← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 145

Sashe 17

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankali a tashe tace  "Ina kayan haihuwar suke, mu tafi Asibiti wannan ai kin kusa haihuwa?"

Da ƙyar Na'ima tace "Cikin ɗakina, kan mudubi" da sauri Anuty ta nufi ɗakin Na'ima bata sha wahalar ganin kayan ba, tana ɗakko wa suka ci karo da Granny a Parlon.

Kallon tsaf Granny ta yiwa Anuty Suwaiba kafin tace "Ya na ganki duk a hargitse kamar wata taɓaɓɓiya Suwaiba?"

Kafin Suwaiba tace komai Ammi dake bayan Granny wanda zuwansu kenan tace "Badai haihuwa Na'ima tayi ba Suwaiba?"

"Haihuwa za tayi, Asibiti zamu tafi" Anty ta faÉ—a a gajarce tana nufar kitchen É—in.

Granny ta buɗe baki sosai tana girgiza kai tace "To mene ya kawo Bazawara gidan Kamalu kuma? Ina da labarin baƙin halin matar nan, yaza tazo tayi kane kane a gidan jikana kamar ita yake Aure?" Ammi dai ba tace komai ba, tabi bayan Anuty Suwaiba zuwa kitchen ɗin.

Se dai miƙewar da Na'ima za tai, tai nishi se ga jariri.

Ammi tace "Iko se Allah, tun farko be kamata ta zauna a gida ita kaÉ—ai ba ga watam haihuwa ya kama".

Ammi ta amshi jaririn hannun Subawai wanda yake ta tsala ihu, tai waje ta ba su guri, cotton da zaiton ta É—auka ta shiga goge masa jiki, cikin ikon Allah kuma mahaifa ta faÉ—o, Anuty ta gyara wajan tass, Na'ima ta haihu a kitchen saboda 5sabar jaraba.. a ranta tana jinjina rashin kirki irin na Khamal Khamis.

Na'ima wacce ta fito wanka yanzu ta shirya cikin atamfa sai kuka take tana faÉ—in "Ammi kin gani ko? ya gwammace ya É—auki yarinyar yayi waje da ita, akan ya kai ni asibiti, Duk abinda muka tsara a rayuwar mu amma Zuwanta ya fara lalata komai, wlh ba zan iya ba"

Ammi da take riƙe da kyakykyawan jaririn Na'ima wanda ya kwashe kamarta tas, babu abinda ya ɗauka na khamal sai kyawawan fararen idanunsa, amma kamar yaron da Na'ima ta ɓaci.

Ammi tace "kiyi haƙuri, bani da bakin baki haƙuri Na'ima, amma bai dace ki dinga danganta Abra da Khamal ba, Khamal da ya iya riƙe kansa  tun lokacin samartaka, tsayin shekaru mene zai sa kice wannan yarinyar ƴarsa ce? Da Khamal zai ajjiye shege da tun yana saurayi zai ajjiye ba yanzu daya yi Aure ba.
Ba ina kare Khamal ba ne, Saboda rayuwa ta sauya Mutane na iya canzawa a kowane lokaci, balle rayuwa irinta sojoji d suke cuÉ—anya da mutane daban daban.

Naima tace "Har mari na yayi akan gantalliyyar yarinya da babu wanda yasan Wacece ita, yanzu fa kiransa akai aka ce masa na haihu, haihuwar da yake ta burinta kalli yadda yayi watsi da komai? Bai damu da ɗan sa da yanzu duniya yake buƙatar jin ɗumin jikinsa ba,
Nasan Khamal sai ya nuna bambanci tsakanin Shegiyar da ɗan daya haifa Wallahi ba zan iya ba" Na'ima ta ƙare maganar cikin kuka, Granny dake zaune tun ɗazu baki saki tana kallon Na'ima na tatala rashin mutunci, ko nauyin Ammi ba ta ji, ta runste idanunta tace.
"Ki ga gantali a kanki, mace babu Tawakkali, nan nan fa naji ana cewa ƴar uwarki wacce ta mutu cikin Shege tayi, amma ke baki duba wannan ba? Kiyi ta zabga Masifa da wannan yammaci yanzu da kin mutu wajan haihuwa kice me?, to kawai a kiramin Khamal yaje ya nemo mace ya aura tun da ita wannan ba macan rufin asiri bace,  wallahi Na'ima ke ba abokiyar zama bace ban taɓa jin haka ba"
Anuty Suwaiba dai na zaune tana ayyana irin yadda zata saka Na'ima taci Uban Abra, hankali kwance.... Ammi ta sake kiran number Khamal amma bai É—auka ba.

Khamal Khamis dake zaune gaban likita Abra na jikinsa wacce ta samu yin Bacci, a hankali yace "Pardon! Ban gane mene kake cewa ba"
Likitan ya gyara zama bayan ya miƙawa Khamal scanning ɗin da akai ma Abra, tare da X-rays da kuma teses yace
"Binciken da mukai duk sun nuna lafiyarta ƙalau, amma akwai yiwuwar ta kamu da depression, gaba ɗaya yarinyar kamar wani abu na tsorata ta.

“Depression?" Khamal Khamis ya maimaita.

Likitan yace "ka kwantar da hankalinka mana"

Khamal ya girgiza kai yace "I can't, kayi min bayani menene Depression É—in ma na kasa fahimta gaba É—aya" Murmushi kawai likitan ya yi kafin yace.
"It's normal for kids to feel sad, act grouchy, or be in a bad mood at times. But when a sad or bad mood lasts for weeks or longer, and when there are other changes in a child's behavior, it might be depression" Major ya ƙanƙame Abra cike da tausayi a hankali yace.

"To me ze sa Abra ta kamu da depression" Likitan ya kalli Captain cike da kulawa kafin ya girgiza kai yace
" Yana iya faruwa, a dalilin gado idan suna da shi a family, ko yanayin environment É—in da suke zaune, ko wani abu da yake damunsu ko yake takura su".

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun!" Khamal ya faɗa sannan  yace "Abra tai ƙanƙanta ta kamu da irin wannan ciwon"
Likitan yace
"Ba abun mamaki bane ba, a wasu yaran akan iya identifying É—in sa da wuri, kamar a shekarunta idan iyaye suka kula suka je Asibiti da wuri,"
Kallon Abra Khamal kawai keyi idan yace baya son yarinyar ya yi ƙarya, cikin kulawa ya kalli Dr yace.

"What Should I Do if My Child Is Depressed?" Kan Likitan a ƙasa yana duba abu ya bawa Khamal amsa da faɗin.
"A dinga bata isashen lokaci, a zauna da ita a tattauna a ji meye matsalolinta, a gane meyasa take takure kanta daga cikin mutane, kuma ba ta magana, tunda shekara uku a yara ai sun fara kiran sumaye da sauran surutu, amma ita kace sunanka kawai take iya kira, sannan kuma a cigaba da haƙuri za ta warke insha Allah"

Khamal yai ajiyar zuciya, Bayan samun cikakken bayanai, hankalinsa ya ɗan kwanta, kuma yayi imani zaluncin Na'ima ne yake ƙara tsorata ta, ya jefata cikin firgici, amma duk da haka abun na damunsa na yadda Abra ba ta magana.
ÆŠaukan Abra ya yi zuwa waje, a hanya ya tsaya tare da siya mata kayan wasa kala-kala wanda zai É—auke mata kewa.
Kai tsaye gidansa ya nufa, yana zuwa ya samu Ammi a Parlo da Granny sai few people Æ´an uwan Na'ima.
Yadda Ammi ke kallonsa yasa ya É—an shafa kai a hankali yace
"First love" Da sauri Granny tai farat tace "Kaga ƙadaddararriyar matar da Ubangiji ya haɗaka da ita? Mace babu rufin asiri ko kaɗan?" Murmushi kawai Captain yayi domin ganin jariri da mutane a zazzaune, ya tabattar masa da haihuwa Na'ima tai.
Ganin jaririn ya sanya ya mance da ɓacin ran da yake ciki... A hankali ya sauke Abra zuwa gefensa ya ɗauki Baby boy ɗin yana rungume shi.

"Abinda kayi ka kyuta yanzu? Kasan illar abinda hakan ke nufi?" Ammi tai maganar tana kallonsa.
Idanunsa akan Baby boy yace "I'm sorry first love ba zan sake ba"

"Uhm bana son Fitina, bana son zuwan yarinyar nan ya kawo sauyi tsakanin ka da matarka"
A hankali yace "In sha Allah, hakan ba zata sake faruwa ba"

baki Granny ta taɓe tana faɗin "yanzu wanne suna ka sakawa Yaron?"

A hankali yace "SALMAM KHAMAL KHAMIS" Ammi tace "Allah ya raya mai gidana Salman"

A ranar Khamal ya lallaɓa Na'ima ya yi, tare da bata haƙuri, gaba ɗaya ya manta da abunda tai masa, saboda murnar haihuwar Salman, yai ta mata faɗa akan abunda ta aikatawa Abra, da bayanin likita tare da misalta idan akan Salman haka ke faruwa ya za ta ji?.
Ta ce In sha Allah ba za ta sake ba, maganar iya baki ce domin bata kai zuciya ba, tana nan tana tunanin ta ina za ta sake ɓullowa lamarin.

Duk da tarin munafunci da zagon ƙasa, haɗi da almundahana da makaman da gwamnati take bayarwa saboda a bawa jami'an tsaro, amma su General Ibrahim  suke ha'inci akan su, anyi nasarar kuɓutar da 'yan makarantar, bayan tafka uban gumurzu, suka kashe sojoji sosai a wannan karon ma.
Wannan karon babu Captain Khamal, a wanda suka je opretion É—in, amma shima anyi Nasara.
Wannan Nasarar da aka yi, ta raunata alaƙar da ke tsakanin Gwaska da General Ibrahim, har yake tunanin ko General Ibrahim ke ƙoƙarin juya musu baya.
Se da ƙyar sannan suka sasanta suka cigaba da yi wa harkar tsaron ƙasa ɓarna.

Shekarar Salman Biyu a duniya, lokacin Abra nada shekaru biyar, a lokacin aka ƙarawa Captain matsayi zuwa Major.

A lokacin kuma bincike ya tabbatar Abra bata da ƙarfin ji, ba sosai take jin magana ba kuma idan zatai magana da ɗan ƙarfi take.... (Conductive hearing loss)
Likitan ya shaidawa Captain wanda yanzu ya dawo Major, ya tabattar masa da idan aka sa mata hearing aid za ta da din ga ji.
Dan da fari Khamal ya zaci abun daga ƙwaƙwalwarta ne, se da ga baya suka gane, idan akai magana a hankali ba ta ji, se an ɗaga murya ko ta kalli bakin mutum, sannan take gane me yace.
Aka samawa Abra hearing aid, wanda Abbin ya bada kuÉ—i masu yawan gaske, aka siyo shi daga Germany dan yi mata amfani da shi.

General Ibrahim ya cigaba da cin karansa babu babbaka, tare da samun goyon baya, da ga manya manyan muƙarraban gwamnati, suka dinga kawo tarnaƙi ga matsalar tsaro, sannan ya cigaba da takun saƙa  da Khamal, mussaman da aka ƙarawa Khamal ɗin matsayi zuwa Major, tunaninsa kawai shi ne, yadda ze kawo ƙarshen Khamal, yayin da Khamal shi ma ya ɗora alamar tambaya akan General Ibrahim ɗin.

Bayan shekara Goma! (MAFARIN ƘADDARAR ABRA).

KAR KU BARI AYI BA KU, AKWAI TARIN SARƘAƘIYA DA BAN MAMAKI A GABA.

BRIGHT PENS
ZEE KUMURYA
NIMCYLUV
AYSHECOOL

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷ DARE DA DUHU ✷*

Brigh pens✍️
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

             *P.....8*

Domin samun complete litattafanmu, ku yi following É—in wannan accounts É—in a Arewabooks

https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949

https://arewabooks.com/u/nimcyluv

Elegant online writers
Chapter 17 · 0% Book details