Sashe 119
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hawaye Salima ta ƙaƙaro cikin kissa ta ce. "Ban san me ya sa ba ta son na ɗauki little ba, ko na yi mata wani lefin ne ban sani ba, ni kuma ina da son yara, shi ya sa bana zuciya na ƙi ɗaukar tata." Duban Na'ima dake huci ya yi ya ce. "Na'ima ke kika haifi yarinyar nan ne ko ke kaɗai aka haifawa ita? Abra is my daughter, ke da Salima kuma duk matana ne, don haka yadda kike da iko da abin da Abra ta haifa ita ma haka, don haka kar na ƙara jin wata rigima ta tashi don ta ɗauki little."
"Wallahi ba zai yiyu ba, Abran ai ni na riƙe ta ba wata can ba, don haka nike da iko da abin da ta haifa."
"Okay, abin da na faɗa ne ba za ki bi kenan? To cigaba kar ki fasa, kar ki ɗauka wai na sauya ne daga Khamal ɗin da kika san ni saboda kwana biyu ina ɗaga miki ƙafa, fitina ce kawai bana so." Ya yi maganar cikin fusata.
Miƙewa Salima ta yi ta kama hannun Abbi tare da kwantar da kanta a jikinsa, cikin muryar rarrashi mai cike da salo da shagwaɓa ta ce. "Honey please ka bar maganar, in dai little ce ba zan ƙara ɗaukar ta ba." Bai ce komai ba sai gefen fuskarta da ya shafa cikin ƙauna.
Tsaki Nai'ma ta ja ta yi wucewar ta part ɗinta, zuciyarta cike da tuƙuƙin baƙin ciki da kishi. Tana shiga ɗaki ta goye A'isha Humairah sannan ta ɗauki wayarta ta kira Aunty Wasila, bayan ta ɗaga ta fashe mata da kuka.
"To uwar kuka, yau kuma me ya faru?"
"Na gaji Aunty wasila, na gaji da zaman baƙin ciki da ganin takaici, wallahi zuciyata ba za ta iya ɗauka ba, idan aka cigaba da haka watarana sai dai ku zo ku tarar da gawata."
"Yanzu dai faÉ—a mini mene ya faru."
Cikin gunjin kuka Mami ta ce. "A gabana fa Khamal yake nuna wa yarinyar nan k'auna, ya rungume ta ko ya ba ta abinci a gabana ba komai ba ne a gurin shi, washegarin da aka kawo ta da yamma har da fitowa main parlour tana tafiya ƙafa a tale, a dole sai ta nuna mini an ɓurma ta, iskanci dai kala-kala."
"Ke ma sai ki tsuro da naki salon, mijinki ne fa, kin fi kowa sanin shi, ai kowa ya iya allonsa ya wanke kawai, amma kya zauna kina wani koke-koke, har yanzu ba ki bar shashancin nan ba Na'ima? Sai ka ce a kanki aka fara kishiya? Duk kin fice daga hayyacinki."
Shiru Mami ta yi ba ta ce komai ba, ita kaɗai ta san halin zafin kishin Mijinta da zuciyarta take ciki, idan ta ga Abbi tare da Salima sai ta ji tamkar ta shaƙe su saboda tsananin baƙin ciki, ga yarinyar da shegiyar kissa da iyayi da firirita.
Washegari da safe Nai'ma ta fito don haɗa wa kanta breakfast ta tarar da Abbi da Salima zaune akan dinning suna cin abinci a cikin plate ɗaya, Salima sai nanaƙe shi take tamkar za ta koma cikinsa, shi kuma sai jifan ta yake da wani irin kallo ƙasa-ƙasa. Wani irin abu mai kaifi da zafi ne ya soki zuciyar Mami, mijinta abin son ta wanda suka shafe fiye da 20 Years tare amma yau shi ne yake soyayya da wata macen da ba ta fi Yar cikinsa ba a gabanta, ji ta yi tamkar ta juya ta koma part ɗinta, amma dai ta ɗaure saboda kar a gane halin da take ciki ta nufi kitchen, cikin yaƙi da hawayen dake ƙoƙarin fita daga cikin idonta. Kamar yadda ta yi tamkar ba ta gan su ba haka su ma suka yi, sai Salima ce ta bi ta da kallon gefen ido tare da sakin wani munafukin murmushi.
Rasa abin da za ta girka ta yi, yunwar da take ji ma nemar ta ta yi ta rasa saboda mugun ganin da ta yi, tana hawaye ta dafa noodles guda É—aya ta juye ta a plate ta fito bayan ta goge hawayen fuskarta. Kakarin aman da Salima ta fara ne ya sa ta tsayawa cak ganin ta tashi ta shiga toilet É—in dake parlour'n da sauri, a ruÉ—e Abbi ya bi bayan ta yana faÉ—in "Lafiya Baby? Me ya faru?" Ba ta ba shi amsa ba sai da ta gama aman, kamo ta ya yi suka fito yana yi mata sannu, har lokacin Nai'ma tana parlour'n a tsaye ta kasa tafiya.
"Baby ko na É—auko key É—in Mota mu tafi asibiti ne?" Ya yi maganar yana shafa bayanta.
Ƙara lafewa ta yi a jikinsa tana kallon Mami cikin yamutsa fuska ta ce. "A'a Honey ba wani abu ba ne, kawai ƙamshin turaren da Maman Salman ta fesa ne bai mini ba, tunda ta fito cikina ya fara hautsinawa, da ta dawo kuma sai na ji abin ya tsananta." Duban Mami Abbi ya yi cikin ko in kula ya ce. "Please ki daina saka turaren da kika sa, kin ga ya sa Baby amai, ko kuma idan kin san ki daina fitowa parlour idan tana nan." Ya ƙarashe maganar tare da kama hannun Salima dake ta toshe hanci suka bar parlour'n. Tsananin baƙin ciki da takaicin da Mami ta ji ba zai misaltu ba, ba ta san lokacin da ta saki plate ɗin hannunta ba indomien ta baje a ƙasa ba, cikin kuka mai cin rai ta yi part ɗinta da gudu.
"Doctor magana fa nake maka ka mini shiru, haba, I'm tired da wannan sabon halin da ka tsiro da shi, gaskiya."
"Na miki dole ki zauna da ni a hakan da nake ko kuma na ɗaure miki ƙafarki ne na hana ki tafiya? Idan ba za ki iya ba you are free to go."
Cikin tsantsar mamaki da shock Hajiya Saudat ta ce. "Yusuf! Yau ni kake fadawa ba ka ɗaure wa ƙafa ka hana ni tafiya daga gidanka ba?"
"Uwata ce ke da ba zan faɗa miki haka ba?" Ya yi maganar yana jifan ta da wani mugun kallo, kasa magana ta yi saboda tsananin al'ajabi. Dogon tsaki ya ja ya ɗauki coat ɗinsa da briefcase ya bar mata ɗakin. A wahalce ta yi zaman ƴan bori a ƙasan ɗakin jin kanta na juya mata, wata irin mummunar faɗuwa gaba ce ta ziyarce ta, lokacin da wani tunani ya ɗarsu a ranta.
Daga yanayin yadda ya shigo asibitin ma'aikatan suka san babu lafiya, dama kwana biyu zuciyoyinsu cike suke da mamakin rashin zuwan shi Asibitin, kasancewar wannan ne karon farko da hakan ta taɓa faruwa. Suna gaishe shi amma ba ya amsawa, fuskarsa a cukule ya ƙara office ɗinsa. After 30 minutes ya aiko a kira masa Nurses and doctors ɗin dake asibitin. Bayan sun hallara ya dinga kiran su ɗaya bayan yana ba su wani envelope. Fuskokinsu cike da mamaki suke baro office ɗin.
"Na shiga uku! Takardar sallama fa na gani." Cewar Nurse Basira cikin tashin hankali.
"Ni ma haka." Sauran Nurses É—in gurin suka haÉ—a baki gurin faÉ—ar haka.
Kafin su ƙara magana wani likita ya fito daga office ɗinsa fuskarsa ɗauke da tashin hankali, yana share zufa ya ce. "Don Allah ko kun san laifin da na aikata da na cancanci kora a asibitin nan? A sani na ni dai ban yi komai ba."
"Ai ba kai kaÉ—ai aka kora ba, mu ma nan duk korarraru ne."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, to me yake damun Doctor Bulama? Me aka yi masa da lokaci É—aya zai kori fiye da rabin ma'aikatan shi? Anya lafiya kuwa?"
"Ƴar Baba ki je ki ɗebo mana ruwan nan, ko na shiga banɗaki fa babu a gidan nan."
Diddire ƙafa ta fara yi tare da faɗin. "Wai don Allah Inna da girmana zan fita ɗiban ruwa? Salan a raina ni."
"Ni zan fita in É—ebo kenan? Don yau É—aya mai É—ebowar ba ya jin daÉ—i shi ne ba za ki fanshe shi ba? Shi ba mutum ba ne kenan da kullum yake É—ebowa kike facakar ki da shi."
Ba ta kuma magana ba ta figi mayafinta ta É—auki botikan É—iban ruwan da guga ta fice kamar za ta tashi sama.
"Budurwar ƙauye."
Ta tsinkayi muryar Adnan a kanta yana kiran ta. Tsayawa ta yi amma ta ƙi juyawa ta kalle shi, sai cuno baki take kamar zai taɓo sama.
"Ni fa ba sunana budurwar ƙauye ba, ba haka Babana ya raɗa mini ba gaskiya."
Murmushi ya yi ya ce. "Ina zuwa da wannan botukan?" Ya soso mata inda yake mata ƙaiƙayi, hakan ya sa ta shagwaɓe fuska ta ce. "Yaya Musa ne ba shi da lafiya, shi ne Inna ta ce wai yau ni zan ɗebo ruwa."
"Ina ne gurin É—ibar ruwan?"
"Bayan nan ne." Ta yi maganar tare da nuna masa hanyar.
Bai ce komai ba ya karɓi botikan suka jera suna tafiya. Gurin ɗiban ruwan rijiyoyi ne da yawa, mutane mata da maza kowa ya zira gugansa yana ɗiba. Ƴar Baba na zira guga Adnan ya karɓa ya fara janyo ruwan yana zuba mata a cikin botikan, bayan sun cika ya ɗauka ya kai mata har ƙofa gida, ita kuma ta ɗauka ta shiga da shi ciki. Haka suka dinga yi har ƴar Baba ta cika komai na gidan.
"To ko ke fa, ba ga shi har kin gama ba, sannu Allah ya saka da Alkhairi, amma yau kin yi sauri, hala babu layi ne a gurin?" Inna ta faɗi haka lokacin da Ƴar Baba ta dire bokitin ƙarshe.
"Ke dai ba na deɓo miki ruwan ki ba?"
"To ai na ga da in kika tafi É—iban ruwan sai ki wuni akan bokiti É—aya, kina ta neman magana a can."
Tura baki ta yi ba ta ce komai ba ta fita gurin Adnan dake jiran ta a waje. ganin yadda duk ya jiÆ™a wandon jikinsa ya sa ta kwashewa da dariya har da Æ™yaÆ™yatawa. Æata fuska ya yi ya ce. "What's funny?" Girgiza kai ta yi tana cigaba da dariyar. ÆŠage kafaÉ—a ya yi ya ce. "Gurin Inna na zo mu yi magana a kan ki, sannan in sanar mata iyayena za su zo neman aurenk.."