← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 145

Sashe 91

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SP Adnan a gajiye ya dawo gida, saboda wani ƙauye suka je aiki, ya sha zirga-zirga, salla kawai yayi, ya duba fridge ya samu sauran juice da Abra take haɗawa ya sha.
Bai nemi wurin da Abra take ba, ya shige É—akinsa ya faÉ—a toilet dan yayi wanka, amma ya ga kayansa a cikin bokiti a banÉ—aki.
Jinjina kai yayi da jinjina yadda Abra ta koyi taurin kai, wankansa yayi da niyyar ya kammala ya ci Abinci, ya ci ƙaniyar Abra.
Sai dai bai ƙara tsinkewa da lamarin Abra ba, sai da ya duba ya ga ba tayi girki ba, ya duba kitchen ma bakomai.
  A fusace ya nufi ɗakinta, yana zuwa ya tarar da ita a duƙunƙune cikin hijjabi tana ta bacci. Ƙafarsa ya sa yana takata ta tashi, amma ko motsi ba ta yi ba, baccinta kawai take.
Yasa hannu ya É—agota yayi wurgi da ita, zafin buguwar da ta yi ne ya sanya ta farka cikin wani irin razani. Adnan ta gani a gabanta yana wani irin zazzare idanu.
"Dame kike taƙama har kike mini wannan iskancin a gida? Baki girki da safe ba, na bar miki wanki ba kiyi ba, dan kin mai da ni ɗan isaka, shine kika kai kayan banɗakina kika watsar, kuma still ba ki girki ba, me kike nufi?" Ikon Allah kawai take kallo, yadda yake ta zazzaga bala'i, babu alamar ma zai bata damar kare kanta.
Sai da yayi ya gama ba tace uffan ba, ta miƙe a hankali ta fara ƙoƙarin gyara zaman towel ɗin jikinta.
"Am i not talking to you Abra?" Ya sake tambayarta cikin tsawa.

Hannayenta biyu ta sanya ta toshe kunnuwanta, dan ji take kamar a cikin kanta yake wannan ihun. Ganin ta toshe kunne ya sanya ya kuma harzuƙa, ya sauketa mata wani wawan mari a kan hannunta da toshe kunnen, wani irin zafi ya ratsata ta shiga zubar da hawaye, amma taƙi ce masa uffan, hannunsa ya sanya ya shaƙeta yadda ba zai mata illa ba ya ce "idan har kika cigaba da ƙoƙarin bijirewa umarnina a cikin gidan nan, Wallahi wahala zaki sha a gidan nan, sai kin gwammace kiɗa da karatu". Ai yana tsaka da maganar ta kyalayo masa amai a jikinsa, kallon Abra yayi cikin tsananin baƙin ciki ya hankaɗeta ta faɗi ƙasa, ta cigaba kakarin amai, sai dai babu komai a cikinta.
Ya kalli hannunsa da jikinsa da ta ɓata amai, cikin takaici ya ce "Ƙazamar banza mara hankali" Ko ɗaga kaia ba tayi ba balle ta tanka masa, ya ƙare mata zagi ya fice.

Gefe ta koma ta kwanta tana haki, saboda yadda ilahirin jikinta ke ciwo, tunani ta shiga yi a ranta, anya ba zata gudu ba, ko ta sanarwa Abbi irin halin da take ciki ba, sai kuma tayi tunanin dole Abbi zai shiga damuwa ya ga daga aurar da ita, har an fara samun matsala dan ta san tabbas sai ya kashe Auren nan. Tayi tunanin ko ta gayawa Abbi Adnan ya san waye mahaifinta, sai kuma taga idan har ta gayawa Abbi, to lallai fa zai gane irin zaman da take da Adnan, wanda hakan ne bata so, ba zata so ace daga yin Auren ace har Auren nata ya mutu ba, a fara lissafa mata Aure.

"Ohhh Allah, Allah ka bani mafita. Faris come back to me, i need your help, kar wannan macucin ya kashe ni, bana son ɗagawa Abbi hankali, da saina kashe Auren nan" ta ƙarasa Maganar tana jin zafi a ƙirjinta.

Na'ima Allah ya taimaketa ta koma gidanta, sai dai sam Major Khamal yaƙi bata fuska, ƙarewa idan ya fice tun sassafe ba zai dawo ba, sai can dare, ta shirya ta tafi sashinsa da nufin bashi haƙuri kamar yadda ta saba idan sun samu saɓani, amma ya koreta ya ce ta fita ta bashi guri.
Gaba ɗaya zaman gidan sai yayi mata babu daɗi, ta san da yaran nan suna nan ko dan Albarkacin su kar su gane Akwai abin da yake faruwa zai haƙura, amma Yanzu da yake ba kowa sai ita kaɗai yaƙi saurarar ta, dan da alamu yayi fushi sosai da ita a wannan karon.
Babban abin da ya sake jefata cikin damuwa shi ne yadda ya ce sai dai taje China ta nemo Salman, dan ba abin da yayi masa zafi da cewar da Salman yayi ba zai sake dawowa Nigeria ba. Gashi yanzu ta hankalta ta dawo daga rakiyar shawarwarin Anty Suwaiba dan ba in da shawarwarin na ta ke kai ta sai tashar Nadama!.

Abra baiwar Allah, kwana biyun nan haka tayi su cikin tsananin ciwo, zazzafan zazzaɓi da amai ba ƙaƙƙautawa, ga bata iya cin komai, dan komai ta ci sai tayi amansa, Adnan kuwa ya daina ko zuwa in da take, idan ma ya zo sai dai ya tsaya daga bakin ƙofa ya zazzage mata masifa ya barta.
Da safe ya shiga ɗakinta, ya tarar ta fito daga wanka, tana zaune a bakin gado, duk ta zabge ta rame sai idanuwa, so take ta shafa mai a jikinta amma ta kasa, hawaye ne kawai ke fita daga idanunta, kanta kamar zai tsage, dan bayan zazzaɓi har da damuwa ke damunta, saboda haryanzu zuciyarta na ƙuna akan rashin sanin haƙiƙanin suwaye iyayenta, ga Adnan ya sani amma azabar muguntarsa ya sanya ya ce na zai bari ta haɗu da su ba, kuma ko ta sanar da Abbi cewar Adnan yasan in da iyayenta suke, Adnan zai iya ƙaryatawa, dan ba ƙaramin makiri bane.

"Ke! Nifa na gaji da wannan halin naki, ba zai yiwu na ajiye ki a gida, amma kullum sai na nemi abin da zanci ba, saboda baki da lafiya dole ki mini Abincin breakfast yau na gaji".

Ɗauke kanta tayi, ta juya masa ƙeya, mai ɗauke da uban gashinta baƙi siɗik da ya sauka a kan gadon bayanta.

"Ina miki magana kike juyowa mini wannan banzan gashin naki?".

"Me kuma gashi na yayi maka, ko da yake ba abin mamaki bane, maybe burgeka yayi".

"Meye abin birgewa a jikin duk wani abu da ya danganci zuriyarku, masu kyan ɗan maciji, miyagu azzalumai, ai duk wani abinda ya shafi mahaifinki muninsa ya ƙazanta".

Cikin ƙarfin hali ta ce "Ai da yake gwano ba ya jin warin jikinsa, kai meye marabarka da miyagun maganganun da kake suffanta mahaifina da su? Wataƙila ma gara shi, baya neman matan banza, kai kuwa fa har karuwa ka kawo cikin gidanka dan abin kunya da.....
Damƙe gashin kanta yayi, wanda azaba ya sanya tayi shiru, saboda tsananin zafi da ciwon da kan yake mata. Cikin tsantsar mugunta da rashin imani, ya cire towel ɗin jikin Abra, ya fara ƙoƙarin kwanciya da ita, duk da yadda yake jin wani irin hucin zafi da jikinta yake mata saboda ciwo.
Kuka take sosai tana ƙoƙarin ƙwatar kansa, tare da kai masa duka, amma jikinta babu ƙwari, yayi abin da ransa yake so, cikin zallar mugunta tana kuka tana wani irin kakari na wahala, amma ko a jikinsa, sai da ya gama ya kalleta yana wani shu'umin murmushi ya ce "Idan nace zan gwada miki irin mugunta da zaluncin da mahaifinki yake yi, to mutuwa zaki yi, dan ba zaki rayu ba, zaluncinsa ya wuce duk wani tunani naki, ki sa a ranki ni ban iya komai ba a kan mahaifinki"
Ido shine kaɗai abin da Abra ta iya raka Adnan da shi, ba ta san da ya zata misalta irin uƙubar da yake mata ba. 'Haka zaki zauna abubuwa na cigaba da kwaɓewa?' wata zuciyar ta tambayeta.
Tana jinsa ya tada motarsa ya bar gidan, ta kai awa biyu a kwance, ko ƙwaƙwaran motsi ta kasa, daga bisani ta tashi da ƙyar ta shiga banɗaki ta gyara jikinta ta sanya kaya, ta duba tana da kuɗin da aka babbata lokacin da za'a kawota, ta zuba a jakarta ta nufi gate ta fice, wanda tun da aka kawota bata taɓa fita ita kaɗai ba.

LITTAFIN KUÆŠI NE, KU SIYA KAFIN KU KARANTA.
0808102134
09047871750
[10/25, 4:54 PM] Abk: Tana tafe a hanya kamar za ta kifa, unguwar kamar quaters take, ita ko maƙotanta ba ta sani ba, dan Adnan bai bata damar ko sallama tayi musu ba da aka kawo ta, da ƙyar ta kai titi, dan ta huta babu adadi.

Duk wasu shedu da yakamata, an tattara su a kan General Ibrahim mai retire,ya tabatta shine ya kashe karuwarsa a Hotel, kuma shike maƙarƙashi na bayyanar da sirrin tsaron ƙasa, dan haka yau Litinin ta kama ranar yanke hukunci, tun ranar Asabar Abbi ya tafi babban birnin tarayya Abuja, dan ganin shari'ar, Gwaska kuwa ya cika wandonsa da iska, ya bar Nigeria gaba ɗaya sai wasu daga yaransa aka kama.
Abin kunya har da tsofaffin manyan 'yan siyasa, da suka riƙe manyan muƙamai a ƙasa a wannan almundahana da aka aikata.
Bayan dogon turanci irin na kotu da alƙali ya gabatar, da faɗan manyan dokoki da ga cikin littafin da suke dogaro da shi gurin shari'a, aka yankewa General Ibrahim mai retire kisa ta hanyar rataya, abin da ya ƙara bawa mutane mamaki shine, hatta Manyan ƙusoshin gwamnatin nan, da aka samu da laifi hukuncin kisa aka yanke musu, abinda ba'a taɓa yi ba a ƙasa, amma aka basu damar ɗaukaka ƙara.
General Ibrahim duk ya rame, tsufansa ya fito, ga shi zamansa a gidan yari, cututtuka suka baibaye shi, yana ta fama da ciwon zuciya da kuma ciwon sugar.
Nan da nan jaridu da gidajen rediyo suka samu abin faɗa, ga lawyoyi duk sun karɓe masa 'yan kuɗaɗensa akan cewar zasu taimake shi yayi free.

Adnan tun da ya tafi gurin aiki, sai tunanin yanayin da ya bar Abra ya dame shi, saboda jikinta da zafi sosai kamar wuta, kuma babu alamar tana iya cin wani abu.
Tsaki yayi tare da ƙoƙarin cire tunaninta daga ransa, amma ya kasa ko yayi yinƙurin cigaba da aiki, da ya tuno ta sai yaji ya damu, ana haka Usman ya zo ya same shi a Office.
Yayi sallama amma maimakon Adnan ya amsa sai yayi tsaki, Usman ya kalleshi ya ce 'Lafiya kuwa ina sallama amma kana tsaki?".

Adnan ya kalleshi ya ce "Sorry, hankalina ne a wani gurin shiyasa".

"Ok, ya garin ya Madam kuma?".
Chapter 91 · 0% Book details