← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 145

Sashe 71

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Darling bee"
Hannunsa ya watsa yana ƙare mata kallo tare da ɗan matsawa kusa da ita he's trying to kiss her cheeks sai kuma ya ɗaga mata gira ya ce.
"Finally Bibina this is my house" "It's beautiful I like it but" hannunta ya kama ya ce "but what? Say it" rungomesa ta yi sosai ta ce "isn't ur house is our house okay" holding nata back yai ya ce "Oh! I almost frgt sbd ke ma na gina gidan".

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" sune kalaman da suka fita da ga cikin bakin Abra a wahale. Ta kasa fahimta, ta kuma kasa gane inda kalaman mijin nata ya dosa "My Surry? Bibina? Our house? What does that means?" Idanunta da suka sauya kala da ga farin da suke da shi zuwa launin jaa ta buɗe da ƙyar tare da zuba musu idanu.
Frm Head to toe ta ke kallon wacce aka kira da Surry, a ƙalla zasu iya age mate da Adnan idan ma zai girmeta sai da shekara ɗaya ko watanni, daurewa ta yi cikin sassauta muryarta tare da ɗauke damuwar da ke zuciyarta, but under her heart sunan Allah kawai ta ke kira, wasu har ƙwace mata suke.

Kusa da Adnan ta ja ta tsaya idanunta akan Fuskar sa, shi kuma yana kallon Surry. "Sannu da hanya" shirun da ta ji ne ya sanya ta ƙara cewa "Wlcm Bebbb" dry Surry ta yi kafin ta kalli Abra sai kuma ta kalli Adnan ta ce "Bebbb ana kira" haɗe fuska ya yi sosai ba tare da ya ce komai ba. "Is she your wife?" "Waa?" Da hannu ta nuna masa Abra ta ce "I think tana buƙatar ka"

"Kin taɓa ganin wuta da ruwa sun haɗu?" Surry ta ce "A'a never" juyawa ya yi gaba ɗaya wajan Abra a hankali ya ja idanunsa ya lumshe kafin ya buɗe a nuste ya kai kallonsa ga fararen yatsun hannun ta wanda suka sha henna sai ɗaukan idanu suke, dugun wuyan ta maƙale da wata siririyar necklace mai ɗauke da red ɗin stone.
Jajayen laɓɓan ta wanda suke rawa da karkarwa sbd tsananin tsoro da kuma abin da zai iya zuwa ya dawo.

"Idan har wuta da ruwa ba zasu haÉ—u ba, ta ya ya ki ke tunanin zan iya kiran maid ina nufin Æ´ar aikin gidan da matsayin mata? Maid É—ina ce"

"Dam!" Zuciyar Abra ta buga a hargitse kuma ta ke duban Adnan muryarta na rawa ta ce "Ni... Ni... ni ce ƴar aikin naka? ina matsayin matar ka mene maka wacece ita?" Ta ƙare maganar tana riƙe ƙirjinta sbd yadda ya ke ɗa ga mata tamkar zuciyarta zata tsaga ƙirjinta ta fito haka ta ke ji, bai ce mata komai ba sai kallon Surry da ya yi ya ce.

"Lemme take a shower" tana rangwaɗa tare da juya ƙugu wanda duk shan magani ya fara lalata su ta Ƙarasa wajan Adnan ta na kama hannunsa tare da kwantar da kanta a jikinsa ta ce.
"Can I help you?" "Sure Bibi" kama hannunta ya yi suka nufi part É—in sa, sai da suka nisa Surry ta juya ta kalli Abra ta ce.
"Ki haÉ—a min Indomie with egg ta ji Attahiru"

Zubewa Abra ta yi tare da zaman ƴan buri a wajan kamar mahaukaciya haka ta fara kuka tare da kunce ɗaurin kanta tana hargitsa kanta, ko idanunta bata iya buɗewa sbd nauyin da Zuciyarta ta yi mata, a wahale ta riƙe ƙirjinta da hannu bibbiyu ta na ƙoƙarin hanasa ɗagawa, sbd ji ta ke tamkar ranta zai fita idan numfashinta ya shiga tare da ɗagawar ƙirjinta. Tun tana addu'a har ta kasa faɗin komai sai idanunta dake lumshewa bakinta na rawa a hankali ta sulale ƙasan carpet kamar sumammiyya.

Saukar ruwan mai tsananin sanyi a jikinta shi ne suka taimaka wajan farfaÉ—o da numfashinta wanda ya bar jikinta, kafin dawowa cikin hayyacinta taji saukar wani ruwan a jikinta wanda yafi na baya sanyi tamkar wanda ya ke É—auke da ice sbd sanyi.
Jikinta na kyarma da ɓari ta buɗe idanunta a tsaye ta gansa da ga shi sai farar Armless da 3Qauter sai ƙamshin Pur oud, Kallon sa ta ke kafin ta ce.

"Ka dubi girman Allah ka faɗa min abin da nai maka, bana da kowa a nan kai kawai na sani mene yasa zaka juya min baya a lokacin da nake tsanin buƙatar ka? Ka ɗauke min dukkan wani farin ciki da jin daɗina ta hanyar nuna rashin kulawa a gareni, kada ka manta a ni amana ce a gareka,ka faɗa min abin da nai maka nayi maka Al'ƙawarin zan gyara kuma na baka hqr" ta faɗa tana sakin kuka tare da kallon sa ta na haɗe hannaye waje guda alamar roƙo.

Kallon tsaf ya yi mata kamar ba zai magana ba, sai kuma ya ce "Ina girkin da sweetheart ta ce ki mata? Ko kin mata aikin ki ne?" Miƙewa ta yi tsaye zuciyarta na yi mata zafi, wani irin kishi ya rufeta har bata san lokacin da ta wurgawa Surry uwar harara ba. Da sauri kuma ta juya zata shige part ɗin ta.

"Idan har kika bar parlourn nan wallahi na lahira zai fiki jin daÉ—i Abra Khamal Khamis"
Cak Abra ta tsaya ba tare da ta kallesa ba, a wannan lokacin ba komai ta ke ganewa ba, ji ta ke inama ba zai auren ba, an faɗa mata daɗin aure an kuma faɗa mata duk soyayyar dake tsakani wata rana ana samun saɓani domin ko harshe da haƙori ana sabawa, balle mutum mai ɗauke da Zuciya wacce jiki ke gudana a cikinta.
Sai dai tunaninta ya samu tawaya ta wannan ɓangaren, babu abu mai muhimmancin kamar daren farko na rayuwar ma'aurata amma ita nata daren ya zo mata a yadda ba tai tunani ba, ta kasan fahimtar Dare da duhun da ke cikin al'amarin. Wanne al'amarin ya ke shirin faruwa acikin rayuwarta dama duniyar ta baki ɗaya?. DESTINY.

Wata zuciyar ta ce.
"Ƙaddara ta ki har nawa ne? U have to think Abra, think think think.... Ta tashi cikin rashin kulawar uwa, ta girma da ƙaunar ƙarninta farin cikin ta, lokaci ɗaya ƙaddara tai mata kutse cikin rayuwarsu aka rabata da jinin jikinta Faris, ta ɗauki ƙaddara ganin yadda Adnan ke nuna mata kulawa tare da yi mata Al'ƙawari kala-kala, hakan duk a cikin tsarin ƙaddarorinta suke? Ko kuma wani abun ke son faruwa ne?... Wani abu mai kama da JUYAYI.

"Heyyy You jakanesss"
Muryar Sp Adnan Aliyu Matawalle ya sauka a kunnanta a gigice ta dawo hayyacinta duk ba sosai ta jisa ba, hannunta na rawa ta taɓa kunnanta sai a lokacin ta ji hearing aid ɗin ne ya goce.

"20mints ya yi maki yawa wajan kawo sweetheart É—ina abinci" zaman hearing aid ta gyara idanunta cike da hawaye ta kallesa ba tare da ta ce komai ba.

"I'm i your mate da ina magana kika zuba idanu ko matar amarci ke damunki ki ke son cinye ni eye?" Murmushi kawai ta yi irin Murmushi da gwanda mutum ya yi kuka akan ya yi irinsa.

"Idan kai zanwa zan yi, it's my responsibility nauyin ka yana kai na, amma ba zan taɓa yiwa karuwar can abinci ta ci ba....,"

"Kauuu!! Kauuuu!!!"
Ya sauke mata wasu tagwayen maruka kamar kumurciu zaki haka ya ke huci idanunsa akanta ya ce. "How dare you da zaki faɗa min haka Ehh? Kada ki dama idan kin amsa Sunan Abra Khamal Khamis kiga, and wannan da kike maganar karuwa ko....?" Ƙwafa ya yi tare da juyawa ya kama hannun Surry suka shige ɗakinsa sai maƙale jikinsa ta ke tana sakin kuka ance mata karuwa.

Dafe kanta da ke juyawa mata tayi, da ƙyar ta ja ƙafafuwanta zuwa kicthen domin ko ta kansa bata sani ba, ganin da akwai komai ta ɗauki Onion da red pepper ta ɗauki Egg da Indomie, tana aiki tana tana sakin ajjiyar zuciya, ga jiri dake ɗaukanta.

"Yaya.. Angel Zanci Indomie Yaya please yunwa na keji"

"Yaya gidan wani zaki,kina gwarara jikin ki" "Angel waya saki aiki, ba Abbi ya ce ki daina aiki ba"

Ajjiyar zuciya ta sauke sbd wuƙar data ya ke. "My Angel kalli hannunki kin yanke, matsa zan yi aiki jeki zauna"
"I love You Angel wannan girki kamar a restaurant"

"Idan ban kula dake ba, waye zai kula dake ni ki daina ɗauka na matsayin ƙani kawai Yaya Angel"

Wani Uban Ihu Abra ta fasa lokacin da maganar Salman É—aya-É—aya ta shiga dawowa cikin kwakwalwarta tamkar yanzu ne muryarsa ke mata kuuwa a cikin kunnanta. sai da tayi kuka mai cin rai tana kiran sunan Salmanun-faris come to back to me zan bika duk inda zaka. Plate É—in Indomie ta É—auka, a Parlour ta samesu suna kallo da sauri ta ajjiye plate É—in jikinta na rawa tabar parlourn sai numfashi ta ke fitarwa, har dare bata sake fitowa bata da tabbacin a gidan suka kwana ko a waje?.

China.
A hankali ya ke tafiya kansa a ƙasa, hannunsa duk biyun zube cikin Aljihu, da ga shi sai wata ƙaramar black t.shirt wacce ta kama jikinsa, sai ƙaramin wando mai kama da trousers. Ƙafarsa sanye cikin wani baƙin takalmi me kyau. Gefen wani kogi ya ja ya tsaya inda ake shan iska ga few mutane a wajan kowa yana abin da ya ke gabansa.
Iskar data kaɗa ya sa shi rufe idanu tare da zame hannunsa guda ɗaya ya ɗora daidai saitin ƙahon zuciyarsa "fat! fat!! fat!!" Haka sautin bugawar ta ke badawa, idanunsa ya ware akan ruwan tare da ƙurawa wasu tattabaro idanu farare tas dasu mace dana miji, irin tattabaron nan ne masu kama da ɗawisu sun ɗaga jela sama tai wani scale kamar zanan love Wayarsa ya ɗauka tare da ɗaukan su a taushashe ya ce. "With my heart desires my dream" idanunsa ya ɗan sauya kala kamar zai kuka hawaye kwance a idanunsa ya ƙara sakin Murmushi a karo na biyu "happy married life Angel stay blessings with your husband not ur choice"
Chapter 71 · 0% Book details