← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 145

Sashe 118

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Angel, ke ba shegiya ba ce, ina da yaƙinin ke 'ya ce ta sunna, ina ga ke ce zaki dace kiga iyayenku, shiyasa Allah ya ɗauke mini Angel ya kawoni garin nan na haɗu da ke".

"Me kake nufi?".

"Twin sister É—inki da na aura, Allah ya yi mata rasuwa kwanakin baya, ta rasu ta bar mini 'yar jaririya mace" yayi Maganar hawaye na zubowa daga idonsa.
Zubewa ta yi a wurin ta É—ora hannu a kanta ta ce "Na shiga uku!"

₦300 NE DAN ALLAH KU SIYA KAN KU KARANTA MANA
08081012143
[11/12, 3:38 PM] Abk: Ƙasa Adnan ya yi da kansa cikin ƙoƙarin tsayar da hawayen idonsa amma ya ƙi tsayawa, ganin yadda yake kuka sai jikin ƴar Baba ya yi sanyi. Idanunta cike da hawaye ta ce. "Ka daina kuka, ba a son yi wa wanda ya mutu kuka, haka Inna take ce mini idan ina kukan rashin Baba." Bai ce komai ba sai da ya share hawayen fuskarsa duka, cikin raunin murya ya ce. "Ai za ki maye mini gurbin ta ko?" Turo baki ta yi ta ce. "Huh'um, wallahi ni ba na son ka, kalle ka fa baƙi." Duk da halin da yake ciki na tuna Abra sai da ya murmusa saboda yanda ta yi maganar.

"Shikenan, tunda kin fi so na auro wata ta riƙe mini ƴata, in ma muguwa ce ta cutar da ita idan bana nan."

Shiru ta yi kamar mai nazari tana kallon shi na wasu sakanni, taɓe baki ta yi ta ce. "Ina son ƴar taka, tunda ka ce ƴar'uwata ce ta haife ta, yaushe za ka kawo mini ita ko kai ni na gan ta?"

"Ranar da kika fara so na." Ya faÉ—a idanunsa a cikin nata.

Janye idanunta ta yi da sauri, cikin raunin murya ta ce. "Amma ka san iyayenmu? Me ya sa suka yarda da mu?"

"Ban sani ba, amma ina nan ina bincike akan hakan, ni da wanda ya riƙi Abra."

"Abra."

Ta maimaita sunan kamar mai tunanin wani abu a cikinsa. Kallon yadda rana ta fito Adnan ya yi ya ce. "Lokaci yana tafiya, mu je ki raka ni gidan Sadin."

"Gaskiya ba zan iya zuwa ba, ni roro na zan tafi, na san yanzu ana can ana ta yi, an kusa rore gyaÉ—ar ma duka ni ban je ba."

"Mu je na taya ki."

Kallon shi ta yi cikin mamaki ta ce. "Ai ba ka iya ba."

"Sai ki koya mini."

"Tom shikenan mu je."

Suna tafe yana tsokanar ta har suka ƙarasa gonar, wani irin farinciki da nishaɗi yake ji na kasancewa da ƴar Baba, ji yake tamkar Abransa ce ta dawo. Yara da manya damƙam a gonar, sun zagaye tumin gyaɗar kowa na roro. Cikin takaici Ƴar Baba ta dubi Adnan ta ce. "Ka ga har an cika ban zo ba, ni da nake riga kowa zuwa, kuma alƙur'an sai ka taya ni." Bai ce komai ba sai idanunsa da yake ba wa abinci yana kallon yadda ake roron gyaɗar. Ƴar Baba na ƙarasawa gurin aka fara kiran sunanta, ta kula wanda ta ga dama ta share waɗanda take jin haushi. Su kuwa ƴan ƙauyen sai kallon Adnan suke, cikin mamakin ganin shi tare da ƴar Baba, suna son su tambaye ta wane ne shi, amma yadda ta yi kicin-kicin da fuska ya sa kowa ya haɗiye gulmarsa bai fito da ita ba.

"Ka zo ka taya ni, ka tsaya kana kallo na." Ta yi maganar cikin sangartar ta.

Ƙarasowa ya yi ya tsugunna a kusa da ita ya ɗauki ganye ɗaya ya fara cire gyaɗar yadda ya ga suna yi cikin yamutsa fuska, a ransa yana tambayar kansa ko mene ne amfanin wannan abun?

Wasa-wasa sai ga SP Adnan ɗan gayu mai ji da kansa ya wuni a gona yana roron gyaɗa, don hana shi tafiya 'yar Baba ta yi da rigimar ta, Sallah ce kawai take tayar da shi, rashin sabo ya sa duk ya galabaita, kayansa suka yi futu-futu da ƙura da ƙasa. Ƴar Baba kuwa sai murna take gyaɗarta ta fi ta kowa yawa, saboda taya ta da Adnan ya yi. Sai da mai gonar ya zo ya rarraba ya ba wa kowa ladan roronsa sannan suka tafi, lokacin Magriba ta kawo kai.

Suna cikin tafiya 'yar Baba ta dube shi ta tuntsure da dariya, saboda yadda ya yi wani kalar tausayi, ga shi ya taka ƙaya a gonar da ɗingishi yake tafiya, ɓata fuska ya yi bai yi ce komai ba.

"Gaskiya kai rago ne, kana namiji amma ɗan wannan aikin ya wahalar da kai, ba ni kwanon abincina da robar ruwan idan ba za ka iya riƙewa ba."

Hararar ta ya yi tare da faɗin. "Idan na ba ki da wanne hannun za ki riƙe?"

"A kai nake ɗora buhun gyaɗata, sai na riƙe kwanon a hannu, haka nake yi kullum."

Jinjina kai ya yi, a ransa yana jinjina yadda mutan ƙauye suke shan wahalar rayuwa. Har ƙofar gida ya raka ta, har ta wuce za ta shiga gida ta dawo ta ce. "Yawwa na tuna, jiya na tafi kiran Inna shi ne ka gudu ko?"

Cikin gajiyar dake addabar jikinsa ya ce. "I'm sorry."

"Ba zan haƙura ba gaskiya, sai dai in ka yarda in kira Innar ta gan ka yanzu."

"Ki bari sai gobe, zan zo na gaishe ta my Angel, yanzu duk a gajiye nake, kin ji ma an fara kiran Sallah, ko da yake na ga ke duk wunin da muka yi a gona ba ki yi Sallar ba."

Murguɗa baki ta yi ta ce. "Ina ruwanka, dama saka mini ido kake yi." Murmushi ya yi tare da kama hannunta ya riƙe, idanunsa a cikin nata yana jifan ta da wani irin kallo.

"Na shiga uku! Don Allah ka cika ni, kar Inna ta leƙo ta gan ni ko Yaya Musa ya zo wucewa." Ta yi maganar cikin tsantsar tsoro da fargaba, idanunta duka a waje tana kallon zauren gidansu.

"Have a nice night, good bye, I love you."

Ajiyar zuciya ta sauke jin ya sakar mata hannu ta rarumi bugun gyaɗarta ta yi cikin gida da gudu a ranta tana gulmar Adnan. Inna dake alwala ta saki salati tare da faɗin. "Wai ƴar Baba kanki ɗaya kuwa? Da magaribar ma ba za kina tafiya cikin nutsuwa ba? Wunin yau bakina shiru amma yanzu daga dawowar ki zaki fara sa ni magana, me yake damun ki ne wai?" Ba ta ce komai ba sai da ta koma ta ɗauko kwanonta ta dawo, bayan ta zauna a kan kujera yar tsugunne ta ce. "Inna daga dawowa ta maimakon ki tarɓe ni da ruwan sanyi na randa da abinci amma sai ki fara da faɗa? Na je na gaji na wahala amma ko ki mini sannu."

"Ba zan yi ba, tunda ke yin abin da aka ce ki yi kike yi, yarinya kina girma amma kullum jiya i yau, ai ta maimaita magana ba kya ɗauka, sai dai ta shiga ta dama ta fita ta hagu, to in ma wani motsin ne a kanki gobe zan kai ki a miki roƙiyya a fitar."

"Taɓ, wallahi ba zan biki a zane mini jikina ba haka kawai." Ta yi maganar tare da miƙewa ta shige ɗaki.

A matuƙar gajiye ya ƙarasa gidan Hakimi, bai zauna ba sai da ya rage kayan jikinsa ya yi wanka ya shirya cikin ɓaddakama ta shiga irin ta matasan garin da kayan wani ɗan Hakimi da ya aro, bayan ya yi Sallah ya naɗe ƙafarsa da hanky, ya ci cakes ɗin da ya zo da su da lemo ya ɗauki torchlight da kuɗi ya fita. Da ƙyar yake iya tafiya saboda yadda ƙafar tasa ta ɗaure, ba ƙaramin cakar shi ƙatuwar ƙayar ta yi ba don da ƙyar ya iya zare ta saboda zugi da raɗaɗin da gurin yake masa a lokacin. Ba don dole ba da kwanciya zai yi a yanzu ya huta, amma aikin da ya zo yi ƙauyen ba na wasa ba ne, ga IG kullum sai ya tambaye shi akan ina aka kwana? Haɗuwa da ƴar Baba duk shi ya ɗauke masa hankali. Da ƙyar ya iya gano layin su Sadi ɗan kunama, yana shiga karnuka suka fara yi masa welcome da haushi..

"Kai, waye a nan?"
Muryar wani É—an tauri cikin shaye-shaye ta doki kunnensa.

Cikin ƙwarewa a aiki ya sauya muryarsa zuwa ta yan yawa ya ce. "Ni ne, abin zuƙa nake buƙata, an ce mini babu inda zan samu sai nan."

Haske shi aka yi da fitila mai haske ba tare da ya san waye ba, sai da suka ƙare masa kallo sannan wanda ya yi magana da farko ya ce. "Kawo silalla a baka abun duniya Baba." Bai ce komai ba ya zaro kuɗi ba tare da ya ƙirga ba ya ba su. Wiwi suka ba shi da wani abu a kwalba wanda ya tabbatar giya ce, karɓa ya yi ya zauna ɗan nesa da su yana kallon gurin cikin nazari, wani ƙaton gida da ya banbanta da ginin gidajen garin ya ƙurawa ido, ko tantanma ba ya yi nan ne gidan Sadi ɗan kunama.

Mami ce zaune a main parlour tana ba wa little abincinta, bayan ta ƙoshi ta kwantar da ita akan carpet ta shiga kitchen don ɗauraye bowl. Kafin ta fito amarya Salima ta shigo parlour'n cikin wasu matsatstsun kaya riga da wando, sai baza ƙamshi take. Ganin little a kwance ita kaɗai ya sa ta ɗauke ta cikin sauri ta fara yi mata wasa tana shilla ta tare da yi mata waƙa.

"Mamana kin fi ta kowa, Æ´ar fara kyakkywa, mai kama da mamanta."

"Malama ya za ki ɗaukar mini yarinya kina ciccilla ta sama a daren nan? Mene haka?" Na'ima ta faɗa lokacin da ta dawo parlour'n tare da ƙwace little a fusace.

"Ki yi haƙuri kar ki karya mata haƙarƙari."

"In na karya kina da asara ne? Haba, bana son maita, na ce bana son ana É—aukar mini yarinya amma don naci da rashin zuciya sai an É—auka."

"A'a, hayaniyar me nake jiyowa tun daga baranda? Lafiya?"
Abbi da ya shigo gidan ya tambaya idonsa akan Nai'ma.
Chapter 118 · 0% Book details