abin da kake ji, ina da tabbacin Abra ta yafe maka, ko baka nemi yafiya wajanta ba?"

"Na nema, amma na cutar da ita da yawa" shafa kansa Hajiya Mama tai cikin damuwa ta ce.
"Shi ya sa a kullum nake ce maka ka rage zafin zuciya Adnan, babu inda zata kai ka sai ladama yanzu dame hakan yai kama? Kada ka manta A'isha Yaya ta ce, she's my sister mene yasa ban É—auki mataki ba ni? Mene yasa Professor bai É—auki mataki ba a matsayinsa na mijinta sai kai?"
"Am sorry Mama nai laifi ki yafe mini"

"Ka nemi yafiyar Ubangiji Adnan, shi ne zai yafe maka laifukan ka, and wannan zaman naka ya fara damuna kada ka samu matsala da zuciyarka"
Tashi yai zaune sosai idanunsa akan Mama yace "Ina son komawa wajan aiki, idan ina zaune ni kaÉ—ai bana iya cire tunani Angel a raina"

"That's good ni ma hakan ya yi mini, yanzu ka sha wannan coffee ɗin kai wanka ka shirya ka fita ko lasvegas ne kasha iska" Girgiza kai kawai Adnan yai domin ya ɗauki Al'ƙawari duk abin da zai sanya shi farin ciki ba zai taɓa aikata shi ba, zai ta zama a haka har zuwa ƙarshen tasa rayuwar.
Coffee ɗin ya fara sha a hankali Hajiya Mama na kallonsa cike da so da ƙaunar ɗan yayar ta ta A'isha. Har mamakin yadda Abra ta sakawa ƴarta suna Aishatul-humaira tai. Yana gama sha ta fita da mug ɗin shi kuma ya shiga bathroom.

After 20 minutes.
Walking slowly ya fito daga part É—insa cikin wata dakakkiyar shadda amy colour wacce ta amshi dark skin É—insa yai kyau sosai amma ya rame sosai idanunsa sun faÉ—a sai dugun hanci. Murmushi Hajiya Mama tai ta ce "Allahamdulillah, Masha Allah First born and last born sai yanzu naji daÉ—i shalalena" ta faÉ—a tana rungomesa marairaice mata fuska yai kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce.

"Ina Abba?"
Juyawa tai sai kuma ta ce "Oh i almost frgt tafiyawta kama shi urgent he's alright left" "Mama me naiwa Abba ne haka? Idan zai tafiya duk sauri baya yi sai ya faÉ—a mini he has changed totally"

"No, kasan Abbanka bai iya fushi ba, yana cikin damuwa da abin da ka aikata wannan shi ne kawai" shiru yai ganin yadda ya sauya yasa ta tallafo haɓarsa ta ce "What again? Laifinka ne, amma kada ka damu kaci gaba da addu'a kana tura masa saƙon apologies ta E-mail nasa yana son ka dole zai sakko" kai ya jinjina ba tare da ya ce komai ba yana ƙoƙarin fita ta ce.
"Car key? Ina zaka bari na saka ai driving naka" idanunsa ya rufe a hankali ya ce "No Mama I can drive with myself ki mini addu'a" "To Allah ya tsare ya kai ka lafiya" da Amin Ya amsa tare da barin gidan.

A hankali yake driving sbd rashin ƙarfin jiki yana hanya Fayyad ya kira shi amma ya kasa picking call ɗin har ya Ƙarasa police station ɗin kai tsaye Ɓangaren I.G ya nufa. Mutane sai zubewa suke suna gaida shi tare da faɗin "Wlcm Back sir" Duk wanda yai masa ta'aziyya ko ta kansa baya bi, a haka ya ƙara wani office.

Cike da mamaki I.g ya miƙe tsaye yana sakin Murmushi na jin daɗin Sp Adnan Aliyu Matawalle zama sukai a hankali ya ce "Allahamdulillah, thank you sir" I.g ya ce "Good amma daka ƙara hutawa till now baka dawo daidai ba fa".

"No bad, am okay sir" shiru duk sukai can I.g ya ce "ina tun wani case na ɗan mafiya ɗin nan wanda ake zarginsa da sace yara yana cire wani sashi na jikinsu?" Adnan ya jinjina kai alamar ya gane domin da case ɗin a hannunsa "Ana zargin mutumin yana ƙauyen Samil babu da tabbaci sai mun bincika,kasan ƙauyen babu hawaye musamman yanzu lokacin siyasa kada a cutar dasu sosai".
Chapter 108 · 0% Book details