← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 145

Sashe 117

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Mama ta ce "Eyya, wannan abu bai yi daɗi ba, amma dan Allah ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, komai nufi ne na Allah. Allah ya baku zaman lafiya kiyi haƙuri" wata irin karaya ta kama Hajiya Na'ima, dan a kwanaki takwas ɗin ita kaɗai ta san da yadda ta yi su, gashi yau Major zai dawo wurinta, amma sam ko ɗokin hakan ba ta yi, saboda gaba ɗaya haushinsa ta ke ji.

"Ya na ji kin yi shiru?" Cikin raunin murya Mami ta ce "Ba komai".

"Na'ima, na san na fiki shekaru, kuma nima mace ce, ƙarewa am a Marriage counsellor, na san abin da ki ke ji, irin wannan babu daɗi, kinga sanadin 'ya'ya Allah ya riga ya haɗa mu, mun zama 'yan uwa, dan Allah idan zan baki shawara, kar ki yadda wani ko wata su ziga ki, a 'yar haɗuwar da muke yi, mijinki yana nuna miki soyayya, kiyi amfani da damarki kar ki ce zaki bar mata shi ki zuba musu ido, kiyi ƙoƙari ki riƙe fadarki a wurinsa, na san da ciwo amma ki yi haƙuri".

Mami ta yi ajiyar zuciya ta ce "To shikenan, na gode sosai".

"Yauwa, sauran maganar idan na zo ma tattauna".

"To shikenan Allah ya kawo ku lafiya, gaida Abban".

Hajiya Mama ta ce "Zaiji insha Allah".

Mami ta mayar da kallonta kan Little, da ta ƙura mata ido, Mami ta yi murmushi, ta janyo little tana shafa mata hoda a goshinta, daga ita sai Pampers.

Mami ta ce "Sweetheart, bari in miki video in turawa Daddynki Salman, na san yanzu suna lectures da mun yi video call ko?" Ta yi maganar kamar Little tana jin me take faÉ—a.

Ta É—auko Comb ta shiga tajewa Little uwar sumar da ta cika mata kai.

Ta ƙurawa Little ido, yarinyar tubarkallah, Allah ya yi mata kyau, ko sallama aka yi, Mami ɓoyeta take yi, ko yawan da ita ba ta yi, saboda baki.

Ganin Mami ta ƙura mata idanu ne ya sanya, ta fara dariya har dimples ɗinta suna lotsawa, sak kammaninta da Abra suka ƙara bayyana.

"Allah sarki Abrana, Allah ya yi miki rahama, ya raya mini abin da ki ka bari, ke babu ke, Faris ba ya kusa da ni, ga abin da babanku yayi mini, da muna tare da na san zaki tayani jin babu daɗin halin da nake ciki. Ina ma ban raba alaƙar da ke tsakanin ki da Faris ba, dama na bari kun yi Aure, kai na yi kuskuren da babu damar gyarawa" ta ƙarasa maganar tana hawaye. Sai da tayi mai isarta, sannan ta tashi, ta ɗau ado cikin wani rantsatsen leshi, ta sha ado sai zuba ƙamshi take yi, ta shirya Little cikin wasu haɗaɗɗun kaya sannan ta ɗauko wayarta ta kira Salman video call.

Murmushi ne ya bayyana a fuskar Salman, ganin kiran Mami, ya amsa kiran, murmushin fuskarsa ne ya ƙara faɗaɗa da ya yi tozali da fuskar Mami tare da little.

"Wow my little Angel, always looking so cute dear" Dariya little ta buɗe baki ta na yi, tana miƙa hannunta kan screen ɗin wayar.

Kissing É—in screen É—in system É—insa Salman ya shiga yi, yana É—agawa Little hannu.

"To mai 'ya, ko ta ni baka yi, sai 'yar ka ko?".

"Am sorry Mami, gaskiya am missing daughter Mami, ba kiga kamannin angel sun sake bayyana a jikin yarinyar nan ba, Mami ba zan zo in tafi da 'yata ba kuwa?"

"Say hi Daddy, My Angel look up, baki kamar na mamanta" yayi Maganar yana murmushi. Idonsa ne ya kai kan Mami, da idanunta suka cika da hawaye.

"Mamina, lafiya na ga idanunki kamar za ki yi kuka?".

"Salman na kiraka a waya, nace ina son ka zo da gaggawa amma ka yi burus ko Faris?".

"Mami ba burus na yi ba, muna daf da fara exams ne, kuma Abbi ne ya ce kar in zo".

"Ai tunda ya san abin da yayi mini, dole ya faÉ—i haka?".

"Mami me ya yi miki kuma?".

"Aure ya ƙaro, yau kwana takwas kenan, ya auro budurwa".

"Aure kuma Mami? Abbin?".

"Zan maka ƙarya ne Salman?"

Salman ya girgiza kai ya ce "Mami, na san Abbi ba zai taɓa yin abin da zai cutar da ke ba, dan Allah kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, kwanakin nan damuwa ta miki yawa, dan Allah kar ki bari wani ciwon ya kama mini ke Mami, dan Allah ki cire komai daga ranki" Mami ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, Allah ya bada sa'ar exams".

"Ameen Mamina, kiyi haƙuri dan Allah, kar ki ji haushin Abbi"
Murmushi ta yi mai ciwo ta katse kiran.

Ta miƙe tsaye, ta ɗauki Little ta saɓata a kafaɗarta, ta fito falo.
Tana fita falon ya gauraye da ƙamshi, hakan ya yi daidai da fitowar Abbi, tare da Salima.

Bin Mami da ido ta yi, ba ƙarya Mami akwai iya gayu.

Major ya yi mata wani lallausan murmushi ya ce "Wurinki zan taho ai, na zaci baku tashi ba".

"Ni na tashi tun É—azu" tai maganar tana nufar hanyar kitchen.

Salima ta ce "Honey dan Allah ko sau ɗaya a bani Little in ɗauka mana, tun da na zo gidan nan ban taɓa ɗaukarta ba".

Major ya ce "My dear, a taimaka a bamu aron Little mu É—auka mana".

"Duk abin da ya shafeka ban mata iyaka da shi ba, amma abin da ya shafeni da iyalina ni ya shafa, dan haka babu ruwanta da iyalina".

"Na'ima meye haka ne? Wannan wace irin magana ce kike yi?"

"Sai kuma kayi ai" ta wuce kitchen abinta.

Ƙarfe goma da rabi na safe, Adnan ya tafi hanyar wucewarta ya zauna, ya shafe a ƙalla awa ɗaya da rabi, sannan ya hangota, tana tahowa, yau buhu ne ta maƙalo hammatarta, tana tafe tana murmushe gyaɗa tana ci.

Tana tunkaro wurin taji ƙirjinta ya tsananta bugawa, ga kuma ƙamshin turaren sa da ya cika mata hanci, ji tayi kamar ta juya ta gudu gida, karta kuma haɗuwa da mutumin nan da ba ta da tabbacin mutum ne ko aljani.

"Budurwar ƙauye, ƙaraso mana kina tafe kina ciye ciye, ko kunya ba kya ji?"

Tsayawa ta yi cak tana kallonsa.

"Idan kika gudu ba zan kai ki wurin 'yar uwakki ba".

Ta yatsine baki ta ce "Ai na fuskanci raina mini hankali kake, yaudarata kawai ka ke, jiyan in shiga gida in fito da Inna ka gudu, ka sa ta dinga yi mini faɗa, har da zata kaini wurin masu ruƙiya aljani ya shiga jikina".

Dariya Adnan ya yi ya ce "kin manta yadda ki ka dinga wahalar da ni ne nima? Ai ramawa nake yi, yanzu ina zuwa?".

"Gona zani"

"Me zakiyi a gona kuma?"

"Roro zani".

"Kinga, yanzu muje ki fara rakani gidan Sadi".

Waro masa manyan idanunta ta yi "Taɓ kawai aje a gaya wa Inna an gani a layin gidan, duk fa 'yan farauta ne a wurin masu shaye-shaye".

"Na dai ga alamar ba kya son in nuna miki in da iyayenki suke".

"Wai kai sai ka yi ta amfani da wannan damar kana tursasani, yanzu aiken Innan zan fasa muje naka?"

"Hukunci ya rage naki ai".

Ta É—an tura baki sannan ta ce "Naji zan raka ka, amma da sharaÉ—i, nima zaka rakani gona ka tayani roro"

Shiru Adnan ya yi, sannan ya ce "Na amince"

"To muje, kuma daga baya zan tsaya in nuno maka gidan in dawo, dan karnuka ba zasu cinye ni a banza ba"

Nan ta yiwa Adnan jagora, suka nufi hanyar gidan Sadi ɗan kunama, wato baban yaron riƙaƙƙen ɗan ta'addan da ya addabi ƙasa tsawon shekaru.

Cin gyaÉ—arta ta cigaba da yi, Adnan ya fizge ledar gyaÉ—ar ya jefar ya ce "Ke kamar ba mace ba, ko kunyar ciye ciye ba kya ji?".

"Kaga nifa ba zaka takurawa rayuwata ba gaskiya, kai Wallahi da gani mutum ne mai son kai, wannan 'yar uwa tawa da gani tana haƙuri, ka fiye masifar tsiya Wallahi".

Jikin Adnan ya yi sanyi da jin abin da Afra ta faÉ—a, sai ya kasa ce mata komai sai cigaba da bin ta da ya yi.

Sai da suka zo daidai wata ƙatuwar bishiyar tsamiya, ta ja ta tsaya ta kalleshi ta ce "Kaga hanyar can, da wancan karen me baƙin baki yake kwance? To duk wanda ka tambaya zai nuna maka gidansa".

"Muje ki nuna mini mana".

"Ai Wallahi ko me zaka yi, taku ɗaya ba zan ƙara ba, duk fa Mutanen banza ne a wurin"

"Alright, hakan ma na gode".

"To dan Allah yaushe zaka je wurin Inna ka gaya mata, muje ka kaini in ganta, ni ko ba 'yar uwata ba ce, dan Allah ka kai ni in ganta, ka ga kan in mutu dai na ga wani nawa a duniya"

"Ina wanda ya tsinto ki?".

"Ba nace maka ya rasu ba"

Adnan ya yi ajiyar zuciya ya ce "To ke a ina aka tsinto kin?".

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Nima ban sani ba ni dai kawai yadda na ji labari, Baba ne ya tsinto ni, ya kai ni gidansa, sai ya je wurin 'yan sanda ya gaya musu ya tsinci jaririya, sai suka ce yaje Allah ne ya bashi. Sai Baba ya ce musu, ba wani bincike da za ayi? Sai suka ce ba yau aka fara haihuwar shegu a yar ba, dan da gani wannan kyan nawa ta hanyar banza aka sameni, ba lallai a samu iyayena ba, dan sun samini suna Afra saboda kyauna, yaje in zai riƙe sun bashi, to daga nan ya riƙeni ya sani a makarantar boko ai ta cewa bani da iyaye, samari da yawa na sona, amma saboda tsinto ni aka yi, sai su fasa aurena, wani ɗan gidan ɗan majalissa ne ya ce zai aureni, babansa ya ce bai yadda ba, da ƙyar babansa ya amince, an kusa kawo kuɗin Auren kuma, yayi hatsari ya mutu, kallon fa shegiya ake mini a garin nan" ta ƙarasa maganar fuskarta ta jiƙe da hawaye.

Hanky É—insa ya ciro a aljihunsa, ya shiga goge mata hawayen fuskarta.
Chapter 117 · 0% Book details